Macizai 200 sun sare shi a kokarinsa neman magani daya

Tim Friede da macijiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Digo daya na dafin wannan macijiyar na iya kashe dan Adam

A duk minti daya, saran maciji na kashe mutum daya, wasu mutum hudu kuma na samun nakasa ta har abada a fadin duniya.

Duk da haka akwai wasu mutane da ke sayar da ransu wurin gudanar da bincike a kan macizai.

Tim Friede, dan jihar Wisconsin na kasar Amurka, yana daukar hoton bidiyon yadda macizai masu dafi ke saran sa, yana sanya wa a shafin YouTube.

Radadi nan take

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tim Friede ya kan bayyana wa masu kallansa a YouTube yadda yake ji idan macizan suka sare shi

A daya daga bidiyon, bayan wata macijiya ta sare Friede sau biyu a tsintsiyar hannunsa, sai Friede ya ci gaba da kallon kyamara yana magana, ba tare damuwa da jinin da ke tsiyaya daga saran macijin ba.

"Radadin sarar irin wannan macijin na zuwa ne nan take. Zafin sarar macikin kamar kudan zuma 1,000 ne suka harbi mutu a lokaci daya.

Kudan zuma na da Miligram daya ko biyu na dafi. Amma dafin wannan macijin ya kai Miligram 300 zuwa 500."

Daga nan, sai ya gaya wa BBC abin da zai biyo baya.

"Nan na kan samu kumburi bayan saran macijin. Ya kan kwantar (galabaitar) da ni na 'yan kwanaki. Daga girman kumburin da wurin ya yi na kan iya hasashen yawan dafin da maciji ya sa a wurin da ya sare ni. Akwai zafi sosa,' yana magana da hakikancewa.

Hadarin da rashin dacewa?

Amma ba kowa ne abin da Friede ke yi a shafin YouTube yake burgewa ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tim Friede ya ce jikinsa ya samu kariya daga saran maciji

"Ba mu san iya abin da mutanen nan ke yi ba. Hakan na da hadari kuma bai dace ba. Ba ma aiki da su," in ji Dokta Stuart Ainsworth na cibiyar da ke bincike a kan magunguna cututtukan da yankuna masu zafi ke fama da su ta Liverpool.

Cibiyar na daga cikin cibiyoyi masu bincike domin samar da rigakafin dafin maciji na bai daya.

Akan yi gwajin sabbin magungunan riga-kafi ne da beraye da wasu dabbobi da ake amfani da su dakunan gwaje-gwaje. Idan an tabbatar da rashin hadarin riga-kafin sannan sai a gwada a jikin dan Adam a wani killataccen wuri.

"Mutane kan bai wa kansu rigakafi, saboda rashin tsauraran matakai. Kuma yin hakan na iya sanadiyyar mutuwa. Mutane su guji yin hakan,", in ji Dokta Ainsworth.

Sai dai akwai karancin ka'idojin gudanar da bincike kan samar da maganin saran macizai, a fannin samar da magunguna a fadin duniya.

"Babu tsayayyun tsare-tsaren kula da sarrafa magunguna ko kare lafiya ko ingancin magunguna," inj i Wellcome Trust ta kasar Burtaniya, daya daga cikin cibiyoyi da ke jagorantar binciken kimiyya na samo sabon rigakafi.

Mummunar hadari

Friede ya sha musana zargin da ake masa cewa yana jefa rayuwarsa a hadari domin neman magoya baya a social media.

"Ba don in yi bidiyon YouTube nake yi ba - Ina so ne in ceci rayuka kuma in kawo sauyi. Ina amfani da YouTube ne kawai domin in samu likitocin da yanzu muke aiki tare," a cewarsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tim Friede ya tsallake rijiya da baya a lokuta daban-daban

Daga cikin jinsi 3,000 na macizai, jinsi 200 ne kadai ke da dafi mai cutarwa da ke iya kisa ko ya illata dan Adam. Kuma Friede ya san yawancin wadannan jinsin sosai.

