Mene ne dalilin kamfanoni na hana amfani da wasu kalmomi?

Daga Mark Johanson

Idan kana neman aiki a Davio, wani karamin gidan sayar da abincin gargajiyar kasar Italiya da ke Amurka, ba za ka taba jin kalmar da ta shahara da ake amfani da ita a wajen aiki: ma'aikaci.

Dalilin haka kuwa shi ne Shugaban kamfanin ne Steve DiFillipo ya hana amfani da ita.

"Ina jin cewa ma'aikaci (dan kwadago) mummunar kalma ce," in ji shi. "Wane ne ke son zama ma'aikaci (dan kwadago)? Kawai ba wani abu ba ne da za ka yi ta fafutikar kai wa gare shi." Sabanin haka ma, wadanda ke yi wa DiFilllipo aiki an fi sanunsu da 'bakin cikin gida.'

"Daukacin masu hidimar aiki da girke-girke sukan yi kai-kawo daga wannan gidan abinci zuwa wancan don neman amfita; mun shawo kan hakan," a cewarsa. "sun zo nan sai suka fahimci suna wani wuri na daban, inda ake ba su kulawa tadaban."

A wajen DiFillipo haramta amfani dakalma daukacinsa wata dabara ce ta karfafa kwarin gwiwar aikin 'bakin cikin gidansa' tare da bayyana managartan manufofin kamfanin ga 'bakinsa na waje' (da ke zuwa cin abinci).

Haramta amfani da kalmomi tare da bijiro da wasu furuce-furuce ana yi ne don kyautata dangantaka da abokan ciniki da jan su a jika.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yawan sauya lakabin kimar matsayin mukaman aiki

Wannan mai gidan abinci ba shi kadai ne ya yunkura a zakuwwarsa wajen tunkarar kalubalen da ake a kai. Kamfanin hada-hadar massararrafar kwamfuta na Montreal GSOFTba da dadewa ba ya haramta amfani da lakabin sashen kula da ma'aikata' saboda ya yi matukar kasancewa na kashin kai, inda aka maye gurrbinsa da sashen al'adu da shirye-shirye da aka dora wa alhakin "hada karfin wajen aiki." Sannan lakabin likon alaka (kulla dangantaka- networking) an haramtata a kamfanin gine-gine da saka jari na Birtaniya da ke birnin Landan (sabanin haka sai dai ma'aikata su halarci 'wajen tatttaunawa' a tarurruka).

Amma haramta amfani da wani lakabi na al'ada, inda aka maye gurbinsa da wani sunan mafi dadin ambato ko yana da wani kyakkyawan alfanu? Ko cukurkuda kalamomin wurin aiki da ma'ana biyu na kara damlmala al'amura ga daukacin wadanda lamarin ya shafa?

Gogaggun mutane da 'yan duba da masu wa'azi

Don fahimtar yawan hana amfani da kalmomi zai yi matukar kyau idan aka dubi yaduwar sababbi da kirkirarrun furuci iri-iri na kimanta matsayin aiki, daga kan "mai kayata makwalashe - sandwich artsit' wanda ke shirya maka abincin rana iri-iri har kan 'mai dimbin basira- genius' da ke katafaren shagon kamfanin kwamfut ana Apple, wanda yake gyara maka wayar al;farma na iPhone. Kamfanonin na'urorrin szdarwa sun shagaltu da wannan lamari, "gogaggun masu kirkire-kire' a Microsoft (kamfanin kwamfuta) da 'yan kwalisar masu wa'azi' suke a Tumblr (shafin zumuntar likon alaka na intanet) da 'Yan duba - Prophets' suke a AOL (America Online- shafin sadarwar Amurkawa).

Kalallame kalaman juyin harshe zai iya rikirkita managarciyar yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci,tattare da bibiyar Kadin al'amura.

