Me ya sa wasu ma'aikata ba sa iya hutu har ran Asabar?

Hakkin mallakar hoto PA

Kana fama da matsalar waiwayar aiki har a daren Asabar, lokacin da ya kamata ka huta?

To wannan za ta iya kasancewa wata matsala da ta danganci yanayinka, amma akwai hanyoyin da za ka yi maganin matsalar.

Zaria Gorvett ta yi mana nazari.

Da karfe tara na dare ranar Juma'a suke tashi daga aiki, amma kuma har karfe uku na dare suna duba wasikunsu na email.

A ranar hutu ma suna taruka ta waya a kan harkokin aikinsu, ko tashi suka yi daga barci suna tunanin wa'adin wasu ayyukan da ke gabansu, kuma hatta irin surutan nan da mutum kan yi idan yana barci na aiki suke yi.

A fadin duniya burin mutane da masana'antu masu takurawa da fasahar yadda ma'aikaci zai samu damar yin aiki a duk tsawon saa'a 24, wato duk tsawon rana da dare na daga abububwan da ke sa mutane damuwa da fargaba a kan aiki.

Cibiyar binciken abubuwan da suka shafi damuwa ta Amurka, ta yi kiyasin cewa takurar aiki tana jawo wa Amurka asarar dala biliyan 300 a duk shekara.

Wani bincike da kamfanin hada-hadar sufuri ta intanet, Expedia, ya yi ya gano cewa kashi 53 ne kawai cikin dari na ma'aikata suke jin wasai, babu gajiya a tare da su bayan hutu.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Ba ka iya hutawa da aiki hatta a gida? To kana bukatar sauya tunaninka

A Burtaniya akwai abin da ake kira larurar Asabar, wadda wani yanayi ne na yuwuwar ma'aikaci ya gamu da rashin lafiya a lokacin da ba ya aiki, abin da ake gani na faruwa ne a sanadiyyar daukar matakin magance gajiyar aiki.

A Amurka akwai makon abin da ake kira makon aiki na saa'a 60, dabi'ar da ake gani tana linka hadarin gamuwa da bugun zuciya. A Japan har ma ana sanya wa matsalar suna inda ake kiranta da karoshi, ko mutuwa a sanadiyyar gajiyar aiki.

Ga ma'aiakatan ofis irin su Samantha King, wadda manaja ce a fannin harkokin kudi a Landan, hatta zaman hutawa ma wahala ne a wurinta.

Ta ce, ''idan ba ka yi wani abu ba a shafinka na Facebook ko Instagram ko wani abu a shafukan sada zumunta na muhawara na intanet, mutane za su rika tambaya lafiya kuwa''

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Wani bincike ya gano cewa kusan rabin yawan ma'aikata ne kawai suke amfana da hutu

Za ka ga yayin da wani ma'aikaci ke fama da wahala da gajiyar aiki wani kuwa ko a jikinsa duk kuwa da cewa ya ma fi wancan dayan tarin aiki a gabansa. Ko me ya sa haka?

Idan ka bari gajiyar aikinka ta bika har gida, wato ka je gida kana ta tunani da yin wasu abubuwa da suka jibanci aikinka to kana cutar da kanka, in ji Jennifer Ragsdale,masaniya a kan tunanin dan'adam a jami'ar Tulsa, a Oklahoma da ke Amurka.

Tsawon shekaru masu nazari sun yi kokarin fayyace bambancin da ke tsakanin amfanin hutun ma'aikacin da ya yi karshen mako yana ta yin abubuwan da suka danganci aikinsa da kuma wanda ya yi watsi da duk wani abu da ya shafi aikin ya je teku ya shakata, ko ya kwanta a daki kawai ya huta abinsa.

Ragsdale ta ce, ''a nan mutane biyu ne ke cikin yanayi daya, amma kuma kowa da irin yadda zai yi a sakamakon hakan, wato martanin kowannensu zai zama daban.

Wartsakewa

Maganar wartsakewa daga gajiyar aiki ta fara daukar hankalin Ragsdale tun a shekarar 2011, lokacin da ta lura da bambancin wartsakewar da ke tsakanin abokan aikinta.

Ta lura cewa yayin da wani zai dauki dan lokaci kadan ya wartsake daga gajiyar aiki wani kuwa zai dauki lokaci mai tsawo. Tun daga wannan lokacin ne ta fara kokarin gano yadda lamarin yake.

