Ka san birnin da cutar HIV ta fara bayyana?

Lokacin da ƙwayar cutar HIV da kuma ciwon AIDS suka fara bayyana, ba a san daga inda suka futo ba. To amma masana sun bayyana mana inda cutar ta fara ɓulla da kuma lokacin da ta fara shiga cikin mutane.

Abu ne mai sauki a ga yadda cutar Sida ta zama mai abin mamaki kuma mai tsoratarwa lokacin da jami'an lafiya a Amurka suka gano ta sama da shekaru 35 da suka gabata.

Cutar ta raba matasa masu lafiya da garkuwar jikin su, ta bar su raunana, waɗanda kowace cuta za ta iya afkawa.

A lokacin dai ba a san daga inda cutar ta zo ba.

To amma a yau mun san dalili da kuma yadda kwayar cutar ta HIV ke haifar da cutar Sida (AIDS) ta zama wata babbar annoba a duniya.

Ba abin mamaki ba ne yadda karuwai suka ringa taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa ta, kamar yadda suma 'yan kasuwa, da kawo karshen mulkin mallaka da sauye-sauye da aka samu a ƙarni na ashirin suka bada gudunmuwa wajen bazuwar cutar.

Ba wai daga sama cutar ta fado ba, wataƙila ta fara ne a mastayin wata ƙwayar cuta da ke shafar birarrika a Afrika ta yamma.

Daga nan ne kuma ta tsallak zuwa bil-adam ta hanyoyi daban-daban, mai yiwuwa sabo da mutane na cin naman birrai. To sai dai fa kwayar cutar HIV da ake samu daga birrai ba ta zama babbar matsala ba a duniya.

Muna da alaƙa ta kusa da goggon biri fiye da sauran nau'ikan birarrika. Sai dai lokacin da 'yan adam suka fara daukar wannan cuta daga birrai ba ta zama wata barazana ga lafiya ba.

Ana kiran ƙwayar cutar HIV da ake samu daga birrai da sunan HIV-1 rukunin O. Ita kuma wacce ake samu daga goggon biri ana kiran ta HIV-1 rukunin M. Sama da kaso 90 na kwayar cutar da ɗan adam ke ɗauka 'yar rukunin M ce.

To shin me ya sa wannan rukunin cutar ya zama daban?

Wani bincike da aka wallafa a 2014 ya bada wata amsa mai ban mamaki.

Hakkin mallakar hoto SPL

Babu wani abu na musamman dangane da wannan rukuni kamar yadda za a yi zato. "Da alama ƙwayar cutar 'yar rukunin M ta yadu ne sabo da dalilai na muhalli" A cewar Nuno Faria wani mai bincike a jami'ar Oxford dake Birtaniya.

Faria da abokan aikin sa sun yi nazari ne a kan kimanin mutane 800 da suka kamu da cutar a tsakiyar Africa.

Ƙwayoyin halittar cutar na samun wani tasiri ne da yake sa su sauya salo cikin sauri. Dan haka idan aka hada kwayoyin cutar biyu aka kuma tantance banbance-banbancen su za a iya gano inda suka samo asali daya.

Kuma ta wannan hanya ce ake gano cewa dan adam yana da dangantaka da goggon biri akalla shekaru miliyan 7 da suka gabata.

Faria ya ce "Ƙwayoyin cutar HIV sun fi ƙwayoyin halittar ɗan adam (DNA) saurin nunkuwa fiye da sau miliyan ɗaya".

Masanin dai shi da takwarorin sa sun gano cewa, rukunin ƙwayoyin halittar cutar na HIV suna da tushe ɗaya ne a shekarun da basu wuce ɗari ba.

Mai yuwawa rukunin M na kwayar cutar HIV ya fara ne a shekarun 1920. Kuma da yake masanan sun bi diddigin duka nau'ikan ƙwayoyin cutar HIV sun gano cewa ƙwayar cutar ta fara yaɗuwa ne a Kinshasa, babban birini Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Hakkin mallakar hoto Zute LightfootAlamy Stock Photo
Image caption A birnin KInshasa ne kwayar cutar HIV ta fara fantsama a cikin mutane

Daga nan ne kuma masu binciken suka sauya salo, suka fara laluben bayanan tarihi domin gano me ya sa cutar da ta fara yaɗuwa a wani birin a Afirka cikin shekarun 1920 ta rikiɗe zuwa wata babbar annoba?

Wasu abubuwa da suka faru daki-daki na iya zama daliln hakan.

Abubuwa da dama na iya zama dalilin saurin yaduwar cutar a shekarun 1960.

A shekarun 1920 dai Jamhuriyar ta Dimokradiyyar Congo ta na karkashin mulkin mallakar Belgium ne, kuma birnin Kinshasa wanda a lokacin ake ambaton sa Leopoldville ya zama babban birnin kasar.

Brinin dai ya ringa jan hankulan matsa da ke neman aiki, sannan su ma karuwai sun yi ta tururuwa. Da haka ne cutar ta HIV ta ringa yaɗuwa cikin sauri.

Amma ba wai a birnin kawai ta tsaya ba. Masu binciken sun gano cewa birnin na Kinshasa na daga biranen Africa da ya fi hada-hada a shekarun 1920, sabo da jirgin kasa da yake zuwa birnin, wanda dubban mutane ke amfani da shi a duk shekara.

Hakan ya sa a cikin shekaru 20 cutar ta Sida (AIDS) ta yaɗu daga birnin zuwa kilo mita 1500.

Hakkin mallakar hoto SPL

Shekarun 1960 sun kawo wani sabon sauyi na yaɗuwar cutar. Jamhuriyar ta Dimokradiyar Congo ta samu 'yanci daga Belgium a 1960, kuma ta zama wajen da masu magana da harshen faransanci daga wasu sassa na duniya ke son zuwa, musamma ma dai 'yan kasar Haiti.

Yayin da matasan kasar suka koma gida bayan wasu shekaru sun tafi da tsarabar kwayar cutar ta HIV zuwa yammacin kogin Atlantika.

Ta shiga Amurka a shekaru 1970, a daidai lokacin da ake ƙara samun 'yancin yin jima'i, kuma ake kara samun taruwar masu neman maza a birane kamar su New York da San Francisco.

Ƙwayar cutar ta HIV ta samu damar yaɗuwa a Amurka da nahiyar turai sabo da yanayin zamantakewa.

Alal misali a jihar Indiana ta Amurka an samu ɓarkaewar yaduwar cutar a shekarar 2015, ta hanyar yin allurar miyagun ƙwayoyi.

Wani bincike da Grand da Markc Liptsitch suka wallafa a shekarar 2014 kan yaɗuwar ciwon sanyi da ba ya jin magani a fadin Amurka sun gano cewa, banbancin halayya a birane daban-daban da kuma banbance banbancen yanayin halayyar jima'i, ya nuna cewa cutar ta yaɗu ne daga yammaci zuwa gabshin kasar.

Sun kuma tabbatar da cewa ciwon sanyin dake bijirewa magani ya taimaka wajen yaduwar kwayar cutar HIV tsakanin maza da ke yin luwaɗi.

Idan kana son ka karanta wannan bincike a harshen Ingilishi latsa nan. We know the city where HIV first Emerged