Dalilin da ya sa ba ka jin daɗin yin bulaguro

Hakkin mallakar hoto b

Shin ko ba ka jin dadin yin bulaguro? Idan haka ne to ba ka yin abin da ya kamata a lokacin bulaguron.

Jessica Patch tana da dalila da dama da suka sa ta karbi aikin tallata hajar kamfanoni a San Francisco. Hakika aikin yana da tasa matsalar, amma ta san cewa za ta yi amfanin da kudin wajen neman maganin rashin haihuwa.

A kowace rana, Jessica na tafiyar mil 55 a mota zuwa ofis abin da kuma kan sa ta kwashe awanni hudu, a hanya.

Patch tana sauraron shirin iyali na Oprah Winfrey domin ta daukewa kanta kewa ta kuma ragewa kanta adadin gajiyar aiki. To amma kuma duk da haka Jessica ta ce wahalar da ke tattare da tafiyar da take yi idan za ta je ofis "tana wahalar da ita."

Bayan wata tara, Jessica ta mika takardar barin aiki. Gajiya ta tararwa matar mai shekara 35, abin da yasa har ta samu matsalar ciwon ciki sannan kuma ta samu ciwon baya saboda tsawon lokacin da take kwashewa tana zama a mota.

Bayan wata tara, essica ta mika takardar barin aiki, a inda ta koma aikin aukar hoto wanda take yi tana cikin gidanta.A watan Oktoba ne dai Jessica take tsammanin za ta haihu.

Jessica Patch dai ba ita kadai ce ba ta jin dadin yawan tafiyar ba. Gately, wani marubucin wani littafi mai suna Rush Hour, ya ce " ina tunanin cewa mafi yawancin mutane suna fuskantar irin wadan nan matsalolin da ke tattare da tafiya saboda muna samun kanmu a cikin jirgin kasa kuma mu makale a ruguntsumin taron ababan hawa. Kuma mutane ba su san abin da ya kamata su yi ba."

To shin tafiya a abin hawa ba ta da dadi ne?

Bincike da aka yi daga kasar Ghana zuwa Jamus ya nuna cewa ana kara samun tazara sosai tsakanin wurin aikin mutane da inda suke aiki abin da ke haddasa musu gajiya da rashin barci da kuma rashin kula da iyali.

Wata kididdiga da aka yi a tsakanin Amurkawa ta nuna cewa idan aka hada awannin da mutane ke tafiya a shekara, za a ga cewar duk mutumin da yake tafiyar awanni 15 a tsawon mako 50, to zai yi asarar bacci ta akalla minti 30, a kullum.

Sabbin nazarin da aka yi sun tabbatar da cewa tafiya zuwa wurin aiki zai iya zama wani abun da zai debewa mutane kewa musamman daga zaman gida.

Sai dai kuma an gano cewa akwai wasu matsaloli da ke hana mutane cin gajiyar amfanin da ke tattare da tafiya.

Matsalar dai tana tare da mutane. Shin ko hakan na nufin ba ma yin abin da ya kamata yayin tafiyar tamu?

Tsara tafiya

Wasu masu bincike na kasa da kasa sun ji ta bakin ma'aiakata 225 na wani babban kamfanin watsa labarai a birnin London, a wannan shekarar, a inda suka gano cewa yanayin nisan tafiyar da suke yi yana da alaka da karin jin rashin gamsuwa da aikin da suke yi.

Sai dai kuma ba a samu wata alaka da ke tsakanin balaguro mai nisa domin zuwa wurin aiki da samun gamsuwa da aikin ba musamman ga mutanen da suke da manufa suka kuma tsara yadda za su yi tafiyar.

Wani dalibi mai nazarin digiri na uku, a jami'ar nazarin kasuwanci ta Columbia da ke New York, a wata makala da ya gabatar mai taken 'Tsara yadda za a yi tafiya', ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa mutanen da ke da manufa kuma suke tsara tafiyar tasu sun fi cin ribar zama wani abu a harkar aikinsu.

Mutanen da ke tsara tafiyarsu su ne wadanda suke tamabayar kansu jerin wasu tambayoyi a duk wata safiya da za su yi tafiya. Tambayoyin dai su ne shin me zan yi a yau? Mene ne alakar aikin nawa na yau da sauran abubuwan da zan yi a tsawon mako? Shin ko abin da zan yi zai taimakawa burina na abin da nake son na cimma, a rayuwa.

Samun damar yin wadan nan tambayoyi a kowace safiya ya kan ba wa mutane samun nasarar gudanar da ayyukan da suka sanya a gaba, ba tare da wata matsala ba.

masu irin wannan ta'ada ta tambayar kansu abin da suke son cimma, ba su cika yin korafi kan gajiyar aiki ba.

Matsalolin kaɗaita a yayin bulaguro

Mutanen da ba sa tuƙa kansu zuwa wurin aikin, to za ka ga cewa sun mayar da hankali wajen karanta jarida ko kuma duba imail. To sai dai yin hakan ka iya zama matsala a gare mu. Saboda me?

Mutanen da suke tafiya a jirgin kasa ko kuma motar da jama'a ke shiga, sun fi tunanin tafiyar da suke yi ta fi tsayi, a kan wadanda suke tuƙi da kansu.

Alkalumma da aka tattara a Canada sun nuna cewa fasinjojin da suke amfani da abubuwan hawa na gama-gari, sun fi daɗewa suna tafiya fiye da wadanda suke tuƙa kansu. Sannan kuma akwai ƙarin gajiya idan mutum ya yi tafiya a cikin turmutsutsin mutane.

Gately, a cikin littafin nasa na 'Rush Hour' ya ce mafiya yawan lokuta, tafiya a cunkoson mutane wadda ba ta dace da ko da dabbobi ba, ita ce take haddasa mutane gajiya liƙis.

Hakan dai yana faruwa a birane irin su Tokyo da Beijing ko kuma Moscow, a inda ababan hawa suka fi komai kai-komo a duniya.

To amma don me fasinjoji suke kula mutanen da ba su sani ba a yayin tafiya?

Gately ya ce "gaskiya ba mu dauki mutane a bakin komai ba, muna kyamatar su, abin da ke nuna cewa hakan na sanya har mu sauka daga abin hawa amma ba mu yi mu'amala da su ba, kamar yadda ya kamata."

Hakan zai iya debe mana kewa daga cunkoson mutane domin nazari ya nuna cunkoson na haddasa tarin gajiya.

Kuma ma bincike ya gano cewa mu'amala lokacin tafiya a cikin mutane, na ba wa mutanen da ke son hulda da jama'a da wadanda ma ba su cika magana ba, damar samun farin ciki a rayuwarsu. idan kana son karanta labarin na turanci za ka iya latsa wannan Could Communting be good for you?