Kama daga gamsheka, kumurci da sauransu, Friede ya jure sarar macizai 200 a cikin shekara 20 da suka gabata. Baya ga jinsin wasu macizai 700 da ya yi wa kansa allura da dafinsu.

Yawan dafin da macizai ke tsittarwa idan suka yi sara na iya bambanta. Wani lokaci maciji na yin sara ba tare da ya tsitta dafi a ciki ba. Yin allurar dafin wata hanya ce ta kula adadin dafin da ake sanyawa.

"Idan ba ka da cikakkiyar kariya daga dafin wani macijin sai ya iya illata tsarin gudanar da jikin dan Adam.

Hakan na nufin hanyar da iska ke wucewa za ta daskare ba za ka iya numfashi ba, idanunka za su rufe ba za ka iya yin magana ba, da haka har sai sashen jikinka ya shanye. Amma kuma ba zai shafi kwakwalwarka ba, don haka za ka ci gaba da yin tunani, har sai ka mutu," in ji Friede.

Saran gamsheka na da tsani

Friede na ajiye da tarin macizai masu dafi da yake gwada karfin saransu, a bayan gidansa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daya daga cikin macizai mafiya hadari - dafinta na iya kisa a cikin minti 30

Ina da gamsheka daga nahiyar Afirka. Saranta na da tsananin radadi mai firgitarwa."

Dafin macijin na da guba mai illata jijiyoyi.

"Sauran jinsin kumurcin na da dafin da ke haifar da cutar da ke nakasa kwayar halitan dan Adam, kamar yadda wata ke iya sare dan yatsa ko ma hannu baki daya."

Friede na aiki ne da wata fahimtar da ke cewa idan aka sanya wa mutum dafin macizai da kadan-kan, hakan zai iya kara karfin kariyar jikinsa. Amma masana sun soki wannan fahimtar.

Samar da kariya?

Irin wannan hanyar - amma ta amfani da dabbobi - ta taimaka wurin samar da maganin sarar maciji gudan dayan da ake da shi yanzu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana tsoron macizai, a wasu al'adu kuma ana girmama su sosai

Tun a karni na 19 ba a sauya hanyar sarrafa maganin dafin macizai sosai ba.

A kan yi wa doki ko tunkiya allura da dafin maciji dan kadan. Daga nan sai dauki sunadaren da ke bai wa jiki kariya daga jinin dabbar domin a yi gwaje-gwaje.

"Wadannan dabbobin na son su kashe ni, amma ni ba na so in mutu. Saboda haka sai na zama ni ne dokin. Me zai hana mu ba wa kanmu kariya? Tambayar da Friede ya yi ke nan.

Dan shekara 51 kuma tsohon direban babbar mota, Friede ba masanin kariyar jini ba ne kuma bai halarci jami'a ba. Tsoronsa na kada macizai su zama ajalinsa ne ya sa ya fara wannan aiki mai ban al'ajabin shekara 20 da suka gabata.

Ya fara ne ta amfani da gizo-gizo da kunamu kafin daga bisani ya fara amfani da manyan macizai.

"Ba da kowane jinsin macizai masu dafi a doron kasa nake amfani ba. Masu saurin kisa ne nake zabowa."

Jikinsa cike yake da tabon saran macizai da ya yi gwajin da su, wadanda suka kusa yin ajalinsa a gwaje-gewajen da ya yi. Amma duk da haka yana jin dadin macizai su sare shi ba tare da kulawar likitoci ba.

"Sau 12 ina tsallake rijiya da baya daga dafin macizai. Sau biyu ana kwantar da ni a asibiti sakamakon sarar gamsheka a shekarar da na fara yin gwajin. Dole sai mutum ya koya. Babu wani likita wata jami'a da za ta iya koya wa mutum wannan."

Ninka rigakafi

Gwajin nasa ya kara masa kwarin gwiwa cewa hanyar da yake amfani da ita na samun nasara.

Hakkin mallakar hoto Swaminathan Natarajan
Image caption Maganin dafin macizai na da tsada kuma yana iya haifar da borin jini

"Sunadarai masu ba da kariya da ke jikina sun kai ninki biyu na adadin da ke ba da kariya daga dafin macizai. Gwaje-gwajen kimiyya sun tabbatar da haka," a cewarsa.

