Hotunan da ke girgiza duniya

Firgitacciyar fuskar wani yaro dan shekara biyar, Omran Daqneesh, lullube da jini da kura, ta girgiza duniya.

Hotunan yaki kan sosa mana rai amma ba su taba sa wa mu fahimci abinda ke faruwa ba.

Jefi-jefi, a kan sami hoton da kan sa duniya ta tsaya cik. Hoton wata yarinya ‘yar shekara tara, Phan Kim Phúc, ta na gudu tsirara a kan wani titi a Vietnam a Yunin 1972 lokacin da fatar jikinta ke ci da wuta na daya daga cikin irin wadannan hotuna.

Hoton da dan jaridar Afrika ta Kudu, Kevin Carter ya dauka na wani yaro a Sudan da ungulu ke jira ya kara sa mutuwa a Maris 1993 shi ma ya na cikinsu.

Da yammacin Larabar makon jiya, duniya ta sake girgiza sanadiyyar hoton wani yaro dake cikin halin tsaka-mai-wuya a birnin Aleppo na kasar Syria. Yaron da ke zaune ba ya motsi akan wata kujera ruwan goro bau, fuskarsa cike da jini da kura, ya kafa wa filin da ke gabansa ido kamar wata ‘yar tsana da ta sha wuya.

Hakkin mallakar hoto AFP

Hoton mai tada hankali, wanda wakilin Al Jazeera Mahmoud Raslan ya dauka, na wani yaro ne Omran Daqneesh mai shekaru biyar, wanda aka ceto shi daga wani gini da harin jiragen yakin Rasha ya rusa.

Nan take hoton ya zamo wata alama ta mutanen da yakin basasar Syria ya rutsa da su. Yakin da ya hallaka akalla mutane 250,000 tare da raba miliyan 12 da gidajensu a cikin shekaru hudu.

Yayinda ake ci gaba da jimamin gawar Alan Kurdi, dan shekara ukun da ya nutse a kogin Mediterranean a Satumban 2015 lokacin da yake kokarin ketarewa zuwa Turai, mutane da yawa a fadin duniya na kara bayyana damuwarsa kan tasirin da yakin ke yi kan kananan yara.

Hotunan Kurdi da Daqneesh sun fara samun gurbi a cikin zukatanmu inda mu ke ajiye hotunan abubuwan da suka danganci tashin hankali. Ba da ban ba dan ba, da sai in ce wadannan hotunan na yara kanana da yakin nan da yaki ci yaki cinyewa a Syria ke ci gaba da hallakawa, a wata fuskar ya yi kama da hoton nan da Francisco Goya ya zana, wanda ya kira Saturn na cin dansa, inda wani gunki daga gumakan Rumawa ya ji tsoron ‘ya’yansa za su yi masa juyin mulki, don haka ya kama su ya na ci daya bayan daya.

Ko da yake rayuwa ba zane ba ce, ayyukan masu fasaha su na kara samu yin nazari mai zurfi kan rigingimun da ke cikin duniya maimakon su karkatar damu daga kansu.

Misali, zanen da Paula Rego ta kasar Portugal ta yi mai suna ‘Yaki’. Zanen da ta yi bayan da wani dan jarida ya dauk hoton yara na tserewa daga wani harin bom bayan da sojojin kawance su ka mamaye Iraq a 2003 (kusan dai irin abinda ya faru a wannan hoton na yakin Aleppo), ya na kalubalantarmu ne mu bambance tsakanin yaki da gaske.

Hakkin mallakar hoto Tate

A zanen Rego, maimakon mutane sai ta nuna wasu abubuwa kamar zomayen wasa. Abinda ke da wuya ga mai kallon hoton shi ne tantance gawar wani abu mai siffar jariri dake tsakiyar zanen; shin ‘yar tsana ce aka yar garin gudu ko kuma dan mutum ne harin bom din ya ritsa da shi?

Yayin da na zuba wa hoton Omran Daqneesh dan shekaru biyar ido sai na tuna da takaici da tashin hankalin da na shiga lokacin da nake kallon wancan zanen yakin na Rego.

Sai dai kuma duk yadda hoton ya motsa min zuciya, abinda na tabbatar shi ne kallon hoto kurum ba zai taba sa mu fahimci halin da mutanen da yaki ya ritsa da su ke ciki ba.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Images that stop the world in its track.