Yadda za ka daina yaudarar kanka

Hakkin mallakar hoto Getty

Bazawara Eleanor Bain ta yi zaton ta hadu da namijin da ya dace da ita a rayuwa. Ta koma wani sabon birni, ta na neman sabon aiki domin fara sabuwar rayuwa da ‘ya’yanta mata biyu, lokacin da ta tsammaci ta yi sabon masoyi.

Sai dai kuma duk da ra’ayinsu ya zo daya akan abubuwa da dama, akwai kuma dimbin matsaloli da su ka dabaibaye sabuwar soyayyar. Wani lokacin idan rikici ya barke tsakaninsu sai su kwashe sa’o’i su na sa-in-sa.

Yanzu da ta ke tuna baya, Bain ta ce ita ta yaudari kanta game da soyayyar. “Ba wai ba na son ganin laifinsa ba ne,” in ji Bain. “Ba na iya gani ne kwata-kwata.” Ba ta yarda akwai matsala ba ko lokacin da kawayenta ke ce mata ba su dace da juna ba. “Na yi iya bakin kokarin nuna musu cewa babu wanda ya cancanci na rayuwa da shi kamarsa.”

Don me mu ke haka? Yaudarar kai wacce hanya ce ta kare kanmu daga gaskiya mai daci. Ita ce dalilin da ya sa mu kan yi ikirarin mu na da gaskiya amma kuma mu ke karya doka; ita ke sa mu gaya wa kanmu muna son wani abu, misali yin ritaya cikin arzikin rufin asiri amma mu rinka abubuwan da za su rusa burin, ita ke sa mu ci gaba da aiki a kamfanin da ake nuna mana wariya wurin karin girma.

Hakkin mallakar hoto Getty

Yaudarar kai na iya saukaka mana takaicin rayuwa, amma ta na tattare da mummunar illa, a cewar Cam Caldwell, farfesan ilimin shugabancin kamfanoni da ma’aikatu a jami’ar Purdue da ke Indiana, Amurka, wanda ke gudanar da bincike kan yaudarar kai tsawon shekaru masu yawa. Ya bayyana yaudarar kai a matsayin “rike akidoji biyu masu karo da juna ba tare da amincewa akwai sabani tsakaninsu ba.”

Daya daga cikin illolin yaudarar kai shi ne ware kai daga cikin al’umma saboda yadda ka damu da kare ra’ayinka ya zarta kokarinka na fahimtar gaskiya, a cewar wani masanin halayyar dan Adam M Scott Peck, a wata makala da Caldwell ya rubuta.

Ga wadanda ke son su guji bonono; rufe kofa da barawo sai su tambayi kansu: Me ya fi illa – sanin matsalar da ke maka barazana a rayuwa ko kuma sakankacewa komai ya na tafiya daidai har sai matsalar ta jawo maka gagarumar asara a soyayya, ko kasuwanci ko wurin aiki? Ko da yake amincewa kanka cewa ka na cikin matsala abu ne mai wuya musamman a lamuran da su ka shafi soyayya, yin biris da matsalar na iya jawo maka cutuwa a kusan kowanne fanni na rayuwarka.

Matakai uku ne

Mafi yawanmu kan yaudari kanmu a wasu lokuta a rayuwarmu. Dubi misali harkar kudi, inda ake tafiyar da komai keke-da-keke amma duk da haka akan samu mutanen da ke riya cewa kamar ba haka lamarin ya ke ba, a cewar Kathleen Gurney, shugabar kamfanin Financial Psychology Corporation, da ke Sarasota a jihar Florida, Amurka.

Ta ce har akantoci kan yaudari kansu game da kudi duk da tarin ilimin da su ke da shi na kididdigarsa. Alal misali, akwai wani akanta da ya yi asarar gidansa saboda gaza biyan bashin bankin akan kari.

“Yaudarar kai ta na da matakai uku,” in ji Gurney. Na farko shi ne rashin amincewa akwai matsala, kamar mutumin da baya biyan bashi akan kari.

Hakkin mallakar hoto Getty

Mataki na biyu shi ne; kankantawa. Ma’ana, mutum zai yarda cewa akwai matsala amma sai ya fara kame-kamen yadda zai nuna cewa ba ta da wani tasiri. “Da gaske ne hakan na faruwa, amma matukar dai ina biyan bashin daga baya, ai ba komai don ina makara.”

Matakin yaudarar kai na uku shi ne gociya. A wannan lokacin mutum zai amince akwai matsala, kuma ta na da illa amma sai ya goce wa daukar alhakinta. “Na sani, amma ai ba laifina ba ne, ayyuka ne su ka yi min yawa shi ya sa ban samu in biya basussuka kan kari.”

To ina mafita? A cewar Gurney neman shawarar abokai ko kwararrun masana ita ce babbar maganin yaudarar kai.

Bugu da kari, ka na iya rubuta abinda ka ke buri a rayuwa sannan ka rubuta me ka ke yi don cimma burin, sai ka kwatanta ka ga in da gaske ka dauki hanya.

Kwarin giwa Yaudarar kai ba a harkar kudi ko soyayya ta tsaya ba kawai. Ta kan addabi mutane da yawa a bakin aikinsu. Anan ma, ana iya ganin yadda buri da karatun wasikar jaki kan maye gurbin nazarin gaskiya da gaskiya.

Wannan shi ne abinda ya faru ga wata ma’aikaciyar banki da ta nemi shawarar Nadine Gimbel, mashawarciya kan harkokin aiki a Frankfurt, Jamus.

Ma’aikaciyar ta yi kukan cewa an ki yi mata karin girma duk da kwazon da ta ke yi a bakin aiki. Matar mai shekaru sama da 40 na jira ne shugabanninta su lura da kokarinta har su yaba mata da karin girma.

“Yaudarar kanta ta ke yi da take zaton cewa wani dabam ne zai gano kokarinta,” in ji Gimbel, wacce ta shawarci matar ta rubuta abinda take bukata sannan ta sanar da shugaban sashin da ta ke aiki. “Hakan ta yi kuma shugaban ya amince da kara mata girma.”

Shawarar Gimbel ga masu fuskantar wariya ko rashin gamsuwa a wurin aiki ita ce, su tantance me su ke bukata su tunkari shugabanninsu ko kuma su bar aikin da bai biya musu bukatunsu.

“Sauyi wani bangare ne na rayuwa, amma mu kan guje shi saboda tsoro,” in je Gimbel. “A gaskiya dai mu kan yi nadamar abinda bamu aikata ba fiye da abinda mu ka yi. Bamu san inda zamu kai ba, in da bamu ji tsoro ba.”

Tabbas! Sanin gaskiya game da kanka dabam, aiki da ita kuma sai da juriya da karfin hali. Ga Bain, ba ta iya samun kwarin gwiwar kawo karshen dangantakarta da sabon masoyinta ba sai da ta ga cin mutuncin nasa har ya kai ga ‘ya’yanta.

“Amma fa da ciwo matuka,” in ji Bain wacce ta ce ji ta yi kamar ta gudu daga garin lokacin da ta gano irin zurfin yaudarar da ta yi wa kanta.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to stop lying to yourself.