Ko shan magunguna na jinkirta cutukan tsufa?

Hilda Jaffe
Image caption Har yanzu Hilda Jaffe mai shekara 95 tana aiki

Za ka yi tsammanin a ce ka gaya wa mutum mai shekara 95 ya tafi a hankali? To ni kam na yi. Hilda Jaffe wata tsohuwa ce mai shekara 95, da na gani tana tafiya da sauri da sauri kusan a ce za ta iya bace wa wasu mutane da suke bin ta.

Mun hadu da ita kenan a zauren shiga babban dakin karatu na New York, inda Hilda take aikin sa-kai na yi wa baki jagora.

To a wannan lokaci za ta kai mu Katafaren dakin karatun da ke cikin ginin ne a lokacin da take wannan sauri, kamar ba mai wannan shekaru ba.

A yadda take wannan tafiya abin mamaki ne kwarai da gaske ga mai shekarunta, domin na ga mutanen da ba su kai ta ba da shekara 60 amma ba sa iya tafiya kamar haka.

Haka kuma kamar sauran mutane masu shekarunta, har yanzu tana sha'awar wasu abubuwa na jin dadin rayuwa da kuma sha'awar ilimi.

Hilda tana yin rubutun nan na wasa kwakwalwa na hada kalmomi wanda ake sanyawa a jaridar New York Times a kullum, sannan tana cikin wasu kungiyoyi biyu na makaranta littattafai, tana zuwa sinima, tana zuwa wurin kade-kade irin na da da sauran abubuwa na nishadin rayuwa.

Haka kuma tana zuwa ko ina a kafa, saboda haka ne ma take bayyana birnin New York da cewa muhimmin birni ne da ya dace da tsofaffi.

Hakkin mallakar hoto Hilda Jaffe
Image caption Hilda a lokacin hutun amarcinta tare da marigayi mijinta Gerry

Na tambayi Hilda, mene ne sirrin tsawon rayuwarta da kuma koshin lafiya?

Sai ta ce: ''Duba iyayenka; mahaifina ya rasu yana da shekara 88, sannan mahaifiyata ta bar duniya tana da shekara 93, saboda haka abu ne da ya shafi kwayoyin halitta na gado.''

An adana kwayoyin halitta na gado da aka diba daga jikin Hilda a cikin kankara a makarantar koyon aikin likita ta Albert Einstein da ke Bronx.

Tana daga cikin mutane sama da 600 da ke sama da shekara 90, wadanda ake gudanar da binciken tsawon rayuwa da kwayoyin halittarsu.

Dakta Nir Barzilai, darektan cibiyar nazarin tsufa, ya ce abin da ke ban mamaki game da wannan rukuni na mutane masu yawan shekaru, shi ne yadda yawancinsu rayuwa su kai ta sharholiya.

Ya gaya min cewa: ''Kusan kashi 50 cikin dari daga cikinsu suna da kiba fiye da kima.

"Yawancinsu masu shan taba ne sosai, ba sa motsa jiki, kuma ba wani abinci mai kyau da lafiya suke ci ba, a takaice ba sa bin ka'idar da likitocinsu suka gindaya musu.''

Bincikensa ya gano kwayoyin halitta da dama a jikin wadannan mutane da ke ba su kariya daga cutukan da ke da nasaba da tsufa.

Ya ce kusan mutum daya ne kawai a cikin 10,000 yake sa'ar samun wadannan irin kwayoyin halitta, amma yana ganin kimiyya ka iya taimaka wa mu da ba mu da irin kwayoyin.

Tuni wasu kamfanonin hada magunguna suka dukufa kokarin ganin ko za a iya amfani da wadannan kwayoyin halitta a kirkiro magungunan da za su jinkirta tsufa da kuma magance cutukan da ke da alaka da tsufan.

Tsawon sama da shekara 60 Metformin shi ne magani mai sauki da ke kan gaba wajen maganin cutar sukari. Gwajin da aka yi da shi a kan wasu dabbobi da dama ya nuna cewa sun samu tsawon rai da kuma cikakkiyar lafiya.

Sai dai abin da masana har yanzu ba su gane ba sosai shi ne yadda wannan yake iya jinkirta cutukan tsufa, amma dai an ga kamar yana rage lalacewar kwayoyin halitta.

