Ko ka san asalin littafi?

Hakkin mallakar hoto Getty

Cece-kucen da ake yi tsakanin littattafan laturoni da na takarda ba sabon abu ba ne. A lokacin da littattafan farko suka fara bayyana a daular Rumawa ma an tafka irin wannan muhawara.

Yanzu dai littafi na fuskantar sauyi. Littattafan laturoni, sun fi takwarorinsu na takarda saukin dauka, inda ake iya daukar daruruwansu a cikin wayar tafi-da-gidanka ko na’urar karanta littattafan laturoni guda.

Ga kuma dubunnansu nan da ka latsa madanni. Ana iya cewa ma littattafan laturoni sun fi na takarda nisan kwana: idan aka sace maka na’urar karanta littattafan laturoni ko ta fadi ta fashe a bandaki, littattafanka na nan da ka sayi sabuwa kurum sai ka sake sauko da su kanta. Don haka ke nan babu karin gishiri idan aka ce littattafai da kuma yadda ake karantasu na fuskantar juyin juya hali.

Ba kowa ne ke farin ciki da wadannan sauye-sauyen ba. Masoya littattafai, mawallafa da masu sayarwa sun saka ido su na ganin yadda za ta karke tsakanin littattafan takarda da na laturoni.

Lokacin da Tom Tivnan na mujallar The Bookseller ya ruwaito cewa a karo na farko a tarihi, adadin littattafan laturoni da aka sayar a 2015 ya yi kasa da na bara, ya rubuta rahoton ne ta yadda za ka iya fuskantar farin cikinsa da faruwar hakan.

Hakkin mallakar hoto Getty

Abin sha’awa game da wannan takaddama da ake yi game da siffar littattafai ta yi daidai da wacce ta faru a can zamani mai dadewa. Shekaru dubu biyu da su ka wuce, wani sabon samfurin littafi ya bullo, wanda ya jawo cece-kuce tsakanin makaranta littattafan wancan lokacin.

Nade shi da kyau

Daular Rum a karnin farko na bullar addinin Kirista cike ta ke da rubuce-rubuce. Gumaka da kaburbura lullube su ke da rubutu, wasikun da aka rubuta kan alluna na karakaina tsakanin al’umma, yayinda attajirai ke da dakunan karatu cike da littattafai na tarihi, falsafa da fasaha. Sai dai littattafan ba irin wadanda muka sani a yanzu ba ne.

Irin nasu littattafan, da aka yi su da takardar ciyawar papyrus wadda ake samu daga kasar Masar, nade su ake kamar tabarma inda su kan kama daga tsawon kafa 15-52. Sai dai duk da yaduwarsu, su na da matsaloli da dama.

Hakkin mallakar hoto john clark

Na farko dai sai an sa hannaye biyu ake iya karanta nannadadden littafi. Sai dai idan akan tebur za a warware littafin, to nan akan sa gwafa ta kafe shi. Idan za a karanta sai a warwaro dama a nade a hagu. Haka kuma akan yi rubutun ne a tsakiyarsa domin ba da sararin nannade gefen. Duk da haka masu nazarin kayan mutan-da sun samo nadaddun littattafan da kasansu ya lalace saboda gugar kayan masu karatu.

Wannan shi ne babbar matsala ta biyu: ciyawar papyrus ba ta dadewa ba ta lalace ba, musamman idan aka dauketa daga busassashiyar hamadar da ta kan fito zuwa kasashe masu danshi. Sarkin Rum Tacitus kan aika wa da dakarunsa da ke yankin Gaul da Germania, littatafan wani malamin tarihi mai sunansa a kowacce shekara don maye gurbin wadanda su ka lalace.

Haka kuma idan aka matsa wa papyrus da nadewa, sai ciyawar ta fara kakkaryewa, abinda ya jawo ke nan mafi yawan nadaddun littattafai na da rubutu ne a fuska daya kurum. Sai dai idan an dai na bukatar rubutan farko ne, sai mai littafin ya juya baya ya sake wani sabon rubutun.

Ba a san asalinsa ba

A cikin karnin na farko ne, wani samfurin littafi mai sabuwar siga ya bayyana. Babu dai takamaiman bayanin daga wane gari ko a wacce shekara ya bulla. Masu nazarin kayan mutan-da sun samo wasu gutsattsarin takardun ciyawar papyrus masu rubutu gaba da baya, abinda ke nuna an ciro su ne daga littafi mai shafuka.

Rumawa kan ce da irin wannan littafi ‘kundi’ saboda ya yi kama da itatuwan da su ke amfani da su wurin rubutu. Rubutacciyar shaida da aka fara samu ta bullar littafi sabon samfuri, ita ce wacce wani mawakin daular Rum, Martial ya rubuta, inda ya ke tallata littafin wakokinsa: “Masu son daukar ‘yan littattafaina domin yi muku rakiyar bulaguro, ku sayi wadannan da fata ta tattara a cikin kananan shafuka: Ku bar wa manya marubuta nadaddun litttattafanku, ni hannu daya ma ya isa rike nawa.”

Wannan tallan da Martial ya rubuta tsakanin shekarun 84-86 CE, ya nuna cewa an san littattafai masu shafuka a cikin karnin farko na kididdigar Kirista, kuma cewa akalla wasu daga cikinsu ana rubuta su akan fata. An dai fara amfani da jemammiyar fata ne a wani garin Girkawa daruruwan shekaru kafin bayyanar kiristanci.

Hakkin mallakar hoto photography

Littafi mai shafuka ya samu karbuwa a matsayin ci gaba kan nadadden littafi. Ana iya yi masa bango na ice ko na takarda mai kwari domin kare shi. Shafukansu na da saukin karantawa, kuma bayan da aka yi musu lambobi sai suka bada damar da mai karatu zai duba abinda ya ke so a shafin da yake so. Ga shi kuma suna iya daukar nunkin banunkin abinda nadaddun littafai masu girmansu ke iya dauka.

Duk da haka ra’ayi ya rabu kan amfani da sabon samfurin littafin a tsakanin al’ummar daular Rum. Arnan Rum, wadanda su ne su ka fi yawa, da kuma Yahudawan daular sun fi ganewa amfani da nadaddun littattafansu, yayinda mabiya sabon addinin Kirista su ka yi ta samar da littattafai masu shafuka game da abubuwan da suka shafi addini da sauran fannonin ilimi.

Mun dai san wanda ya yi kaye a wannan tseren: zuwa karni na shida, da maguzanci da nadaddun littattafai sun kasa karewa yayinda Kiristanci ya danne lambar Yahudanci.

Hakkin mallakar hoto wikipedia

Ba lallai ba ne littattafan laturoni na karni na 21 su sami jajirtattun magoya baya kamar yadda littafi mai shafuka ya samu shekaru aru-aru da suka wuce ba, amma dai su na ci gaba da samun karbuwa.

Ko za su maye gurbin littafin takarda, ko kuma su ne za su kama hanyar nadadden littafi? Lokaci, da ribar masu sayar da littattafai, su ne alkalai.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The mysterious ancient origins of the book.