Hattara da shafukan sada zumunta. Kar ka yi asarar aikinka

Image caption Shin shafukan sada zumunta sun samu fargabar bayyana ra’ayoyinmu?

Alvarez, mashawarciya kan harkokin talla kuma mahaifiyar ‘ya’ya biyu da ke zaune a London, ba ta cika sa hotuna a Facebook ba, don haka ba ta yi tunanin mai zai biyo baya ba, lokacin da ta sa hoton danta mai ta-ta-ta babu wando a shafinta.

Ta ce: “Hoton na da ban dariya. Kuma na saba samun kyakkyawar tarba idan na saka abubuwa a Facebook.”

Kunyata uwa?

Sai dai, bayan da wasu su ka danna maballin ‘so’ da kuma sakonni masu dadi da ta fara samu, sai kuma suka ta biyo baya. Wani ya rubuta “Abin dariya amma dai ki cire. Akwai masu mugun tunani da yawa.” Daga nan sai sakonnin suka su ka yi tuttudowa.

Alvarez ta ce kafin a jima, abokan huldarta sun fara tsayar da ita akan hanya su na ce mata ta goge hoton.

Ta kuma sami sakonnin sirri da dama daga mutanen da ke ba ta shawarar cewa ta cire hoton saboda ‘akwai hatsari’.

Ta ce: “Sai dai aka sa ni jin cewa na tafka wani babban kuskure kuma wannan na nuna cewa ni ba uwa ta gari ba ce.

Mafi yawan sakonnin na cin mutunci ba wai shawara ba.”

Wannan lamari ya sa ta shiga taka-tsan-tsan.

“Zan ci gaba da wallafa abubuwa a shafukan sada zumunta, amma dai na koyi darasi,” in ji Alvarez. Ta ce sa’arta guda labarin kai wa abokanan aikinta ba.

Claire Knowles, wata lauya da ke kamfanin Acuity Legal, ta ce wata abokiyar huldarta ba ta yi dace da irin wannan sa’ar ba.

Sakonta da ta wallafa a shafinta na Facebook ya sa aikinta cikin hatsari. “Ta rubuta cewa manajanta shashasha ne kuma bai san aikinsa ba – wannan kuwa abu ne da ya saba wa dokar tozarta mutane a intanet.” In ji Knowles.

“A hankali labari ya koma ga kamfanin da ta ke aiki har shi kansa manajan ya ji.

Hakan ta sa aka ladabtar da ita bisa tuhumar rashin ladabi. Iyakacin shaidar da ake bukata daga shugabanninta shi ne su nuna cewa rubutun nata ya bata ran manajan kuma ya zubar da kimar kamfanin.” A cewar Knowles.

Abokiyar huldar Knowles, wacce ba za a iya bayyana sunanta ba saboda dalilai na shari’a, ta ce ba ta da niyyar tozarta manajanta, kawai dai ta na huce takaicinta ne.

Ta kuma ce ba ta san akwai wata dokar amfani da kafafen sada zumunta a ofishinsu ba, kuma babu wanda ya ba ta horo a kan haka.

Daga karshe dai, an ba ta takardar gargadi, abinda kawai ya hana a kore ta shi ne dadewarta a bakin aiki da kuma nadamar da ta nuna.

Yi tunani kafin wallafawa

Idan abokan aikinka na cikin abokan huldarka a shafukan sada zumunta, wajibi ne ka kasance cikin taka-tsan-tsan kamar a wurin aiki, in ji James Murray, mukaddashin darakta a kamfanin daukar ma’aikata na Robert Walters.

Bayan sharholiya, da ganganci, na dan gajeren lokaci da muka yi a farkon samuwarsu, shin a yanzu shafukan sada zumunta na sa mu yi wa kanmu takunkumi?

Wani bincike da Pew Research Center ta gudanar ya nuna cewa yanzu bamu cika bayyana ra’ayinmu na gaskiya game da al’amuran yau da kullum ko sauran sha’anin rayuwa ba.

Wannan fargabar na daya daga cikin dalilan da su ka bunkasa amfani da WhatsApp, inda masu amfani da su kan aika da sako ga zababbun abokansu, ko kuma SnapChat, wanda sako ke goge kansa jim kadan bayan aika shi.

Kuma ku sani, daukar hutu daga wurin aiki ba ya rage muku fuskantar hatsari idan ku ka wallafa wani abu da ya jawo suka.

