Ka san amfanin ajiye aiki?

Abinda a baya ake dauka tamkar wani gagarumin ganganci, ajiye aiki na tsawon lokaci, a hankali na samun karbuwa har ma wadansu ma’aikatun su na goyon bayan yin hakan. Ga matakan da ya kamata ka bi wurin samun nasarar hutun aiki.

Lokacin da Winston Chen ya shaidawa abokansa cewa ya ajiye aikinsa na babban jami’in fasaha a wani kamfanin shirya manhajar kwamfuta domin komawa wani karamin tsibiri a cikin hamadar kankarar Norway tsawon shekara guda tare da iyalinsa, kadan daga cikinsu ne su ka ce bai yi daidai ba. Maimakon haka, yawancin abokansa kan ne: “Ina ma ni ma zan iya.”

Yayinda mutane da yawa ke burin ajiye aiki kafin lokacin ritaya, kadan ne ke iya gwadawa. Amma adadin masu daukar dogon hutun aiki bayan sun girma na ci gaba da karuwa, a cewar kwararru a harkar.

A bangare daya, ana samun kamfanoni da dama da ke amincewa ma’aikatansu su ajiye aiki da niyyar komowa bayan wani dogon lokaci, a daya bangaren kuma mutane su na yawan sauya aiki fiye da shekarun baya. Kuma, bisa la’akari da abinda ka yi da hutun na ka, ka na iya samun aikin da yafi wanda ka bari tun san da ka tashi komawa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Lokacin sauyi

A tsarin Chen, wanda ya kwashe shekaru goma ya na aiki a kamfani guda kafin aje aikin a 2011, gani ya yi lokaci ya yi da zai samu sauyi a rayuwarsa. Niyyarsa ita ce ya nemi aiki a wani kamfanin dabam, amma bayan da ya saurari wani jawabi karkashin tsarin TED sai ya fara nazari sosai akan daukar dogon hutu.

Sai dai da fari ya yi fargabar cewa idan ya dau tsawon lokaci baya aiki, zai iya samun cikas duk san da ya dawo neman wani sabon aikin. Ya ce: “Wannan ne babban dalilin da ke hana mutane ajiye aikinsu, ni ma haka lamarin ya kasance gare ni. Amma sai ka kalli muhimmincin gudanar da rayuwa irin yadda ka ke so.”

Bayan ajiye aikin, Chen ya fara neman wani aikin na dabam – har sai da wani abokin huldarsa ya shaida masa cewa ana neman malamin makaranta a wani karamin tsibiri da ke yankin hamadar kankara a Norway.

Matar Chen, wacce aka haife ta a Norway kuma na sha’awar komawa bakin aiki bayan da ta ajiye domin rainon ‘ya’yanta tsawon shekaru biyar. “Ta kira makarantar ta waya su ka dauke ta aikin,” in ji Chen. “Don haka nan da nan mu ka yanke cewa abinda zamu yi ke nan.”

Karin karbuwa

Paul Payne, manajan darakta na wani kamfanin daukan ma’aikatan sufurin jirgin kasa da harkar gine-gine da ke Birtaniya, mai suna OneWay na daya daga cikin kwararru kan daukar ma’aikata wanda ya lura cewa abokan huldarsa da dama kan dauki hutun shekara guda su na tsaka da aiki.

Ya ce: “Wannan lamari abin lura ne, musamman a wannan lokaci da kamfanoni ke bukatar rike ma’aikatan da su ka horar, yayinda su kuma ma’aikatan ba sa son zama wuri daya.

Duk da dai ba za a ce tsarin ya dace da kowacce irin sana’a ba amma dai kamfanoni da dama na bai wa ma’aikatansu damar daukar dogon hutu tare da ci gaba da biyansu albashi don su wataya su sake dawowa bakin aiki cike da karsashi.”

Hakkin mallakar hoto iSTOCK

Tambarin lalaci

Daukar shekara guda ba ka aikin komai ba dalili ba ne da zai sa a yi maka tambarin lalaci, in ji Payne. “Ajiye aiki alama ce da ke nun aka na son koyon sababbin abubuwa.” Ya kuma kara da cewa: “Hakan kuma zai iya sa ka dawo bakin aikinka da sabon tunani, wanda zai iya taimaka wa wurin kara inganta aikinka.”

