Ka san matsalar tara kayan sawa da yawa?

Wani abun sha'awa dangane da Joshua Becker a kowace safiya, shi ne rashin ɓata lokaci wajen zabar suturar da zai sanya saboda tufafinsa ba su da yawa.

Becker wanda ya wallafa wani littafi mai suna 'The More of Less' wato Kaɗan mai amfani. Littafin dai wani bangare ne na wata ƙungiya mai suna 'Project 333', a inda 'yan kungiyar suke sanya tufafi 33 har tsawon watanni uku.

"Ni a wurina wannan shi ne yadda ya fi dacewa a sanya tufafi," in ji Becker wanda ya zauna a Peoria na Arizona da ke Amurka.

Yanzu haka dai Becker yana ajiye kayan sawa 30 ne kawai a adakarsa ta ajiye kaya. Ya ce " Ba na ɓata lokaci wajen zaben kayan da zan sa, a kullum."

Marubuta na cewa yanzu haka mutane sun fara gane rashin amfanin tara abubuwan da ba ka bukatar su.

Kuma mutane irin su Becker sun fara daga mallakar tufafin da yake da bukata.

Hakkin mallakar hoto Mark Zuckerberg Facebook
Image caption Kayan sawar Mark Zuckerberg
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai kamfanin shafin Facebook, Mark Zuckerberg

Irin wannan dabi'a ce mamallakin shafin sada zumunta, Mark Zuckerberg ya dauka, a inda yake sanya tufafi iri ɗaya a kullum.

Ita ma Karl Lagerfeld wadda mata ke kwaikwayo wajen sanya tufafi, sutura iri daya take maimaita sanyawa a kowace rana.

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Amurka, Barack Obama, a kullum yana sanya kwat da wando mai launin zargina ko kuma ruwan toka.

Yayin da wasu dai suna da ra'ayin ajiye kayan sawa guda 10 tare kuma da wasu karin kayan sanyi ko zafi, wasu kuwa suna ganin abin da ya kamata su yi shi ne mallakar sutura guda 33 da suka hada da sauran wasu abubuwan da mutum zai yi ado da su .

"Hakika mutane suna fahimtar gwargwadon abin da zai wadatar da su." in ji Courtney Carver, wata tsohuwar shugabar tallata haja wadda kuma ta fara kafa tsarin mallakar tufafi 33 wato 'project 333', domin yin gwaji, kimanin shekaru shida da suka gabata.

Yadda za a cimma mallakar kaya kaɗan

Ga mutanen da suke da niyyar share adakarsu ko kuma akwatinsu ta kaya, to hakan yana tattare da kashe kuɗaɗe masu kauri.

Carver ta kashe abin da ya gaza Dala 1,000 a duk shekara wajen sauya kayan da suka nuna alamun gajiya.

Hakan kuwa ya sha banban da fiye da Dala 6,000 da take kashewa a baya, a kowace shekara wajen sayen kayan zamani, duk wata.

maimakon sayen kaya kowane mako, yanzu Carver tana leƙa shagunan kaya fiye da sau uku a shekara domin ta ga irin kayan da take son saya.

"Idan na je shago sayen kaya, dabarun tallace-tallace ba sa jan hankalina." in ji Carver

Jennifer Baumgartner wadda ta rubuta littafin 'You are What you Wear' wato tufafin da ka sanya su suke nuna irin yadda kake kuma kwararriya a fannin ilimin sanin halayyar dan adam, takaice kayan na sawa yana da amfani wajen yawan tunani.

Ta ce idan ka mallaki tufafi dai-dai gwargwado, hakan zai taimaka wajen mallakar iya abin da kake bukata.

Ta kara da cewa " mu na kokarin ba wa abubuwan da muka mallaka ma'ana abin da kuma a zahiri ba haka ba ne."

"Babu dalilin da zai sa tufafin da muka mallaka su sa mu a cikin wani hali ba ko dai na farin ciki ko kuma akasin haka."

Ba a takaice iya yawan tufafin da mutum ya kamata ya mallaka ba, in ji Jennifer Scott wata marubiciya da ke zaune a Los Angeles, wadda kuma take da kayan sawa guda 10 a adakar ajiyar kayanta.

Adakar ta Scott dai ta kunshi riga da wando guda uku da wandon jeans guda biyu da rigunan bulawus guda uku da dan tofi da kuma wata rigar mai gajeren hannu da kuma kayan zanzaro kamar belet da jaket da rigunan sanyi.

Idan mutum yana son ya dade da kaya kaɗan to sai ya sayi kayan da za a iya amfani da su a yanayin zafi ko sanyi ko damuna.

Carver ta ce "ina sanya kayana masu sarau-sarau na kuma cire kayan da na ke zuwa aiki da su, idan ba na aikin."

Takaita yin amfani da tufafi masu yawa, ya na da mafani dangane da yadda mutum ya ke tunanin.

Hakan zai taimaka wajen rage wahalar da ke zuwa saboda tunanin yanke hukunci wajen zabar abin da mutum zai sanya.

Carver ta ce mafi yawancin mutane suna fara koyon tunani ne tun daga zabar abin da za su zaba na sanyawa, abin da kuma daga bisani yake shafar sauran ayyukan gida.

Abin da ya kamata ka yi

Becker ya ce ya ce ya fara da yin gwaji na zabar tufafi masu kwari da za su iya jure wanki da kuma sanyawa yau da kullum.

A bayan-bayan nan, Becker ya daina sayen irin kayan da ransa yake so na ƙwalisa, misali ya daina sayen kamfai mai aljihu saboda ya lura aljihun na yagewa da wuri.

Becker dai ya fi mayar da hankalinsa kan sayen riguna masu kwari da ba sa canzawa bayan shan wanki.

Ya ce "Ba zan sayi kayan da ba su da kwari ba."

Masu takaita kayan sawa kamar Scott, sun yi amannar cewa takaice kayan na sawa ba wai na nufin rashin tafiya da kayan zamani kuma na 'yan kwalisa ba.

Mutane da dama suna da ra'ayin cewa amfani da tufafi marasa yawa na ba wa mutum saukin wajen "yin irin adon da ka ga dama dai-dai da zamani." in ji Scott.

"Akwai kayan da ake shigar asin-da-asin da su kuma suke sanya mutum ya fito ya yi fes da shi." in ji Scott.

Scott dai tana banbance akwatinan kayanta. Daya ta kayan wurin aiki da kuma ta kayan yau da kullum.

Maganar da ta fi shahara, ita ce ba dukkan mutanen da suke da ra'ayin mallakar kaya kadan ne suke daina shiga shago ba kwata-kwata.

Maimakon mutum ya cirewa kansa ra'ayin ƙwalisa gaba daya, Scotta ta ba da shawarar cewa mutum zai iya rinka zuwa shagunan sayar da kaya yana ganin su amma ba wai lallai sai ya saya ba. idan ka na son karanta na turanci za ka iya latsa wannan People with few clothes in their closet