Dabi’un Turawa sun zama abin alfahari a China

Hakkin mallakar hoto Darcy Holdorf

Wasu mata ‘yan China ne zaune reras kan kujeru, kayatattun jakunkunansu na ajiye daura da kafafuwansu, su na sauraron wani mai daukar hoto a mujallar Tatler ta kasar China, cikin nutsuwa ya na wassafa musu yadda ake bayyana cikin jama’a.

Ya na musu bayani game da kwalliya da haskaka kundukuki. Dakin ya sha kwalliya da takardar kawata bango ta Pierre Frey, yayinda matan ke shan shayi daga kofin tangaran na Bernardaud. Su na rike da takardu, su na daukar darasi kan yadda ake zaman daukar hoto.

Darasin mai taken “Yadda ake zaman daukar hoton hamshakai” na daya daga cikin darussan da ake koyarwa a cibiyar Sarita, wata makarantar koyar da tarbiyyar Turai da ke horar da sababbin masu kudi na kasar China.

Sauran darussan da makarantar da ke unguwar ‘yan gayu ta Sanlitun da ke Beijing, sun hada da yadda ake rainon yara, tarbiyyar cin abinci, da yadda ake furta sunayen kayayyakin kasaita.

“Mafi yawan dalibaina sun yi abin kunya ne a kasashen waje ko kuma wurin liyafar kasuwanci. Su kan zo nan ne domin saukaka wa kansu jin kunya,” in ji Sara-Jane Ho, wacce ta kafa makarantar, a yayin da take zaune cikin dakin da aka kawata shi da tsofaffin kujerun alfarma na Faransa.

“Yawanci mu na koyar da yadda ake mu’amala ne a kasashen waje,” in ji Ho, wacce ta yi karatun tarbiyya a Institut Villa Pierrefeu da ke Switzerland, daya daga cikin makarantar horar da ‘yan mata tarbiyyar hamshakai da su ka rage a duniya.

Kawo yanzu dai ta samu daruruwan masu kudin China da ke halartar makarantarta. A nan gaba kadan za ta bude reshe a birnin Shanghai.

Kasar China dai na da hamshakan masu arzikin da dukiyarsu ta zarta dala biliyan guda har su 190, kuma ta na da miloniyoyi fiye da dari biyu, inda ta ke matsayi na biyu a bayan Amurka, a jerin kasashe masu yawan masu kudin gaske, a cewar wani bincike da mujallar Forbes da kamfanin Boston Consulting Group su ka gudanar.

Mafi yawan masu kudin sun yi arziki cikin dan kankanin lokaci daidai da bunkasar tattalin arzikin China da yawaitar hanyoyin samun kudi. Wasu daga cikin sababbin masu kudin nan na da karancin sanin yadda ya kamata su yi hulda da ‘yan kasashen waje a harkokin kasuwanci ko mu’amalar rayuwa.

“Shekaru 30 da su ka wuce kasar China a ware take,” in ji Ho. “Bunkasar tattalin arziki ya zo mata na kamar kiftawa da bisimilla. Don haka sauyin ya janyo takura da yawa akan mutane.”

Sakamakon haka, wasu ‘yan kasuwar ba su da kyawawan dabi’u wurin hulda da Turawa ko ma takwarorinsu na nahiyar Asiya. Yayinda kyakkyawar mu’amala kan sa a samu nasara a harkokin kasuwanci.

“Sanin yadda ake amfani da wuka da cokali mai yatsu wurin cin abinci na da tasiri wurin kulla huldar kasuwanci,” in ji James Hebbert, wakilin makarantar koyar da halaye na gari ta Burtaniya, Seatton, a China.

Cike gibi

Daliban makarantun koyar da tarbiyya a China sun hada da jami’an gwamnati, yaran da su ke karatu a makarantun kasashen ketare, matan auren da ke saukar manyan baki, da kuma mutanen da ke tafiye-tafiye a kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto Seatton
Image caption Masu daukar darasin na koyon yadda ake shan shayi da yamma a al'adar turawa

“A na matukar bukatar wadannan darussa a kowanne mataki na al’ummar China,” in ji Hebbert, wanda dalibansa na farko direbobin motocin Rolls Royce ne da su ke son shigarsu ta dace da motocin, daga baya kuma sai masu kudi su ka fara zuwa domin su koyi dabi’o’in mutanen Burtaniya.

“A cikin shekaru kalilan, na ga sauyi a irin daliban da su ke zuwa nan. ‘Yan China da dama na fita kasashen waje. Sun fahimci amfanin sanin dabi’un abokan huldarsu.”

Idan koyon yadda ake feraye lemo da wuka ba wani muhimmin abu ba ne a Turai, a China sababbin masu kudi a shirye su ke da su biya duk abinda ya kama don su koyi dabi’un da su ka dace da sabon matsayinsu a rayuwa.