A jikin mutane bincike ya danganta maganin metmorfin da rage hadarin kamuwa da cutar zuciya da ta sukari da kuma dakushewar kwakwalwa ko basira.

Dakta Barzilai, wanda kuma mataimaki ne na darektan kimiyya na kungiyar masu bincike kan tsufa, yana kokarin gudanar da wani bincike na mutane 3,000 da shekarunsa suka kama daga 65 zuwa 79, inda za a ba wa rabinsu maganin memorfin kullum sauran rabin kuma a rika ba su nau'in maganin na bogi.

An samu kusan rabin dala miliyan 70 da ake bukata don gudanar da nazarin; ana kuma fatan za a fara gwajin na shekara shida a 2018, amma wannan kila zai dogara ne ga taimakon da za a samu daga wani ko wasu masu bayar da agaji.

A halin yanzu dai hukumar da ke kula da harkokin lafiya ba ta sanya tsufa a cikin jerin larurorin da suka danganci lafiya ba, wato tsufa ba rashin lafiya ba ne a wurin hukumar (FDA).

Hakkin mallakar hoto Max Touhey Photography/NYPL
Image caption Babban zauren dakin karatu na Rose da ke New York wanda aka bude a shekarar 1911, inda Hilda Jaffe take aikin yi wa baki jagora

To amma Dakta Barzilai ya ce idan har gwajin da za a yi da maganin metmorfil ya yi nasara, to hakan zai tabbatar da cewa tsufa abu ne da za a iya jinkirta shi.

Kuma mai binciken ya yi amanna za a samu magunguna masu tasiri sosai a kan matsalar a nan gaba.

Wani fannin kuma da za a iya yin bincike don jinkirta tsufa da maganin cutukan da suke da nasaba da shi, shi ne tsarin aikin jikin halittu ta yadda kwayoyin halitta ke daina rabuwa.

Yawancin kwayoyin halittar mutum sukan hayayyafa ne zuwa wani lokaci mai wa'adi, wanda hakan ke kare cutar daji, domin kwayoyin halittar da kara rtabuwa, to amma idan suna ta hayayyafa hakan zai iya kasancewa da wani hadari na samun kuskure ko illa ko nakasu a wannan hayayyafa.

A kashin farko na rayuwar mutum, wannan hayayyafa ta kwayoyin halitta na samar da kariya ga jiki daga cutar daji.

Amma yayin da muke girma ko tsufa, wadannan kwayoyin halitta da ke hayayyafa sai su taru da yawa su cunkushe wuri, sannan su cutar da sassan jikin da ke makwabtaka da su, wanda hakan kuma sai ya bujuro da cutukan da ke da alaka da tsufa, misali a gabobi da kuma idon mutum.

A shekara mai zuwa (2018) kamfanin hada magani na Unity Biotechnology da ke California na shirin fara gudanar da gwajin wani magani na kawar da tarin wadannan kwayoyin halitta da ke cunkushewa ko hayayyafa a guiwa a lokacin da mutum ke manyanta.

Babban likitin cibiyar, Dakta Jamie Dananberg ya gaya min cewa; ''Ciwon gabobi shi ne babban dalilin da ke sa ba a jin dadin tsufa.

Fatanmu shi ne a samu allura daya kawai da za a yi wa mutum ta kawar masa da wannan ciwo, ta dakatar da shi, sannan kuma kila ma har ta fara gyara matsalar da ke damun guiwar.

Bayan guiwar maganin da kamfanin ke kokarin kirkirowa har da wanda zai yi irin wannan aiki na magance matsalolin da suke addabar ido da huhu da koda a lokacin tsufa.

Ko da maganin da za a kirkiro za a rika yi wa mutum allurarsa ne duk bayan 'yan watanni, in dai an samu 'yar nasara da shi to ba shakka hakan zai iya inganta rayuwar jama'a.

Sai dai fa a sani su wadannan magunguna ba wai za a kirkiro su ba ne domin su taimaka mana mu kara tsawon rayuwa ba, a'a, sai dai kawai don su rage mana radadin cutukan tsufa tare da kara mana lafiya a tsawon shekarunmu.

Idan har magungunan suka yi aiki, to ke nan da yawanmu za mu zama kamar Hilda Jaffe wajen samun tsawon rayuwa da kuma tsufa da cikakkiyar lafiya.

Labarai masu alaka