Dan Cable, Farfesan nazarin dabi'ar dan Adam a wajen aiki a jami'ar LBS (London Business School), cew aya yi, duk da cewa bai damfaru da jin cewa dole ne akakabalakabin mukami kamar "Injiniyan hasashe -imagineer' zaimayar da injiniyoyin a wajen was an shakatawa na Disney Land su kara basirarkirkire-kire, ba yarda da cewa salon sarrafa harshe zaio zaburar ngartar aiki da bin Kadin al'amura na kashin kai.

Idan za ka samu daidaikun mutane su yi tunani kan yadda za ssu tunanin bullo wa kamfani da sababbin dabaru na daban,kawai kalma daya ko biyu za su biya bukata a amtswayin tunatarwa a kai- a kai; dole a tafi tare da kai, kana da muhimmanci, kai mai jajircewa ne (kan aiki)," in ji shi.

Ta hanyar cewa ka duaki 'bakin cikin gida' (aiki) sabanin ma'aikata, "ta yiwu ka zakulo wasu mmutane daban da kekan wani tsari na tunanoi tun kafin ma su shigo kamfnain,"in ji Cable. Binciken da ya gudanar ya yi nuni da cewa baya ga daukar ma'aikata, kirkirar lakabin mukami na da muhimmanci gadaukacin shawo kan dugunzumar dmuwa da zaburar da kuzarin kwazon ma'aikata.

Sauya lakabin wajen aiki

Lamarin da ke tashe wajen juya harshen lakabin wajen aiki da falsafa (alkiblar tunani) duk jigon takun tafiyar sabon karni na 21 ya haifar da haka, wanda bincike ya nuna hankoron cimmma babbar manufa fiye da wadanda suka gabace su. Hana amfani da kalmomi kaitsaye da maye gurbinsu da wasu na nuni da fafutikar kai wa mataki na gaba.

Daukacin hanin kamfani kan amfani da kalmomi an dora shi ne kan doron shawo kan munanan al'amuran da ke tattare da kayan kamfani. Kundin nazari da aka fitar a shekarar 2014 matsayin wnai bangare na yarjejeniyar kamfnain motoci na General Motors da Gwmanatin Amurka ya nuna yadda kamfanin ya horar da injiniyoyi yadda za su kauce wa furta kalmomi 69 da ke harzukarwa (ruruta wuta ko tayar da hankali) da furuci iri-iri da suka hada da "gurbata - defect,' 'flawed - mai matsala' da 'ramin mutuwa - death trap'".

Kuma kamar yaddda yake kunshe a wani rahoto da ka tattara a sshekarar 2011 a mujallar Wall Street, wanda ya bi Kadin sirrin kundin horar da ma'aikata, d atattara bayanai kan trurruka, Apple (kamfanin kwamfuta) ya horar da ma'aikatan da ke aiki a sashen ciniki da su kauce wa yinfurta kalmomin da suka hada da "cikin rashin sa'a' sabanin haka masu basira ma'aikatan Apple an umarce su su rika cewa "tamkar yadda lamarin ya kasance - as ita turns out' don rage illa a lokacin da wani lamari ya taso.

Kan al'amarin da ya shafi kaya (da aka kera a kamfani) da biyan bukatar abokan ciniki... ana hana amfani da munanan kalamai tare da karfafa furuci iri-iri da ke nuni da kwarin gwiwar samun tabbaci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana hana amfani da munanan kalamai tare da karfafa furuci iri-iri da ke nuni da kwarin gwiwar samun tabbaci

Shafin intanet na kamfanin na'urorin sadarwa Gizmodo, wanda shi ma ya yi la'akari da kundin da ke dauke da sirrin ma'aikaci,ya yi nuni da cewa ma'akatan Apple (kamfanin kwamfuta) an hana su amfani da ire-iren furucin da suka hada da 'kwayar cuta -bug' ko 'tarwatsewa ko lalacewa -crash' inda aka fifita'ba sa motsawa ko harbawa -not responding'. Sannan 'dumi-warm'kan 'zafi -hot' wajen siffanta kayan da ke fitar da zafi.