Shekaru biyu da suka gabata, hotunan Tim Friede a shafin YouTube sun ja hankalin wani masanin sunadarai masu ba wa jiki kariya, Jacob Glanville, wanda ya bar aiki a mastayin babban jami'i a kamfanin sarrafa magunguna na Pfizer, domin ya kafa kamfaninsa na yin maganin dafin macizai.

"Abin da Tim ya yi abin yabawa ne, amma yana da hadari. Ba zan taba ba wa wani shawarar ya yi ba," in ji Glanville.

Yanzu kamfanin na daukar samfurin jinin Friede wurin yin gwaje-gwajen domin samar da sabon maganin dafin macizai.

"Sun dauki samfurin kwayoyin halitta na DNA da RNA da kuma sunadarai masu ba da kariya wanda suka tagwaita su. Wannan shi ne kololuwar kimiyya," in ji Friede.

Cutar da aka yi watsi da ita

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce a macizai na saran mutum miliyan 5.4 a kowace shekara. Mutum 81,000 zuwa 138 na mutuwa daga dafin macizai. Wasu 400,000 na samun nakasa da dindidin da ke illata rayuwarsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A yawancin sassan duniya mutane da macizai na rayuwa a muhallai guda, wanda hakan ke nuna yiwuwar samun fito-na-fito a tsakaninsu

Amma sai a 2017 hukumar lafiya ta duniya ta ayyana sarar maciji a jerin cututtukan yankuna masu zafi da aka yi watsi da su.

An ware 19 ga watan Satumbar duk shekara a matsayin ranar wayar da kan al'umma kan saran macizai. Makasudin hakan shi ne magance matsalar da ke illata al'ummomin karkara a yankunan Asiya da Afirka da Kudancin Amurka wadanda har yanzu ba su da cikakken tsarin kula da lafiya na zamani.

A kasashe da dama, magungunan dafin macizai ba su aiki, saboda dadewa a wurin ajiya ko kuma saboda su kan yi aiki ne a kan dafin wasu jinsin macizai ban da wasu.

Beraye

A watan Mayun wannan shekarar, cibiyar Wellcome Trust ta sanar da kafa gidauniyar dala miliyan 100 domin samo sabbi kuma ingantattun magungunan dafin macizai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi gwajin sabbin magungunan da aka kirkira domin tabbatar da rashin hadarinsu ga rayuwa

Su ma wasu hukumomi da cibiyoyi na kokarin samar da magani mara hadari kuma mai sauki.

Aikin da Friede ke yi da Glanville zai sa Friede ya samu kudade masu yawa idan har sun iya samar da sabon maganin rigakafi.

"Ba za a biya ka ba don maciji ya sare ka. Amma idan muka hada rigakafi za a samu kudi. Ina da lauya kuma mun rattaba hannu a kan yarjejeniya," in ji Friede.

Glanville ya zaku a fara gwaje-gwajen da za a gudanar a nan gaba.

"An dade ana wannan binciken - muna gab da fara gwaje-gwaje da beraye."

Tsanantawa da manufa

Glanville da Friede na samun suka daga masanan kimiyya saboda yadda suke amfani da hanyoyin da suka saba wa tsayin kimiyya. Amma duk da haka mutanen biyun sun kare salon gudanar da binciken nasu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tim Friede ya ce yana daukar hadari mai tsanani ne domin cimma wata manufa

"Mun kiyaye abubuwan da suka shafi ka'idoji cikin lura. Mun bi irin tsarin da ake amfani da shi wurin nazarin hadurran da ke da alaka da abubuwan da ake mu'amala da su a wurin aiki irinsu raunuka da HIV da sauransu.

Da yake tabbatar da cewa hanyar da yake bi na da matukar wahala ga wasu, Tim Friede ya kara da cewa akwai yiwuwar saura kadan a samu sakamako.

"Akwai manufa a tsanantawar da nake yi. Na sa rayuwata a cikin hadari ne domin neman maganin dafin macizai na bai-daya kuma mai sauki.

Labarai masu alaka