Yadda masu daukar aiki ke bibiyarku a Facebook

Image caption Masu daukar aiki na amfani da shafukan sada zumunta kamar su Facebook don daukar ma'aikata

Shafukan sada zumunta irin su Facebook na taimakawa masu daukar ma’aikata neman irin mutanen da su ke so.

Sai dai kuma anya hanyoyin kebance masu ganin talla a shafukan ba za su bai wa kamfanoni damar nuna wariya ba?

Kusan watanni hudu da su ka wuce, Lisa Dorahy ta ga wani tallan neman ma’aikata a shafinta na Facebook.

Ba ma aiki ta ke nema ba, kuma ba ta cika duba shafin Facebook ba, amma aikin mataimakiyar rabin lokaci a kamfanin daukar ma’aikata ya bata sha’awa.

Kamar wasa sai ta danna tallan, cikin kwanaki uku an kira ta ganawa, bayan mako guda kuma aiki ya samu a kamfanin daukar ma’aikata na Human Connections Group da ke kasar New Zealand. Daga baya ne Dorahy ta gano cewa dama an shirya tallan ne domin ya riske ta ko kuma dai mata irinta.

Talla a Facebook ba bakon abu ba ne – tabbas kun saba ganinsu a shafukanku. Sai dai kuma mai yiwuwa kun taba ganin tallan aikin da ba ya cikin abubuwan da ku ka saba yi a baya. Hakan na faruwa ne saboda masu neman ma’aikatan na bukatar mutane masu irin kwarewarku, sakamakon bayananku da ku ka wallafa a shafin Facebook da kuma dabi’o’inku a shafin.

Yayin da masu neman ma’aikata da yawa ke tururuwar tallata gurabe a Facebook, masana na gargadin cewa damar da shafin ke bayarwa na aika sakonnin talla ga wasu kebantattun mutane zai iya bai wa wasu kamfanonin damar nuna wariya bisa ga dalilin shekaru, kabilanci, addini ko jinsi.

Image caption Fiye da mutane biliyan daya ne ke amfani da shafukan sada zumunta a kowace rana.

Lokacin da BBC ta tuntubi Facebook, kamfanin ya ki amincewa ya mai da martani game da tsarin aika tallan neman aiki ga wasu kebantattun mutane.

Ga yadda tsarin ya ke: tallan Facebook wani tsari ne da ke bai wa kamfanoni damar tallata hajarsu a shafukan masu amfani da Facebook.

Lokacin da za su bada tallan, kamfanonin na iya zabin irin mutanen da su ke son su ga tallan, ta hanyar bayyana shekarunsu, jinsinsu, launin fatarsu, addininsu, abubuwan da su ke sha’awa da ma sauran bayanai da dama.

Ba Facebook kadai ne shafin zumuntar da ke bai wa masu talla damar zabin wadanda su ke son su ga tallan na su ba – duk wani shafi da ke tattara bayanan abokan huldarsa ma zai iya hakan. Misali Google+ da Instagram, mallakar Facebook su ma su na bada wannan damar, yayin da LinkedIn ke bai wa masu neman ma’aikata damar zaben wadanda za su ga tallansu bisa la’akari da shekaru ko jinsi amma ban da launin fata ko dabi’ar jima’insu.

Ma’aikata biliyan guda

Mutumin da ya kafa kamfanin Link Humans da ke London, wanda ke tallace-tallace a Intanet, Jorgen Sundberg ya kiyasta cewa kaso 10 na kusan kamfanonin daukar ma’aikata 20,000 da ke Burtaniya na yin talla a shafin Facebook.

Image caption Jorgen Sundberg ya ce akasarin masu daukar aiki na amfani da Facebook

Ya ce: “Facebook yafi kowanne kamfanin fasahar zamani tattara bayanai game da abokan huldarsa.”

Wani mai magana da yawun Facebook ya ce kamfanin ba zai iya bayyana adadin kamfanonin daukar ma’aikata da ke talla a shafin ba.

Babu irin ma’aikatan da ba za ka samu a Facebook ba, saboda fiye da mutane biliyan guda ne ke ziyartar shafin a kullum, in ji mutumin da ya kafa kamfanin Social-Hire mai daukar ma’aikata ta hanyar shafukan sada zumunta, Tony Restell. “Yadda masu hada-hadar kudi ke bukatar hulda da abokansu, haka masu aikin karfi su ke da wannan bukata, don haka babu irin wanda babu a Facebook.”

Kasancewar akwai mutane mabambanta a Facebook, ya zamo dole masu tallata guraben aiki su zabi wadanda su ke so su ga tallansu. Idan ba haka ba kuwa, zamu yi ta ganin tallan guraban aikin da babu abinda ya hada mu da su.

