Me ye dangantakar aikinmu da kimarmu a rayuwa?

Me ye sa mu ke tambayar mutanen da mu ka hadu da su aikin da su ke yi? Hakan na iya zama alamar mummunar alaka tsakanin aikinmu da kuma sanin mu su waye. Cikin minticon farko na fara tattaunawa da bakin ido, akan tambayi Yasaman Hadjibashi abinda aka saba tambayar kowannenmu: "Wane aiki ki ke ne?"

Da gangan ta ke kin bada amsa kai tsaye.

Ta na iya fadar digirin MBA da take da shi daga Jami'ar Harvard, ko kuma matsayinta na babbar jam'ia a bankin Barclays Group Africa. Maimakon haka, Yasaman kan bada amsar da take fatan za ta bambance tsakanin rayuwarta da kuma aikinta. Ta ce "Zan so mutane su san ni tukun kafin su san me ye aiki na. Hakan kuma kamar wani gwaji ne in ga ko za su mutuntani ba tare da sanin matsayina ba?"

Hakkin mallakar hoto iStock

Ba Hadjibashi ce kadai ke kokarin bambance tsakanin rayuwarta da aikinta ba: kwararru akan harkokin aiki sun ce ko mutanen da suka samu gagarumar nasara a sana'o'insu za su yi amfani da bambance tsakanin waye su da kuma me suke yi.

Rarrabe tsakanin rayuwarka da aikinka na rage alhini idan ka rasa aiki, ya na bada damar kulla kyawawan alakoki a wasu harkokin da basu shafi ofis ba, sannan kuma ya na sa mutum jin kimarsa ba ta ragu ba idan ya bar wani babban aiki.

Sai dai kuma a wannan zamani da kamfanoni da dama ke bukatar ma'aikatansu su mai da hankali dari bisa dari kan ayyukansu, abu ne mai matukar wuya ga ma'aikata da dama su rarrabe tsakanin rayuwarsu da kuma aikinsu. Hakan zai iya sa musu rashin jin dadin rayuwa kamar yadda Al Gini, malamin harkokin kasuwanci a jami'ar Loyola ta Chicago kuma mawallafin littafin 'Aikina, Rayuwata' ya bayyana: "Karancin abubuwan yi a waje na sa mu kara dogaro da ayyukanmu. Don haka da zarar mun rasa aikin sai rayuwarmu ta sukurkuce."

Hakkin mallakar hoto Alamy

Hakika, ma su tambayarmu aikinmu na kokarin gano matsayinmu cikin al'umma, kamar yadda a wasu al'ummomi na nahiyar Asiya akan damu da sanin iyaye da kakannin mutum tare da arzikinsu maimakon sana'a in ji Ho Shee Wai, mai ilimin halayyar dan Adam kuma darakta a cibiyar Counselling Place da ke Singapore.

Sai dai duk da cewa mutane kan tambayemu aikinmu ko sana'armu ne domin su san matsayin da zasu ajiye mu, bayyana sunan kamfanin da ka ke wa aiki ko kuma matsayinka a sana'a na iya sa mutane su alakanta kimarka da aikin da watakila ma kokari ka ke ka bar shi. A cewar Ho Shee Wai; "Kar ka yadda aikinka ko sana'arka su zamo ma'aunin kimarka."

Barin aiki a gefe

Mutanen da ke alakanta kimarsu da sana'o'insu ko aikinsu kurum na iya shiga matsananciyar damuwa duk lokacin da su ka rasa su, yayinda wadanda ba haka su ke ba za su iya girgijewa cikin hanzari, a cewar Susan Krauss Whitbourne, farfesar ilimin halayyar dan Adam a jami'ar Massachusetts Amherst da ke Amurka. Ta kara da cewa abinda zai kawo nisanta aiki da rayuwa shi ne kokarin tattauna abubuwan da basu shafi aiki ba da abokai da kuma 'yan uwa.

Amma ma'aikatan da su ka fi gamsuwa da ayyukansu su ne ma su ka fi bukatar nisanta rayuwarsu da aikin.

Ma'aikatan da ke jin dadin aikinsu saboda ganin muhimmancin abinda su ke yi ko kuma annushawar da su kan samu a wurin aiki, su ne su ka fi alakanata rayuwarsu da ayyukansu fiye da wadanda su ke yi don kudi ko matsayi, a cewar wani bincike da Krauss Whitbourne ta gudanar.

Hakkin mallakar hoto iSTOCK

Ta kara da cewar, ko da yake jin dadin aikinka na sa ka farin ciki a rayuwa, hakan na sa raba tsakanin aikinka da rayuwarka ya wahalar kwarai da gaske.

Matakan samun 'yantacciyar kima a rayuwa

Na farko, ka gabatar da kanka bisa kwarewarka ba tare da ka dangana da kamfanin da ka ke aiki ba ko kuma matsayinka a kamfanin, in ji Francois Daumard, wani jami'in fasahar sadarwa da ke San Francisco. Lokacin da Daumard ya sauya wurin aiki daga Microsoft zuwa Apple, sannan ya koma wani kamfanin da bai shahara kamar wadannan ba sai ya koma gabatar da kansa a matsayin kwararre a harkar fasahar sadarwa ba tare da ambaton kamfanin da ya ke wa aiki ko matsayinsa a kamfanin ba.

Wannan dabarar ta taimaka masa wurin tsare kimarsa musamman a idon mutanen da ba su da alaka ta kusa da shi.

Sai dai, dabarar da tafi ci ga mafi yawan mutane, ita ce samun wani abin debe kewa mai muhimmanci, wanda bai danganci aikinsu ba, a cewar Krauss Whitbourne, wacce ke bada sa'o'i da dama cikin mako guda ta na sakar tuma-kasa.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Ta ce; "Kamata ya yi ki dauki wannan abin debe kewar a matsayin wani abu mai muhimmanci a rayuwa ba wai kawai rage lokaci ba. Ma'aikata da yawa na yin sana'o'in hannu domin debe kewa kurum kuma da zarar aiki ya fara yawa sai su yi watsi da su. Abinda ya kamata shi ne ki ba su muhimmanci ta hanyar da zaki iya gabatar da kanki a matsayin mai yin wadannan abubuwan lokacin da duk ku ka hadu da bakin ido."

Duk da Hadjibashi ta gamsu da sana'arta, ta ce irin mutanen da take hulda da su - matan aure mazauna gida, malamai, 'yan kasuwa - sun sa ba ta yadda ta alakanta kimarta kan aikin da ta ke yi kacokan ba. Idan ta na tare da kawayenta, aikinta ba ya cikin abinda su ke tattaunawa domin mutane da dama ba sa iya fahimtar aikinta. Haka kuma, alakanta kimarta da abubuwan da take yi idan ta bar wurin aiki na ba ta damar ta gudanar da rayuwa mai inganci. Ta kara da cewa; "Kasancewa tare da kawayena na ba da damar nisanta tsakanin rayuwata da aikina."

Idan kana so ka karanta wannan a harshen ingilishi latsa nan. Why you shouldnt ask people what they do