Zuma ce ta fi kowane kwaro kisa a duniya

Dabbobi da dama suna amfani da ƙari wajen sanyawa abokan gaba dafi. To amma wata halitta wadda harbin da take yi ya fi kowanne zafi.

Harbin da kwari ko dabbobi suke yi, a inda suke tsarta dafi, wani makami ne da Allah ya ba wa dabbobi da kwari.

A duk lokacin da wani kwaro ko dabba kamar kunama ta harbi mutum da karinta, to karin ne yake shiga cikin fatar mutum sannan kuma sai dabbar ko kwaron ya tsarta dafin a cikin jini.

Kwayoyin dafin kuma za su bi jiyoyin jini ne domin yawatawa a jikin dan adam.

Abin tambaya a nan shi ne wane kwaro ne ko dabba ya fi kowanne harbi mai dafi kuma wanne ne daga ciki ya kamata mutum ya gujewa?

Wannan tambaya ce mai dan rikitarwa. Kamata ya yi tambayar ta ce wane kwaro ne ko dabba wanda dafinsa yake kisa?

Za mu fara ne da batun zafin harbin da dabbobin suke yi. Kuma ta yadda mutum zai fahimci haka, ita ce idan wani abu ya harbe ka.

Justin Schmidt, wani masanin ilimin kwari, ya bari wasu kwari sun harbe shi da sunan yin gwajin.

Ya kuma yi bayani kan yadda zafin harbin yake bisa la'akari da cizon da kwarin suka yi masa.

Tabbas, mutanen yankunan Amurka ta tsakiya da ta Kudanci, za su amince da Schmidt cewa mafi yawancin raɗaɗin harbi dai-dai yake da tururuwar da ake kira 'Bullet ant'.

An ce ko sunanta aka ambata, mutane suna jin kamar an harbe su.

Sai dai kuma kwaron da ya fi kowanne guba shi ne tautau. To amma Schmidt ya bayyana kwaron da cewa "ba shi da dafi amma cizonsa na da zafi."

Sabanin wannan tunani na Schmidt, kwaron Maricopa mai kama da kwarkwasa ka iya zama kwaron da ya fi kowanne dafi.

hakan na nuna cewa kwari masu harbi ba wai kawai suna harbin mutane ba ne domin su sa a ji zafi, suna hadda rasa rai da ma wata gaba da ke cikin dan adam.

Misali idan aka yi la'akari da Kunama wadanda sun gawurta wajen harbin mutane wanda kuma yana da hadarin gaske.

Kunama ta kasance wani kwaro mai dauke da ƙarin da mutane suka fi jin tsoro.

Sai dai kuma wani masani kan halayyar Kunama, Lorenzo Prendini da ke gidan tarihi na Amurka ya ce daga cikin kimanin kwari guda 2000, ashirin ne kawai daga ciki ake dauka suna barazana ga rayuwar dan adam.

Kunama dai dangin wasu kwari ce da ake kira 'buthidae' wadanda kuma suka samo asali daga Mexico sannan suka yadu a fadin duniya.

"Akwai kwari masu dafi sosai a Afirka ta Arewa da kuma yankin Larabawa," in ji Prendini.

Nazari ya nuna cewa dangin kunamar da ake kira Autralis ya fi kowanne kisan mutane.

Hakkin mallakar hoto Daniel Heuclin NPL

Sai dai kuma bincike ya nuna cewa matasa masu cikakkiyar lafiya ba su cika mutuwa ba saboda cizon kunama ba musamman idan suka samu allurar da ke kashe dafin.

Mafi yawancin wadanda harbin kunama ke kashewa su ne kananan yara da tsofaffi da kuma garma-garma, in ji Prendini.

Prendini ya kara da cewa "an fi samun harbin kunama a kauyuka wadanda suke kusa da dandazon kunami."

Bayanan da suka nuna cewa harbin Kunama ya fi kisa a kauyuka ba su inganta ba.

Hakkin mallakar hoto AFP

Har wa yau, nazarin cewa kifin Jelly mai kama da ciyawa rumfar kare, ya fi kisa saboda gubarsa, shi ma bai inganta ba.

Masana sun gano nau'i 25 na kifin na Jelly da ke iya cizo. Kuma mafi kankantarsu shi ne wanda yake da jela mai girman sentimita daya.

To amma suna da fuka-fuki fal a jikinsu wanda kowanne ya ninka girman jikinsu sau dari. Dafin da fuka-fukan nasu ke fitarwa suna yin illa sosai.

Wani abun sha'awa shi ne mutane ba sa mutuwa a wannan zamanin sakamakon cizon kifin na Jelly saboda bunkasar fannin likitanci da kuma wadatar magunguna.

Idan dai ana son gano kwari da ke yin kisa to sai dai a yi duba zuwa ga doron kasa.

Zuma suna da alamin guba a tattare da su. A Japan, mutane 30 zuwa 50 ne suka mutu saboda harbin zuma.

A garin Ankang da ke China a 2013, mutane 41 ne suka mutu a tsawon watanni uku.

Sai dai kuma sai zumar ta harbe mutum kamar sau 500 shi ne za a iya samun dafin d zai yi kisa, in ji Schmidt

Akwai dalilai masu dama da ka iya sa zuma ta zama wadda ta fi kowanne kwaro kisan dan adam.

Hakkin mallakar hoto CLAIRE SPOTTISWOODE

Na farko dai shi ne bukatar zumar da ake yi a ko ina a fadin duniya ya sanya mutum yake farautar ta ido biyu kuma suke yawan yin arangama.

Dalili na biyu kuma shi ne akwai zumar da take da zafin rai.

Akwai dai banbanci tsakanin zumar gida da ta daji. Yayin da ta gida take da sauki kai, ta dajin tana da saurin zuciya kuma suna kai wa abokan gaba hari.

A karni na 20 ne aka kai zuma zuwa yankin Kudancin Amurka kuma sun fantsama zuwa Arewaci, a inda suka zama masu kisan jama'a.

Irin wadannan nau'in na zuma mai kisa tana kashe mutane tun shekaru aru-aru.

Sai dai kuma suna kisan ne kawai idan suka ga za a matsanta mu su. Idan ba ka taba su ba to babu ruwansu da kai.

To duk da cewa nazari ya nuna harbin zuma guda daya ba ya kisa, to harbin ka iya haddasa musamman idan mutum yana da wasu kwayoyin halittar da ba za su jurewa dafin harbin ba.

Idan mutum yana da cuta kamar ta tasa ko Asthma a turance, harbin zumar ka iya janyo ajali. Idan kana son karanta labarin a harshen Turanci sai ka latsa wannan The worst sting you can ever feel