Baya ga haka Facebook na cajar masu talla kudi kalilan idan mutanen da aka tallatawa sun nuna sha’awarsu, amma su na cajin kudi da yawa idan mafi yawan wadanda aka tallatawa ba su nuna sha’awarsu ba.

Zabi ka darje

Wacce ta kafa rukunin kamfanonin Human Connections Group, Emily Richards na amfani da Facebook wurin cike daya daga cikin uku na guraben aikin da ta ke da su.

Mai daukar ma’aikatan, da ke New Zealand ta ce ta kan batar da $14 domin tallanta ya isa ga mutane 10,000, abinda ta ce babu tsada idan aka kwatanta da sauran kafafen yada labarai.

Image caption Mai daukar ma'aikata Emily Richards na amfani da Facebook don samun kusan kashi uku na ma'aikatan da take nema

Sai dai kuma ta na sane da cewa ana iya amfani da Facebook wurin nuna wariya lokacin daukar aiki.

Ta ce: “Ina ga mutanen banza za su iya amfani da wannan damar wurin kawo nakasu ga daidaiton jinsi da launin fata da ma duk wani adalci da mu ka kwashe shekaru muna kokarin ganin ya tabbata.”

Muna nema: Saurayi, mai cin nama

Domin gwajin yadda ake zaben masu ganin tallace-tallace a Facebook, BBC ta bayar da tallan gurbin aiki a shafin. Da farko mun zabi samari masu shekaru 18-25, da ke zaune a New York.

Daga nan kuma sai mu ka ce ban da mazan da su ke da ‘ya’ya ko aure ko ma su ke da budurwa. In da mun so ma da zamu iya kebe wani launin fata.

Sai kuma muka ce ban da duk wadanda ba sa cin nama da kuma wadanda ke son alawar cakulati.

Ba da jimawa ba kuwa Facebook ya amince da tallan, inda aka shirya nuna shi ga samari, mara sa ‘ya’ya, maciya nama da ke birnin New York su 430,000.

Davida Perry, shugabar kamfanin aikin lauya na Schwartz & Perry da ke New York, ta ce tallata guraben aiki ga wasu kebantattun mutane a Facebook zai iya sabawa dokoki da yawa.

A Amurka, doka ta haramta nuna bambanci wurin daukar aiki bisa dalilin shekaru, launin fata, addini, jinsi, daukar ciki, nakasa, ko halayyar jima’i.

A Burtaniya, haramun ne a nuna bambancin shekaru, jinsi, daukar ciki, halayyar jima’i, addini, ko aure a wurin daukar aiki. Ana iya kama ka da laifin nuna wariya ma idan aka yi la’akari da wurin da ka tallata gurbin aikin – misali, talla a mujallar maza kadai.

Don haka duk da cewa su tallace-tallacen babu alamun wariya a cikinsu, tsarin da ake bi wurin zaben wadanda za su gansu zai iya keta dokokin haramta wariya.

Duk da haka, “zai yi matukar wuya a kama masu tallan da cikakkiyar hujjar da za a iya hukunta su,” in ji Perry.

Amma ta ce, da masu neman ma’aikatan za su tallata matakan da su ka bi na kebe wadanda za su ga tallace-tallacensu da kuwa za su iya haduwa da fushin kotu.

Image caption Masu nuna wariya a cikin tallan Facebook na iya fuskantar tuhuma.

Ka’idar talla a Facebook dai ta bukaci duk masu bada talla da su kauce wa “nuna bambanci, muzganawa, tsokana, ko wulakanta abokan hulda,” kuma wajibi duk wanda zai ba da talla a shafin ya tabbatar ya cika wannan ka’idar.

Mun so jin ta bakin Facebook game da ware mutanen da zasu ga talla amma ya yi gum.

Alheri ne

Duk da barazanar wariya da ke cikin tallan Facebook, kwararru a kan harkar daukar ma’aikata ta intanet na shawartar mutane da su daina musu mummunan zato.

Sundberg na kamfanin Link Humans ya ce tabbas za’a iya amfani da tallan Facebook domin kitsa sharri amma kuma za’a iya amfani da su domin tabbatar da alheri.

Ya ce: “A kullum ba’a rasa mutanen banza, amma dai mafi yawa na amfani da tsarin ne bisa doka. Idan kai sana’arka nema wa kamfanoni ma’aikata, duk inda ka juya ana tunatar da kai bukatar budawa kowa ya samu, don haka babu dalilin da za ka yi amfani da Facebook don kawo wariya.” Idan kana son ka karanta na turanci sai ka latsa nan: How recruiters are stalking you on Facebook