Me ya sa muke almundahana?

Hakkin mallakar hoto Dipankar

Cuta a wurin aiki da fagen wasanni ba kyau, amma wasu lokutan mu kan yi. Ga dalili.

Tun kafin a fara gasar wasannin Olympics ta bana, wata badakala ta mamaye kafafen labaran duniya ita ce– an haramtawa ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Rasha baki daya in ban da mutum guda daya tak shiga gasar, saboda zargin gwamnatin kasar ta ba su kwayoyin kara kuzari.

Bayan da aka fara gasar, mun ji ‘yan wasa na zargin abokin karawarsa da amfani da haramtattun kwayoyi, kamar ‘yar tseren nunkayar Amurka Lilly King da ta zargi takwararta ta Rasha, Yulia Efimova, ko dan tseren ninkayar Australia Mack Horton wanda ya nuna yatsa ga abokin takararsa dan China, Sun Yang.

Hakkin mallakar hoto Getty

Sai dai kuma samun nasara ta hanyar bin hanyoyin da basu dace ba, ba a fagen wasa kawai ta tsaya ba. Akwai lokuta da dama a wurin aikinmu da kuma rayuwarmu ta yau da kullum da mu kan ji bukatar taimakawa kanmu ta barauniyar hanya.

Sai dai masana sun ce ba kwadayi ne kawai ke samu yin hakan ba. To wane dalili ne ke sa wasu mutan su yi cuta? Tsabar kwadayi ne da rashin tarbiyya? Shin kasayyar da muke a zamantakewar zamani ta na taimakawa a yi cuta?

Almundahana a kimiyyance

Masu nazarin halayyar mutane sun gano cewa samun nasara kan kara wa mutane kaimin cuwa-cuwa, yayin aiki a matsayin wani bangare na rukunin jama’a na kara sa a yi almundahana.

Amos Schurr, mai nazarin dabi’ar mutane a jami’ar Ben Gurion da ke Isra’ila, na gudanar da bincike kan yadda cudanya da mutane kan sa mu dauki cuta a matsayin wani abu mara muhimmanci da kuma yadda nasara a gasa ke kara wa mutane kaimin yin cuta.

Binciken ya kunshi gwaje-gwaje da dama ta hanyar wasannin tambayoyin ‘yar kure da kuma na kada dan dayis, inda manazartan su ka binciki yadda ‘yan wasan su 23 ke bayyana nasarar da su ka samu.

‘Yan wasan dai na da damar samun kyautar kudi bisa la’akari da lambar da ta fito a dayis din da su ka kada. Schurr da tawagarsa sun gano cewa wadanda su ka yi nasara a wasannin farko sun fi shirga karya, domin samun kudi fiye da hakkinsu.

Tawagar Schurr dai na binciken yadda kasayya ke iya jawo almundahana, da kuma yadda cudanya da mutane ke sa wadansu su yi cuta. “Dabi’o’inmu sun danganta da irin abokan huldarmu – duk lokacin da mu ke aiki cikin jama’a, mu kan bayyana dabi’ar da ta ke karbabbiya a wurin wannan gungun mutanen ne,” in ji Schurr.

Hada-baki kan cuta

Mutane kan yi almundahana, idan abokan huldarsu su ka zuga su, kamar yadda wani bincike daga jami’ar Nottingham da ke UK, ya bayyana, bayan gano cewa hadin baki na iya bada muhimmiyar damar cuwa-cuwa.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Amos Schurr ya gano cewa yin nasara a gasa na sa mutane almundahana

Masu binciken, sun bukaci wasu mutane bibiyu su hada kai a gasar kada dayis da nufin cin kudi. Dan wasa na farko zai kada dayis din sai ya gayawa na biyu lambar da ke jiki. Idan na biyun shi ma ya kada kuma ya samu irin lambar sak, sai a basu kudi su biyun.

A mafi yawan lokuta duk mutane biyun da aka hada a gasar, kan hada baki su yi karya don su samu kudin – adadin lokutan da su ka ce sun kada lambobi iri daya a jere ya ninka adadin da hasashe ke nuna zai iya yi wa har sau biyar.

