Birnin da ya fi ko wanne sauƙin zama a duniya

Birnin Vienna ya kasance wata mahaɗa tsakanin gabashi da yammacin Turai kuma kamfanonin kasashen duniya sun lura da hakan.

A baya-bayan nan ne babban birnin na Austria ya yi wa birane 229 na duniya fintinkau wajen kasancewa birnin da ya fi kowane sauƙin zama, kamar dai yadda wani bincike da kamfanin tuntuba na Mercer, ya yi.

Kusurwar da birnin ya kasance da kuma sauƙin zaman da yake da shi ne suka janyo hankalin 'yan kasuwa da masu son zuba jari. Manya-manyan gidajen alfarma da zane-zane suna daukar hankalin masu yawon bude.

"Ni a wurina, Vienna ne ya fi kowane birni kyau a Turai," In ji Magnus Beyer, wani injiniya da ke kwalejin Imperial a birnin London wanda kuma a baya-bayan nan ya je birnin na Vienna domin a manufar kasuwanci, a inda kuma ya halarci babban taron majalisar Turai na kungiyar manazarta kimiyyar Duniya, da aka gudanar a watan Aprilu.

Hakkin mallakar hoto AP

Baya ga sunan da birnin ya yi dangane da yadda ya kasance abin sha'awa tun a zamanin baya, masu ziyarar birnin da aka tambaya sun ce kyawun birnin ne yake jan hankalinsu.

" A koyaushe kyawun birnin ne yake jan hankalinsu. Da yawa daga cikin su suna mamakin yadda mutane suke tafiya a filin Allah ba tare da wata matsala ba da kuma kasancewar ababan na zamani sannan babu cunkoso duk da cewa nan ne babban birnin kasar." in ji Jan-Paul Dantil, manajan otal na Ritz Carlton da ke Vienna.

Ya kara da cewa mutane daga kasashe da kungiyoyi daban-daban na duniya suna sauka a otal din domin yin kasuwanci.

Jakadun kasashe da manya-manyan jami'an gwamnati da masana suna zuwa nan misali ma shi ne irin mutanen da suka sauka a otal din a lokacin taron Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC. Tun shekarar 1965 kungiyar ta OPEC take gudanar da ayyukanta daga nan Vienna.

Kasancewar Vienna daya daga cikin wurare guda hudu da Majalisar Dinkin Duniya take da ofisoshi a fadin duniya, birnin ya kasance inda wasu daga cikin sassan na MDD suke kamar Hukumar Kula da Makamashi ta MDD. Kuma ofisoshin na MDD suna da ma'aikata 4,400 daga kasashe 120.

Birnin na Vienna wanda yake da yawan jama'a da suka ɗara miliyan 1.8, ya zamo birnin na biyu mafi girma da ake magana da yaren Jamus.

Ursula Kainz na Kungiyar Kasuwanci ta Vienna wadda ke shawartar kamfanoni na cikin gida da na ketare, ya ce akwai dalibai 200,000 da ke jami'o'i daban-daban, abin da ya karawa birnin kimar kasancewa na kowa kuma wanda yake da dimbin matasa da ke more rayuwarsu ta fannin raƙashewa da dare.

"Idan ba ka zo birnin ba shekaru 10 da suka gabata, to yanzu ba za ka iya ɓata, saboda an samu yawaitar gidajen cin binci da mashaya iri-iri da masana'antu sannan kuma akwai kabilu daban-daban." in ji Kainz.

A baya dai birnin na Vienna ya kasance mahadar Turai ta tsakiya ne kawai amma yanzu birnin ne zuciyar Turai baki daya, tun bayan faduwar Tarayyar Soviet. Kuma alamu na nuna birnin ne kofar bunkasar tattalin arzikin nahiyar Turai daga gabashi.

Bugu da kari, sakamakon kara fadada da Tarayyar Turai ta yi a gabashin nahiyar, Vienna ya zamo wata cibiyar hada-hadar kasuwanci.