Haramtatttun kalmomin kwanan nan sun kara jagwaba al'amura, inda kalmomi da lakabin mukamai da furuci iri-iri suka kara tsaurara har suka kauce wa al'adar kamfanin.

A cewar Cable haramta amfani da kalma wata dabara ce mai fadi ta kimanta darajar kashin kaidon isar da sako ga daukacin jama'ar waje (abokan ciniki) da ma'aikatan cikin kamfani." Idan alal misali ka rusa sashen kula da abokan ciniki ka maye gurbins da "rundunar gwarazan faranta zukata,' a matsayin shafin zumunta na katafariyar kafar tarairayar aiki, ka yi hakan ne don raba mu (matasan da ke da rajin kawo ci gaba) daga su (tsofaffin da ba su da karsashin sauyi).

Da zarar ka fara hana amfani da wasu kalmomi kana maye gurbinssu da wani abu daban za su iya kwata zaurancen shaguben George Orwell (marubucin Gandun Dabbobi - \Animal Farm).

Yayin da sunaye suka zama tsohon ya yi

Lisa Merriam, kwararrriyar mai bayar da shawara kan hada-hadar ciniki ko harkokin kasuwanci da ke birnin New York, kuma marubuciyar manuniyar dabarun Merriam na lakaba suna, inda ta ce ka'idojin harshe na iya zama 'kaikayi koma kan mashekiya' a kai- akai. "Da zarar kamfanoni sun nuna ko'in kula, sabanin abin da aka zata ke aukuwa. Lamari ne na wulakanci mai rikitarwa," inji ta.

Merriam ta ce, ta hanyar sauya kalamai da kimar mukamn aiki kawai don tafiya da zamani, ma'aikata na yi wa kansu shamaki da masu daukar aiki a nan gaba, "idan an lakaba musu (sabon salon mukaman) da ba sa kayatarwa, wai don tafiya da zamani."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yawan sauya lakabin kimar matsayin mukaman aiki

Yawan sauya lakabin kimar matsayin mukaman aiki da aka sani na al'ada zuwa wasu sababbin dabaru na iya haifar da dimbin matsaloli fiye da warware su.

Binciken baya-bayan nan da aka gudanar kan mutane 1,00 'yan Birtaniya, inda aka bukaci su nuna ko lakabin mukaman aiki 18 da ake amfani da su a kamfanonin sadarwa na gaske ne ko na bogi ne.

Sakamakon :Janjanin juyin jagoran hadari 'The cloud Master (Wasan kwamfuta na shekarun 1980) ya fi zama tabbatacen aiki fiye da kimar matsayin ayyuka shida daga cikin tara da ake da su a kamfanin sadarwa (na'ura mai kwakwalwa ta kwamfuta).

Henry Goldbeck , shugabn kamfanin daukar ma'aikata na Goldbeck da ke Vancouver ya bijiro da wnanan lamari a sakon da ya baje a shafin sadarwa na LinkedIncewa,masu daukar ma'aikata bas a duba bayanan da masu neman aiki ke bajewa a shafukan sadarwa ta yadda za a gano cewa su "kwararru ne" ko "shahararru ne" kamar yadda ya yi kai-kawo (a nazarinsa). Suna neman akawun kudi (masu lissafin shige da ficen kudi - raba riba da asara).

Ta yiwu mafi muhimmanci lamarin, Mariam na da tabbacin cewa dole ka yi takatsantsa wajen hana komai a wajen aiki, musamman a yanayin muhallin wannan zamanin da al'amura ke bijirowa ba kakkautawa.

"Da zarar ka fara haramta amfani da wasu kalmomi, tqre da maye gurbinsu da wani abu daban a iya karke wa da kwata zaurancen shaguben George Orwell (Marubucin Gandun Dabbobi -Animal Farm)," in ji ta. "Zabar sababbin kalmomi don maye gurbin kalmomi masu ma'ana karara da aka fahimce su, zai iya haifar da rudani ko rashin yarda, har ta kai ga an cusa wa ma'aikata jin rashin ganin kimar kamfani."

Labarai masu alaka