Daga cikin mutane 500 da aka tattauna da su domin rubuta littafin ‘Reboot Your Life’ wanda aka walllafa a 2011 domin ba da shawara game da daukar dogon hutun aiki, babu ko daya da ya yi nadamar daukar hutun (mai tsawon wata guda zuwa shekaru biyu), a cewar Jaye Smith, daya daga cikin marubutan littafin, kuma daya daga cikin wadanda su ka kafa kamfanin Reboot Partners a New York, mai ba ma’aikata shawara kan yadda za su ribaci rayuwar aiki.

Ta ce: “Duk kansu sun ce sun ga ci gaba a rayuwarsu sanadiyyar dogon hutun da su ka dauka daga aiki.”

Jarraba sabon abu

Idan ki na tunanin ajiye aikinki domin fadada tunaninki da samun karin kwarewa, kamata ya yi ki tafi wata kasar dabam, inda za ki yi aikin sa kai ko karamar sana’a, wadanda za su kara mi ki kaifin tunani idan kin koma bakin aikinki na baya, a cewar Payne. Wannan aikin kuma zai iya kara miki kwarewa akan aikin da ki ka bari.

Ya ce: “Wa ya san iya abinda za ki iya koyo idan ki ka yi aiki tare da wasu kwararrun, da su ka samu horo a wani yanayi da ya bambanta da irin wanda ki ka taso a ciki?” Ya kara da cewa: “Irin wannan dogon hutun na iya bunkasa kwarewarki ta hulda da jama’a da dabarun warware matsaloli, duba da yadda masu aikin sa kai ke fama da karancin kayan aiki.”

Hakkin mallakar hoto Getty

Akwai hatsari

Sai dai, ba kowacce ma’aikata ce za ta amince ma’aikatanta su dauki hutun shekara guda ba – amma akwai hanyoyin da za ki iya nuna musu muhimmancin hakan, a cewar Holly Bull, shugabar wani kamfani bai wa ma’aikata shawara game da daukar dogon hutu, da ke New Jersey a Amurka.

“Ki bayyana wa ma’aikatar kudirinki da kuma ribar da ki ka ganin za su iya samu sakamakon wannan hutun, mai yiwuwa su amince idan su ka tabbatar bayan hutun za ki koma aiki da su.”

Bull na ganin ke ce ya kamata ki san abinda ya fi muhimmanci a rayuwa: “Idan ba su yadda ba sai ki ajiye mu su aikin dungurungum.”

Lokacin tafiya ya yi

Daukar hutun shekara guda na iya zama hanyar samun aikinki na gaba. “Ina ga ya kamata mutane su tambayi kansu idan sun gamsu da aikin da su ke yi. Idan ba su gamsu ba, mutane da yawa kan ji tsoron sauyawa, amma dai na tabbatar gara ki nemi aikin da ki ke so da ki makale a inda ba kya jin dadi,” in ji Bull.

Ta kuma bayyana cewa “Daukar dogon hutu wata dama ce da za ki jarraba sabon aikin da ki ke sha’awa, idan bai yi miki ba sai ki koma wanda ki ka ajiye.”

Hakkin mallakar hoto Alamy

Wasu mutanen kan gane ko aiki ya yi mu su ko bai yi mu su ba cikin ‘yan makonni kadan, amma ita Bull sai da ta yi wata guda cur ta na aikin binciken ciyayen cikin ruwa, kafin tabbatar da cewa ba ta da juriyar da za ta iya mai da shi sana’arta.

A kan tsinci dami a kala

Shi kuwa Chen, a lokacin hutun ne ya kirkiro wata manhajar wayar salula domin debe wa kansa kewa. Wannan manhaja ita ce ta zamo tushen kafa sabon kamfaninsa, Voice Dream lokacin da ya koma Boston bayan shekara guda.

Ya ce: “Ba dole ne ka dauki hutu da niyyar kafa sabon kamfani ko sauya sana’a ba. Abin lura shi ne: Idan aka dauke maka bukatar kudi ta dan wani lokaci, me za ka yi domin jin dadin rayuwarka?”

Idan kan so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The surprising benefits of a mid-career break.