A nazarin da ta yi a kan ma'aikata 183 daga masana'antu daban-daban, a ranar Lahadi da yamma sun bayyana yadda suke hutunsu na karshen mako, da kuma yadda suke ji sakamakon hakan.

Ta kasa abin da ma'aikatan ke yi a lokacin hutun gida biyu. Kashi daya abu maras wahala (kamar wanka a shaya) dayan kuwa wanda ya danganci aikin ofis kamar amsa wasikun email

A gaba kuma sai aka ba jarraba su wadannan ma'aikatan domin sanin yanayin yadda za su ji. An ba su jerin abubuwan da za su sa su ji dadi da kuma wadanda za su bata musu rai, aka kuma bukace su da su bayyana yadda suke ji.

Kamar yadda za ka yi tsammani, rukunin mutanen da suke da yanayi mai kyau sun fi wartsakewa daga damuwa ko gajiyar aiki cikin sauki.

Su kuwa masu yanayi na damuwa ko masu saurin fushi da wuya suke wartsakewa, duk abin da suka yi, hankalinsu ba ya daukewa daga damuwar aikin nan.

Idan ma suna tunanin shiga sabon mako abin na kara ba su haushi saboda aikin da suke tunani za su shiga.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Idan kana da damuwa, hatta zaman kallon talbijin a lokacin hutun karshen mako ba zai yaye maka damuwar aiki ba

Sai dai lamarin kusan ya fi yadda muke dauka sauki, domin mutane suna da bambanci. Wadanda suka fi yin fice a bangaren rashin damuwa, suna daukar duk wani kalubale ne a matsayin abin da za su lakanta har su yi nasara a kansa, maimakon su dauke shi a matsayin wani abu da zai gagare su ko wanda ba za su iya maganinsa ba.

Ragsdale ta danganata wannan ga halittarmu ta kin da yake da wuya ko maras dadi, domin shi mutum a karan kansa idan zai samu dama to zai kauce wa duk abin da ba zai ji dadinsa ba.

Ragsdale ta ce, ''dukkanninmu muna fassara yanayin da muka samu kanmu daidai da fahimtarmu wadda ba lalle ta zama daya ba. Babu wani tsari daya da za a ce ya dace da kowa wajen magance matsalar damuwa ko gajiya.''

Ga masaniyar tunanin dan'adam a kan harkokin aiki da kasuwanci Jane Clarke, kokarin hutawa ma takura ne ga aikinsu, domin tunanin cewa akwai aiki a gabansu na iya hana su sakin jikinsu su huta

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Wasu ma'aikatan na bukatar su fita, su shakata

Haka ita ma Corrine Mills, kwararriya kan koyar da harkokin aiki, wadda ke Landan take gani. Ta ce, '' wasu mutanen ba sa iya zama a daki cikin duhu kawai su huta, sai sun fito sun yi wani abu na motsa jikinsu.

A nan Mills ta bayar da shawara yin wani abu kamar na motsa jiki, ko kawai mutum ya fita tattaki zuwa wani gandun shakatawa, ko dai yin duk wani abu da zai dauke maka hankali daga aiki na 'yan wasu mintina.

Idan kana daga cikin irin mutanen da suke da matsalar kasa wartsakewa daga gajiya ko damuwar aiki a karshen mako, akwai yadda za ka iya sauya yanayinka, wato tunaninka.

Tun da abin da ke sa mu wartsakewa ya shafi halayyarmu ne, ba wai wani aiki ba, akwai hanyoyin da za mu sauya yadda muke tunani.

Ragsdale ta bayar da shawarar koyon yadda mutum zai iya sauya tunaninsa ya zama mai kyau. Mutum ya rika tunanin alheri a aikinsa maimakon ya rika tunanin yadda ba ya jin dadin aikin ko kuma wahalar da ke tattare da aikin, abin da ke sa ya ji aikin ya dame shi.

Nazarce-nazarce sun nuna cewa yin wannan dabara ta yin tunani mai kyau a kan aikinka, ka iya rage ma damuwa da gajiyar aikin, kuma hakan zai kara maka basira da cigaba da kuma hadin kai bayan wata shida.

Idan har ka yi nasarar sauya wannan dabi'a taka a game da aikinka, za ka ga ba da dadewa ba ka fara neman yadda ma za ka yi da lokacin hutun naka (ka rasa ma abin da za ka yi).

Amma fa kada ka manta cewa za ka je wurin aiki ranar Litinin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. This is why you can't switch off at the weekend