Mafi yawan 'yan wasannin Olympic talakawa ne

kana zaton cewa duka 'yan wasannin Olympics attajirai ne? Sam ba haka ba ne. Da daman su suna neman ayyukan da za su riƙe kan su.

Yayin da Serena Williams ta shiga filin wasannin Olympics a birnin Rio a watannan, tauraruwar ta wasan tennis 'yar Amurka ba ita kadai ta shiga fili ba. Ta je wasannin ne da tawagar ma'aikata da ta ke biya albashi, da masu horar da ita, da masu ɗaukar nauyin ta, wadan da suke taimaka mata a duk motsin da ta yi.

'Yar wasar wacce ta ke da kudin da ya kai dala miliyan 150, (hakan ya sa ta zarce duk wata 'yar wasa kudi a duniya) ta na yin atisaye na sa'a talatin a kowane mako, to amma fa banda wannan ba ta da wani aiki da take dan neman albashi.

Irin su dai ba su da yawa a cikin 'yan wasannin Olymipcs.

Hakkin mallakar hoto EPA

Idan kana yawo a birnin Rio da ake wasannin Olympics, wataƙila ka yi kiciɓis da mutane irin su Donna Vakalis 'yar ƙasar Canada. Tana yin atisaye na sa'o'i 30 a kowane mako dan fafatwa a wasan shallaken sanda a kan dawaki, da wasan lanƙwaya, da wasan jifa, da nunƙaya, da tseren dawaki, da kuma gudun yada ƙanin wani.

A duk lokacin da ba ta atisaye kuwa 'yar wasan mai shekaru 36 tana ci gaba da ƙoƙarin samun digiri na uku ne a ɓangaren fasahar gine-gine a jami'ar Toronto, sannan kuma ta na wasu 'yan aikace-aikace dan samun kuɗin da za ta cimma burinta na wasannin Olympics.

Vakalis ta ƙiyasta cewa tana buƙatar kuɗin Canada dala dubu hamsin ($39,000 US) a shekara dan yin atisayen wasan shallaken sanda a kan dawaki na zamani, to amma sabo da ba ta yi rijista ba tana da giɓi sosai, domin abinda ta ke samu daga gwamnati bai wuce dala dubu hudu da ɗari biyar ba a kudin Canada ($3,450 US).

Hakkin mallakar hoto Getty

"Da kanmu mu ke biyan masu horar da mu, mu mu ke biyan kudin cibiyar wasannin da kan mu, mu ke biyan masu kula da lafiyar mu, da masu yi mana tausa, hakan na nufin akwai nauyi sosai a kan mu". A cewar ta.

Hakan dai ya sa Vakalis ta ke ta fafutukar neman kuɗi ta hanyar koyarwa ta ɗan wani lokaci, da taimakawa masu bincike, da kalaman ƙarfafa gwiwa, da kuma kula da shafin YouTube na wata jami'a.

Ta na kuma neman tallafi na kuɗin da aka ware wa wasannin Olympics da ma kuma sauran hanyoyi na samu kuɗi daban-daban ciki kuwa har da amfani da shafukan Internet, inda ta ke sayar wa magoya bayanta kayayyaki domin taimaka mata.

Ba wai Vakalis ce kaɗai ke cikin irin wannan mawuyacin halin ba, wani rahoto na baya-bayannan ya gano cewa 'yan wasannin Olympics na Canada na kashe kimanin dala 14,920 ta Canada, sama da abin da su ke samu daga gwamnatin tarayya da gwamnatocin shiyya. Kuma kashi 20 daga cikin su na fama da bashin da ya kai dala 40,000 na kuɗin Canada.

A baya, iyalan 'yan wasan Olympics a Amurka sun nemi gwamnati ta kai musu ɗauki kan mummunan talaucin da su ke fama da shi, da bashin kuɗaɗen horarwa, da tafiye tafiye.

Hakkin mallakar hoto Getty

Akwai 'yan wasannin Olympics sama da su 100 a ƙasashen duniya da dama da suke neman tallafi daga jama'a ta shafin internet na GoFoundMe.

Haka kuma akwai 'yan wasannin Olympic da su ka yi atisaye domin wasannin Rio, yayin da a ɓangare ɗaya kuma su ke ci gaba da wasu harkokin na neman kudi.

'Yan wasan dai za su bar birnin Rio nan da 'yan kwanaki a matsayin gwaraza na duniya, amma fa na ɗan wani lokaci. To amma da daman su sun shiga wasan ne a matsayin mutane gama gari da bashi ya yi wa kanta.