Kaninz ya ce fiye da kamfanoni 200 daga kasashe daban-daban da ke da hedikwata a birnin kuma ana samun karin wasu kamfanoni da ke bude ofisoshi.

Al'adar girmamawa

Ana daukar mutanen Austria da wasu girmama juna musamman wajen matsayi da mukamai. Ko da masu digirin farko, ana ba su girma da kalmar 'magister' wadda ke nufin wani masani.

Masu digiri na uku kuma ana kiran su da 'doctor' da ke nufin likita ko da kuwa ba likitocin ba ne.

A kasar ba sa karbar gaisuwar mike ta 'Hello' a Turance wadda ke nufin sannu, har sai idan kana da alaka ta kut-da-kut da mutumin da kake gaisarwa kamar abokin kasuwanci.

Maimakon wannan gaisuwa ta 'Hello', kamata ya yi mutum ya ce "Grusez" abin da ke nufin gaisuwa ga Allah. Wannan ce irin gaisuwar da abokan kasuwanci ke yi idan suka hadu suna musabaha, a Austria wadda kasa ce ta masu bin darikar Katolika.

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

A wasu bangarorin kuma al'ummar ta Austria ba su cika takurawa ba kamar makwabtansu na arewaci wato mutanen Jamus. Idan mutum ya makara da kamar minti 10 ba a daukar hakan laifi ne, a Vienna.

Mutanen Vienna sun kasance masu alfahari da al'adarsu. Hakan ne ma ya sa za ka gan su suna gayyatar abokan huldarsu domin cin abincin gargajiya wanda a mafiya yawan lokuta ke dauke da kwalbar giya da ake kira wa lakabi da 'Grüner Veltliner' musamman a lokacin cin abincin rana.

Yadda ake zuwa birnin Vienna

Fiye da kamfanonin jirage 60 ne ke yin jigilar mutane kai tsaye zuwa Vienna. Ana bi ta filayen jiragen Franfurt da Zurich da kuma birnin London.

A bara, filin jirgin na Vienna wadda aka yi wa kwaskwarima ya karbi bakuncin fasinjoji miliyan 23. Kuma jirgin kasa ne yake daukar fasinjoji daga filin jirgin zuwa cikin birnin na Vienna, a cikin minti 16 kuma a kan kudi $12.25.

Maganar da ta fi shahara ita ce zama a birnin Vienna babu tsada idan aka yi la'akari da kasancewarsa babban birni a nahiyar Turai.

Ana samun abincin rana a kan $11 sannan kuma kwalbar giya ba ta wuce $4.50.

Sai dai kuma wani daban shi ne dole ne mutum ya rinka yawo da kudi a jikinsa. Shaguna da gidajen cin abinci masu dama ba sa amincewa da katin biyan kudi.

Mafi yawancin 'yan kasuwa suna rufe shaguna ne da misalin karfe 19:00 sannan kuma ba a budewa ranar Lahadi.

Wurin zama a Vienna.

Akwai otal-otal da yawa masu gado 65,000, a birnin na Vienna. Ga mutanen da suke son zama a otal din yake da abubuwan tarihin kasar, akwai Hotel Sacher, daya daga cikin otal-otal din da aka yi a kan doron tarihi.

Abinci da Gahawa

Shan gahawa wani abu ne da ake girmamawa a Vienna. Abin da ya janyo wannan dabi'a dai a tarihance shi ne wasu sojojin kasar Turkiyya ne suka manta da buhun gahawa guda biyu, a lokacin da suke son su shiga birnin domin yaki, a karni na 17.

Abubuwan yi lokacin da ba a aiki

Mutum zai iya kashe kwarkwatar idanunsa da yawon ganin manya-manyan gidajen alfarma da gidajen tarihi, a lokacin da ba yin komai.

idan ka ware awa daya kacal domin yin tafiya a fadin Vienna, za ka ga irin kyawun da ake fada dangane da birnin.