A watan Yuli, jaridar The Telegraph ta Ingila ta bada labarin cewa wata ma’aikaciyar hukumar raya al’adun Burtaniya, ‘British Council’, Angela Gibbins za ta fuskanci ladabtarwa bayan da ta soki Yarima George a shafin sada zumunta.

Jaridar ta kuma bada labarin cewa an kori wani babban kuku a Derby, UK, Alex Lambert bayan da ya wallafa hoto a Instagram, da ya yi ikirarin ya na sa nama a abincin mutanen da ba sa cin nama.

“Yadda ma’aikata ke amfani da shafukan sada zumunta na shafar yadda ake kallon kamfaninsu ko da ba sa cikin wadanda ke kula da shafukan kamfanin a zaurukan sada zumunta,” in ji Chris Lee, shugaban kamfanin ba da horo kan tallata haja a intanet Silvester & Finch da ke London.

Ya ce: “Ma’aikata na iya fitar da bayanan sirri bisa kuskure ko su bayyana ra’ayin da zai bata sunan kamfanin.

A 2015, wani kamfani a UK, Game Retail ya kori daya daga cikin ma’aikatansa saboda rubutan cin mutunci da bai dangancin aiki ba, wanda ya yi a shafin twitter.

Da farin dai ma’aikacin ya yi nasara a kotu inda ya zargi kamfanin da korarsa ba bisa ka’ida ba, amma Game Retail ya yi nasara bayan da ya daukaka kara.

Hanyar daukar aiki

Shin abinda ka wallafa a shafukan sada zumunta na iya hana ka samun aikin da ka ke fata? E. Yanzu haka kamfanoni na amfani da shafukan sada zumunta wurin tantance wadanda za su dauka aiki, koda yake da yawansu ba sa fadar haka.

Wani bincike da kamfanin daukar ma’aikata, Robert Walters ya gudanar, ya gano cewa rabin masu daukar aiki a shirye su ke da su binciki wadanda za su dauka ta hanyar shafukan sada zumunta, yayinda kaso 63 na amfani da shafukan sada zumunta na sana’a irinsu LinkedIn wurin tantance masu neman aiki.

Mutane na iya cusa kansu cikin masifa, matukar za su wallafa abu a shafin sada zumunta ba tare da tunani ba, in ji Steve Nguyen, mashawarci a kan shugabanci da kawo sauyi da ke Dallas, Texas.

Sai dai a lokuta da dama ana wallafa babu tunani saboda rige-rige. “

Saboda kowa ya na so a fara ji daga wurinsa, sai ayi ta wallafa babu nazari a kokarin rubuta labarin ban dariya ko kuma tada hankali,” in ji Nguyen.

To idan mun san hakan na iya jefa mu cikin hadari, me ya sa mu ke ci gaba da yi?

Rashin hangen nesa na iya jawo haka, in ji Nathalie Nahai, mai nazarin halayyar mutane a intanet, wacce ta wallafa littafin ‘Webs of Influence.’

Ana sadarwa a intanet ne ta hanyar kafafen da ke iya boye mu, abinda ke sa mu jin cewa zamu iya yin bayani kan duk abinda mu ka so – bisa sigar da ba zamu iya yi ba a rayuwarmu ta zahiri.

A intanet, wadanda su ka fi zake wa su suka fi jan hankali ba wadanda su ka fi kwarewa ba.

Hakan ya na raba mana hankali, in ji kwararru. Muna kara wallafa bayanan da suka dace da yadda muke son a kalle mu, sannan mu na rage wallafa bayanan da ba su dace da yadda mu ke son a kalle mu ba.

Sai dai, hakikanin gaskiya, shafukan sada zumunta sun bamu damammaki fiye da wadanda suka karbe mana.

“Babu wata hujja cewa shafukan sada zumunta na rage mana ingancin alakarmu, ko sa mu janye jiki, ko kuma su rage mana ikon mu’amala da abokan huldarmu, in ji Pamela Rutledge, daraktar cibiyar bincike kan halayyar masu amfani da kafafen yada labarai, wacce ta ke California.

Sirrin dai shi ne kullum mu rika la’akari da abinda mu ke rubutawa don ganin ko ya dace da burin da muka sa a gaba ko kuma bai dace ba. Idan kana son karanta wannan labarin da harshen Ingilishi latsa nan: Think before you over share. Yes, it can get you fired