Ƙasa da daƙiƙa ɗaya ta ragewa ɗan wasan kurmanu na ƙasar Australia Mattew Abood ya samu cancantar shiga wasannin Olympics cikin 2012 a birnin London. Ba wai gaza shiga gasar kawai ɗan wasan ya yi ba, ya ma rasa samun tallafi daga gwamnatin Australia.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabo da rashin samun kuɗi daga gwamnatin Australia da kuma rashin samun cancantar shiga wasannin Olympics a London a 2012, Mattew Abood ya ƙirƙirawa kansa wani tsari na tanadi domin samun shiga wasannin Olymipcs a Rio.

"Na tuna tambayoyin da na ringa yi wa kaina, Me ya kamata in yi? Ba ni da aiki, kuma ba karatu na ke ba, ni ba wani aiki na iya ba" In ji Aboot.

Ya tunkari baban bankin Australia da wani tsari da ya yi na shekara hudu, ba wai dan cimma burin sa na shiga wasanni a Rio ba kawai, har ma domin ya samu wata sana'a da zai dogara da ita.

Abood ya na aikin kwanaki biyu a mako a matsayin masani kan bunƙasa kasuwanci ga babban bankin na Australia tsawon shekaru huɗu.

Ya ce kuɗin da ya ke samu ya taimaka masa wajen samun horon da ya bashi damar shiga wasan kurmanu a Rio, buri ne dai da ya daɗe yana son cimmawa, sai dai ya cika burin sa da gumin goshi.

Ba kamar 'yan wasan Olympics na sauran kasashe ba, yan wasan Olympics na Amurka ba sa samun tallafin kuɗi kai tsaye daga gwamnati. Hakan ya sa sai dai su dogara kan tallafi daga hukumomin gudanarwar wasannin su daban-daban.

Asusun tallafawa 'yan wasannin motsa jiki na Amurka ya ce idan mutum yana so ya ɗauki nauyin kan sa zuwa wasannin Olympics, zai iya kashe dala dubu 12 zuwa dala dubu 120 a shekara, domin horarwa, da kudin sufuri, da sayen kayayyaki. A Amurka ana neman talafin kudi dan 'yan wasannin Olympics, wanda wata hukuma ta ke kula da su.

"Ba wai 'yan wasan na Olympics ake bawa kuɗaɗen ba har tsawon rayuwar su, domin su ci abinci, su sayi motoci, sannan su ci gaba gudanar da rayuwar su" A cewar Augie Wolf, wani tsohon ɗan wasannin Olympics na Amurka, wanda kuma ya kafa asusun tallafawa 'yan wasannin na Olympics.

Ya ce mafi yawan 'yan wasan a Amurka suna rayuwa ne cikin ƙunci, suna bara, suna rancen kudi, ko kuma su dogara kan kuɗin jin ƙai da wasu ke samarwa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wolf ya ce "Mafi yawan 'yan wasan suna rayuwar taimake ni-in taimake ka ne, za ka ga mutum uku na zaune a gida mai ɗaki biyu".

wanɗanda suka gaza samun isasshen kuɗin da zai ishe su gudanar da al'amuran yau da kullum, suna neman wasu ayyukan da za su iya basu damar yin atisaye a wasu lokutan daban. Wasu 'yan wasan na Olympics kuwa suna yin atisaye ne a lokacin da suke aiki a wurare kamar su McDonalds, da dillancin gidaje, da kuma aikin soja.

Muhimmiyar Dama.

Duk da ya ke waɗanda suka shiga wasannin Olympics karon farko suna matuƙar shan wahala, a 'yan shekarun nan abubuwa na inganta, a cewar masanin tarihin wasanni Mark Dyreson, kuma farfesa a jami'ar Pennsylvania ta Amurka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu 'yan wasan na Olympics kamar Usain Bolt na samun miliyon kudade daga ɗAukar nauyin sa da ake yi da kuma tallace tallace. To sai dai wasu sai sun nemi aiki don samun kuɗin abinci

A yanzu kana da 'yan wasannin Olympics kamar ɗan tsere Usani Bolt na Jamaica, da kuma ɗan Kurmanu Michael Phelps na Amurka.

Ga matasa masu shiga wasannin Olympics, samun damar zuwa gasar ma kawai na iya sa wasu su dauki nauyin ka, ba ma a ma ganar ke shiga fili. Hakan dai wata babar dama ce. To amma fa gwaji ne kawa za a yi ko za a dace. Domin tamkar kasada ce, kuma ba ka da tabashin cewa haƙarka za ta cimma ruwa.

Kuɗi ba ya samuwa ga 'yan wasannin Olympic, sai bayan an kammala wasannin. Wannan ne lokacin da suke bibiyar mutanen da suka ƙulla wata magana da su, dan ɗaukar nauyi da kuma bada labaran irin muhimmiyar rawar da suka taka a lokacin wasannin na Olympic.

Idan ka na son karanta wannan labari a harshen Ingilishi latsa nan. Many Olympians struggle just to make ends meet