Masu binciken sun gano cewa cuwa-cuwa ta biyu cikin rukunin mutanen da ke raba-daidan abinda su ka samu, da kuma rukunin da su ke da fahimtar juna.

Wadanda su ka rubuta sakamakon binciken, Ori Weisel da Shaul Shalvi sun kammala bayaninsu da cewa almundaha da rashin gaskiyar da suka haddasa badakala a kasuwannin hadahadar kudi na duniya “ba lallai kwadayi ne kadai ya haddasa su ba, a’a har da hadin baki da kuma yiwuwar raba-daidai a cuwa-cuwar da aka samo.” Yadda dabarun cuta ke sauyawa.

Hanyoyin da mutane ke bi wurin kitsa cuta na sauyawa, kuma wannan muhimmiyar barzana ce ga harkokin kudi, gudanar da kamfanunnuka da kuma sha’anin siyasa, a cewar masu fashin baki game da damfara. Fasahar kere-keren zamani ta bullo da hanyoyi da dama da ma’aikata da ma dalibai za su iya cuta.

Phillip Dawson, mukaddashan daraktan cibiyar bincike kan jarrabawa da koyon karatu ta hanyar na’urorin zamani a jami’ar Deakin da ke Victoria, Australia ya ce: “Wadansu sababbin hanyoyin magudin jarrabawa sun hada da sato bayanan tambayoyin jarrabawa da aka adana a kwamfuta da kuma bad-da-sawun kwaso bayanai kai tsaye ta intanet, ta hanyar amfani da shafin fassarar Google, inda ake fassara bayanin da aka kwafa da Ingilishi zuwa Spananci sannan sai a sake fassara sakamakon zuwa Ingilishi.”

Haka kuma ana samun irin wannan fasahar a kamfanonin bada shawarwari, da kafafen yada labarai da kuma jami’o’i.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Fasaha ta na badar daamar yin cuta cikin sauki, to amma fasahar na kuma bada damar gano su

Sai dai kuma Dawson ya ce akwai karin sababbin hanyoyin kama masu satar bayanan wasu kamar shafin Turnitin, wanda ke binciko duk wurin da aka dauko wani bayani kai tsaye daga intanet. Dawson ya ce: “Ba na jin almundahana ta dadu ko ta ragu a cikin ‘yan shekarun nan. Kawai dai salonta ya sauya.”

A ganin Dawson, tsadar rayuwa ta tilasta wa mutane neman karin hanyoyin samun kudi saboda albashinsu ba zai wadace su ba. Hakan na iya sa wasu mutanen su fara neman hanyoyin samun kudi na cuwa-cuwa.

Haka kuma, matsantawar da ake wa dalibai sai sun ci jarrabawa na sa satar amsa ta zama zabin wadanda ke da karancin lokacin karatu.

Yadda za a gyara

Albishir ga wadanda su ke jin ba dadi idan sun yi cuta kuma su ke fatan sauya dabi’o’insu ta yadda za su zamo masu gaskiya a wuraren ayyukansu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan nunkaya na Australia Mack Horton ya ambaci abokin karaware sa Sun Yang dan damfara

Daina mu’amala da macuta zai iya rage mana sha’awar yin cutar, kamar yadda sakamakon wani bincike da aka gudanar a makarantar nazarin kasuwanci ta jami’ar Harvard ya bayyana. Binciken ya gano cewa zama da macuta na sa wa mutum amincewa da cutar.

Yadda aka gudanar da binciken kuwa, wasu abokai a ka yi wa jarrabawa, amma ba da saninsu ba an sa daya daga cikinsu ya saci amsa a gabansu, ko da su ka ga abokinsu na satar amsa sai su ma su ka fara kokarin yi. Amma da wani bako ya fara satar amsa, sai su kuma abokan su ka hade kai su ka rubuta jarrabawarsu cikin ka’ida.

“Mutane kan karbi dabi’a ne ko kuma su guje ta bisa mahangar abokanan huldarsu,” in ji Schurr.

Don haka, in muna son mu zamo masu gaskiya, sai mu nesanta kanmu da abokai marasa gaskiya, mu kuma kusanta kanmu da abokan kasayya marasa gaskiya.

Idan kana so ka karanta wawnnan labari a harshen Ingilishi latsa nan. We all know cheating is bad. So why do we do it?