“Idan na sake komawa Milan mu ka je cin abinci, zan iya gaya wa mijina ya daina rike wukarsa kamar ya rike takobi,” in ji wata dalibar darasin tsarin cin abinci na kasashen Yamma wanda James Hebbert ke gudanarwa a Shanghai.

Hebbert na cajin yuan 20,000 (3,243) a darasi guda ga rukunin dalibai 10 domin daukar darasi da yamma.

Darasin da aka fi rububinsan a cibiyar Sarita ‘saukar baki,’ akan biya yuan 100,000 ($16,216) a tsawon kwanaki 12, inda dalibai kan koyi darussan da su ka danganci yadda ake hira da kuma giyar da ta dace da kowanne nau’in abinci.

Rashin tarbiyya

Kafafen yada labari da ma shugaban kasar China sun sha sukan irin dabi’un da wasu ‘yan China ke yi a kasashen waje. A wata ziyara da ya kai kasar Maldives, shugaban kasar China Xi Jinping ya shawarci ‘yan kasar da “su nuna wayewa a lokacin da su ka tafiye-tafiye a kasashen waje.”

Fiye da ‘yan China miliyan 100 ne su ka fita kasashen ketare a 2014, kuma rashin tarbiyyarsu ya yi shuhra a kafafen yada labarai. Daga cikinsu akwai: bata fuskar wani gunki a Masar, zuba wa ma’aikaciyar jirgi ruwan zafi da kuma yin fitsari a waje.

Hakkin mallakar hoto Darcy Holdorf
Image caption 'Yan takarar sarauniyar kyau suna karabar horo

A watan Oktoban da ya gabata, hukumar yawon bude ido ta China ta gargardi matafiya da su nuna kyakkyawar tarbiyya a waje. A cikin wani littafi mai shafi 64, hukumar ta gargadi ‘yan China masu fita waje da su guji yin fitsari a kwamin wanka, satar lemar dira daga jirgi, ko tsugunawa kan masan tangaran da kafafunsu.

Daga cikin hukunce-hukuncen da aka tanadawa ma su irin wadannan dabi’u har da cin tarar kamfanonin da su ka shirya tafiyar da kuma haramtawa mara sa tarbiyya sake fita daga kasar.

“Mutanen China ba su da tarbiyya. Iyayensu ba sa koya mu su kyautata mu’amala. Na kan yi mamaki duk san da maza su ka bude min kofa a birnin Paris. Wannan ba zai taba yiwuwa a China ba,” in ji Yue-Sai Kan, wata ba’amurkiya ‘yar asalin China mai shiryawa da gabatar da shirye-shiryen talabijin, kuma marubuciyar littafin koyar da tarbiyya, wanda aka sayar da fiye da kwafe miliyan uku kawo yanzu.

Kan ta na gabatar da lacca akan kyawawan dabi’u kuma ita ke horar da ‘yan matan China da ke shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya.

Yayinda wasu dabi’un da Turawa kan dauka rashin mutunci ne sun samo tushe ne daga bambancin al’ada, wasu kuma na da alaka ne da zamanin juyin-juya-halin al’adu na zamanin mulkin gurguzu, inda ake daukar duk wata dabi’a da ke nuna alamun wayewa a matsayin ta ‘yan jari-hujja don haka ake yin hukunci mai tsanani.

“Idan ka na gwagwarmayar neman abinda za ka sa a baki, ba ka cika tunanin kyautatawa wasu ba,” a cewar Ho.

Wasu abubuwa da ke kama da rashin tarbiyya a idon baki – irin su turareniya, datsen layi, magana da karfi ko kwakule hanci a bainar jama’a – halayyar yau da kullum ce ga mafi yawan ‘yan China.

Sai dai a yayin da China ke kara hulda da sauran kasashen duniya, a hankali ‘yan kasar sun fara fahimtar irin kallon da ake musu a kasashen ketare.

Sabon salo

Domin nisanta kansu daga wannan kaurin sunan, da yawa daga cikin sababbin masu kudin na kokarin kyautata dabi’unsa a makarantun tarbiyya. Haka kuma su na kallon kyawawan dabi’u a matsayin alamar wayewa.

Hakkin mallakar hoto Seatton
Image caption Ana fara bada horon shan shayin yamma ne da shirya furanni

“Mutanen China sun fahimci cewa matsayinsu na kasar da tafi kowacce karfi a duniya ya sa su a wani hali da zasu bukaci sanin al’adu da dabi’un da za su kyautata alakarsu ta siyasa da kasuwanci,” in ji Viviane Neri, shugabar makarantar Institut Villa Pierrefeu.

“A da, mallakar mota shi ne abin birgewa,” in ji Hebbert. “Yanzu masu kudi na neman wani abun dabam da za su bambance kansu da talakawa.”

Idan kana so ka karata wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Wester Manners the latest Chinese status symbol