Zuciyar babanta ce ta ceci wannan mutumin

Hakkin mallakar hoto Lauren Demby at Lauren Rapea Design

Hotunan wata amarya wacce mutumin da ya gaji zuciyar mahaifinta ya yi mata rakiya a lokacin auranta na coci sun mamaye intanet a wannan makon. Kelly Grovier ta yi nazari akan matsayin zuciya na alamar mutumin da ya rasu.

A watan Yulin 1822, a gabar tekun Tyrrhenia da ke Tuscany, a ka kona gawar shahararren marubucin wakokin Ingilishi Percy Bysshe Shelley bayan da ya mutu a ruwa. Shekarunsa 29 lokacin da ya cika.

Lokacin da daya daga cikin abokan Shelley, marubuci Edward Trelawny, ya lura da cewa zuciyar marubucin wakokin ba ta kama da wuta ba, sai ya sa hannu ya tsamo ta.

Daga bisani sai Trelawney ya bai wa matar mamacin, Mary Shelley (marubuciyar littafin Frankenstein) kyautar zuciyar. Ita kuma ta ajiye ta tsawon rayuwarta.

Hakkin mallakar hoto Wikipedia

Wani hoto mai motsa rai, wanda ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta na intanet a makon nan ya tuna min da wannan labari na zuciyar Shelley, da kuma muhimmancin wannan tsokar a rayuwar mutane.

Hoton dai wata amarya ce da ke tsaye gaban coci lokacin daurin aurenta.

Amaryar na taba kirjin mutumin da ya rakota har gaban cocin - mutumin da ya ke raye sanadiyar tallafin zuciya da ya samu daga baban amaryar, wanda aka yi wa kisan gilla.

Shekarun Jeni Stepien 23 lokacin da wani dan daba mai shekaru 16 ya harbi babanta, Michael, a ka a wani lungu da ke Pittsburg, Pennsylvania, a watan Satumban 2006.

Duk da yake likitoci sun ce ba za su iya ceton ran Michael ba, iyalansa sun san da cewa gabobin jikinsa na iya ceton wasu mabukatan don haka su ka amince da bada tallafinsu.

Sai ga Arthur Thomas - malamin jami'a mai shekaru 63 wanda ke fama da gazawar zuciya a daidai lokacin da bala'i ya afkawa iyalin Stepien. Bayan shekaru 10 da faruwar lamarin, Thomas ya sada zuciyar Michael da diyarsa Jeni a ranar aurenta ta hanyar yi mata rakiya a coci.

Hakkin mallakar hoto Lauren Demby at Lauren Rapea Design

Hotunan Jeni Stepien da su ka yi ta karakaina tsakanin Twitter da Facebook a makon nan, wanda ke nuna yadda ta ji bugun zuciyar mataccen mahaifinta, na kunshe da wani annuri na soyayya da kuma dadin rayuwa.

Hotunan sai su ka yi kama da irin kwarjinin wani mai aikin fasaha na zamani: Gabriel Orozco na Mexico, wanda ya yi wasu hotuna biyu da taken "Hannayena su ne zuciyata". A hoto na farko fasihin ne huntunsa rike da zuciyar da aka kwaba da tabo, inda hoto na biyu kuma ke nuna fasihin na miko zuciyar ga me kallon hoton.

Wannan hoton na Orozco ya yi waiwaye baya zuwa shekaru 200 da suka wuce, lokacin da ka ceto zuciyar Shelley daga wuta sannan kuma ya yi hasashen gaba zuwa ga zuciyar Michael Stepien, wacce ke ci gaba da bugawa bayan mutuwarsa.

Idan kana so ka karanta wanna a harshen Ingilishi latsa nan. This man was saved by her father's heart