Makarantun da su ka fi kyau a duniya

Image caption Gine-gine ne na koyo da koyarwa, amma kuma su na da dan karen kyau!

Nancie Atwell, ba’amurkiyar da ta lashe gasar gwarzuwar malama ta duniya, ta ziyarci London, inda ta isar da sakon cewa yara na fuskantar barazanar “cin jarrabawa maimakon samun ilimi”.

Aji, a cewar Atwell, wacce aka zaba gwarzuwar malama, daga cikin malamai fiye da 5,000 daga kasashe 127, ya kamata ya zama wurin “hikima da farin ciki” maimakon takura da tsoron faduwa.

Kalaman na Atwell za su faranta ran wayayyun masu ilimantarwa tun daga shekaru aru-aru zuwa yau wadanda su ka kara ‘kyau’ bisa “hikima da farin ciki” da Atwell ta bayyana.

Stowe da ke Buckinghamshire, ba ko tantama ta na daya daga cikin makarantun da su ka fi kyau a fadin duniya.

An kafa ta ne a 1923 a harabar daya daga cikin manyan gidajen masu sarauta na Ingila wanda aka yi barazanar rushewa a lokacin.

Bayan da shahararren mai zanen taswirar gidaje Clough William-Ellis, ya jagoranci gwagwarmayar ceton ginin, sai aka mayar da shi makaranta.

John Fergusson Roxburgh, hedimastan Stowe na farko, ya ce makarantar za ta tarbiyyantar da dalibanta “su san kyau a duk inda su ka ganshi a rayuwa.”

Dalibansa a kewaye su ke da kyau a kullum, tun daga lambuna masu ban sha’awa wanda Capability Brown ta tsara zuwa ga gine-ginen alfarma wadanda fitattun masu zana taswirar gine-ginen Ingila a karni na 18 su ka tsara.

Cikinsu har da John Vanbrugh, William Kent, Robert Adam da John Soane.

Tun daga 1989, hukumar kula da gidajen tarihi ta Burtaniya ce ke kula da lambun makarantar.

Makaranta mai iyo

Ba kowacce makaranta ce za ta iya kama kafar Stowe ta Ingila ba.

Amma dai ina iya samun kyau har cikin wuraren da ke fama da talauci.

Wacce makaranta ce za ta fi kayatarwa fiye da makaranta mai iyo da ke Makoko, wani yankin gabar teku da ke Lagos a Nigeria?

Kamfanin tsara gine-gine na kasar Netherlands NLE karkashin jagorancin gwanin zana gidaje dan Nigeria Kunle Adeyemi, shi ne ya gina wannan makarantar katako da ke bisa ruwa a bakin teku.

Makoko unguwar talakawa ce wacce mahukunta su ka sha barazanar rushewa tare da sauya wa mazaunanta matsuguni kasancewar ba bisa doka su ka kafa gidajensu ba.

Sai dai kuma wannan makarantar da ta burge al’ummar duniya ta sa Makoko ta zama abin alfahari ga ‘yan Nigeria da dama.

Kyau, wani abu ne mai muhimmanci ga wadanda su ka kafa makarantun farko, musamman ma wuraren da ake daukar karatun addini da na sanin rayuwar duniya a matsayin abu guda.

Misali, kyawun jami’o’in Oxford da Cambridge da ke Ingila ya zamo abin koyi ga masu ginin makarantu a kasashen duniya dabam-daban.

Dakunan karatu

Akwai daliban da ke zabar kwalejin Magdalen, ta jami’ar Oxford saboda tsabar kyanta kurum – musamman hasumiyarta da William Orchard ya wassafa.

Ba abin mamaki ba ne da dakin karatun Magdalen ke dauke da littatafan ilimin tsara gine-gine masu dadadden tarihi, ciki har da littafin De Architectura na Vitruvius, fassarar harshen Holland wanda aka wallafa a 1649.

Asalin littafin dai an rubuta shi ne tun a karnin farko na daya kafin kafuwar addinin Kirista. A cikin littafin Vitruvius ya yiwa masu tsare gine-gine tunin su yi gina mai kwari, wadata, da kyaun gani.

Wuraren da suka fi kyau a makarantun duniya, dakunan karatu ne.

Dogon Daki na tsohon dakin karatun kwalejin Trinity da ke Dublin, Ireland ya isa abin misali. Dakin mai tsawon mita 65 an kammala shi ne a 1732 bisa tsarin Kanar Thomas Burgh, injiniya, kuma dan majalisar dokoki.

Soraye da tsakar gida

Daga Turai zuwa kasashen larabawa zuwa sassan duniya baki daya, jami’oi kan dauki tsarin soraye da tsakar gida ne.

Hakan ya na bada damar nazari cikin tsanaki, wanda zai bada damar rubutu, da bincike da kuma karatu.

Daya daga cikin jami’o’in da tafi kyau a kasar Amurka ita ce Kwalejin Scripps, wacce Ellen Browning Scripps ta kafa a 1926 a kauyen Claremont da ke nisan kilomita 56 gabas da Los Angeles.

Yayinda Magdalen, Trinity da Scripps kwalejoji ne na musamman da aka kafa su dimbin kudi, haka ma takwarorinsu na zamani irin su jami’ar jihar Moscow (1953) da Cibiyar ilimi ta Rolex da ke Lausanne (2010) wacce kamfanin tsara gine-gine na Japan, Sanaa ya tsara, ana iya samun kyau a kowanne farashi kuma a birane da kauyuka.

Sababbin makarantu

Jim kadan bayan kammala yakin duniya na biyu, majalisar lardin Hertfordshire a Ingila ta kaddamar da aikin gina makarantu.

An yi amfani da karfe mara nauyi wurin samar da ajujuwa masu girma da haske domin tabbatar da jin dadin dalibai da malamansu.

Wannan tsari ne na ci gaba a lokacin da Burtaniya ke cikin matsananciyar karayar arziki.

A yanzu, wasu maginan na kokarin samar da irin wancan tsarin a sababbin makarantun da ake gina wa a biranen Burtaniya. Sabuwar makarantar Hackney da ke Gabashin London ta samu gurbi ne a kusa da gin-ginen masana’atu.

Ba ta da wadatar haraba irin ta makarantun Hertfordshire, ba ta kuma da ginin alfarma irin na Stowe, amma ta samar da karin wuraren shakatawar dalibai da malamai ta hanyar yin watsi da tsarin samar da kwararo tsakanin ajujuwa.

Wata makarantar mai ban sha’awa kuma ita ce Druk White Lotus School da ke Shey can cikin tsaunukan yankin Ladakh na kasar India.

An kwashe shekaru 15 ana ginin makarantar a yankin da ke fama da karancin kudi da tsananin ruwa da guguwa.

Don haka ba kudi ne ke sa makarantu kyau ba sai dai kwarewa da sanin makama tare da akidar cewa, an yi su ne domin koyo da ci gaba.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: The world most beautiful schools