Ka san dalilin rashin gashi a jikin dan adam?

Idan ka kwatanta mutum da biri ko ma duk sauran dabbobi, za ka ga jikin ɗan adam duk sanƙo ne, kuma hakan shi ne ke bawa ɗan adam damar ci gaba da rayuwa ba tare da mastala ba.

Ka yi duban tsanaki ga abokin ka, ko dangin ka, kai ko ma ga mutumin da ba ka san shi ba. shin ka ga wani abu sabo a tare da shi?

Ka manta da dogon hanci, ko kuma yadda girar sa ta lanƙwasa, duba gashin sa, shin ya na da gashi ko kuwa bashi da shi?

Hakan ba wani sabon abu ba ne a wajen mu, sabo da ba mu saba da ganin gashi a jikin bil adama ba. to amma idan mu ka kwatanta kan mu da sauran dabbobi, da ma birrai masu yanayin bil adama, za mu ga cewa mu kadai ne bare a cikin dabbobin ta fuskar gashi a jiki, mu namu ɗan kaɗan ne.

Ba kamar sauran dabbobi ba, mu fatar mu a waje take, haka mu ke rayuwa.

Duk da dai cewa gashi na da amfani, domin yana kare fata, a wasu lokutan ma yana sa a yi ɓadda kama

Hakkin mallakar hoto RM Alamy
Image caption Gashi kadan ne a jikin mu lokacin da aka haife mu

Charles Darwin shi ne mutum na farko da ya raya cewa asalin mutum daga biri ya ke, ya kuma yi mamaki cewa ɗan adam sanko ne da shi a jikin sa.

Babu wanda ya yi tunanin cewa rashin gashi a jikin ɗan adam na da wani amfani a gare shi. A cewar Darwin. Ya ce mun rasa mafi yawan gashin jikin mu ne sabo da bukatar jima'i. Mun fi son mata ko miji mara gashi a jiki.

To amma fa wannan ba shi ne dalili ba shi kadai. Domin kafin a fara son rashin gashi sai an rasa gashin tukunna.

Wani bincike ya nuna cewa kakannin mu na asali tamkar birarrika su ke. A wajen su gashi na da amfani, wajen dumama musu jiki a lokacin da ake sanyi cikin dare.

Hakkin mallakar hoto Martha
Image caption Birrai sun fi mu yawan gashi a jiki

Akwai nau'in halittu masu yawan gaske da suke yawo a bayan kasa 'yan miliyoyin shekaru da suka gabata.

Kimanin shekaru miliyan biyu zuwa uku da suka gabata, kakannin mu sun fara zama a sarari a wurare masu zafi ., hakan dai na nufin cewa sun fi zama a cikin tsananin zafin rana a kullum.

A dai dai wannan lokacin ne kuma su ka fara farauta suna cin nama sosai, sabo da a lokacin akwai dabbobi masu yawan gaske. Wannan futar zuwa sarari na daga dalilan da suka sa jikin mu ba bu gashi.

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Wanan nau'in birin yana tafiya a tsaye sama da shekaru miliyan uku

A shekarun 1990 Peter Wheeler na jami'ar Liverpool a Birtaniya ya yi wasu bayanan na lissafi da suka nuna adadin zafin da muke bukata dan mu yi aiki yadda ya kamata. Bayanan sun nun cewa idan har kwakwalwar halittu ta yi dumi sosai, yadda suke tunani zai ragu.

Idan ya zama halittun suna da gashi da ya lullube su, ba za su yi saurin hucewa cikin sauri ba. Wheeler ya bayyana cewa akwai wasu abubuwa biyu da suka haifar da sauyi kuma suka sa kakannin mu su ka samu abin da zai ringa sanyaya musu jikin su.

Mutanen farko sun ringa rage zafin jikin su ne ta hanyar gumi.

Sanan kasncewar su a tsaye yana sa saman sa jikin su ne kawai ke yin zafi sabo da shi ne rana ke duka kai tsaye.

Hakkin mallakar hoto Anup Shah
Image caption Wannan nau'in birin shi ma yana yin gumi sosai

A hankali dai halittun sun fara tafiye-tafiye masu nisa, wasu lokutan ma gudu su ke yi, dan farautar manyan dabbobi, kuma wannan yana sa jikin su ya kara zafi. Domin dacewa da irin wannan yanayi , suna bukatar hanyar da za su rage gashin jikin su, ta yadda za su ringa yin gumi, kuma hakan zai basu damar su dade suna farauta.

A yau, dan adam ne yafi dukkan halittun dake rayuwa a bayan kasa gumi, wasu kwayoyin halitta na samar da gumin da ya kai lita 12 a kullum ga kowa ne mutum, kamar yadda wani masani a jami'ar jihar Pennsylvania a Amurka ya bayyana.

Bincike ya nuna cewa tafiya a tsaye ba wai shi ne dalilin da ya sa dan adam ba shi da gashi ba a jikin sa, to sai dai yana daga dalilan da suke taimakawa zubewar gashin.

Image caption Yawan gudun da muke yi yana ba mu damar dadewa a duniya

Wani bincike ya nuna cewa nau'in dan Adam mai suna Homo Erectus a turance shi ne farkon mutum da ya zauna a duniya kimanin shekara miliyan daya da dubu dari takwas. Yana tafiya ne a tsaye, sannan bangaren kwakwalwar sa ya fi sauran bangarorin kan sa girma. Kuma Homo Erectus shi ne mutum na farko da ya bar nahiyar Africa, sannan a cewar binciken shi ne kakan mutanen da ke rayuwa a yau.

Jabalonski na da ra'ayin cewa dan adam ya fara rasa gashin jikin sa ne ya na kuma futar da gumi a lokaci daya, ma'ana a lokacin da Homo ya fara rayuwa.

Hakkin mallakar hoto SPL

To sai dai duk bayanan da Wheeler ya yi ba su bayyana yadda dan adam ke samun dumi da daddare ba, a lokacin da gari ya yi sanyi, kuma in dai ba gashi a jikin sa zai samu karancin abin da zai kare shi daga hunturun sanyi.

Dávid-Barrett da takwaran sa Robin Dunbar sun yi kokarin yin bayanin da zai yi dai-dai da abin da ya ke mafi dacewa, sun ce in har mutum yana so ya rayu cikin yanayin sanyin ba tare da gashi ba, yana bukatar kona sinadarin Calorie, kuma hakan na nufin dole da rana ya ringa cin abincin da ya ke da Calorie da rana. Masanan sun ce mutum zai iya yin haka ne kawai idan yana cin dafaffen abinci.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Wasu mutanen sun fi wasu rashin gashi

Wasu masana kamar Richard Wrangham na jami'ar Harvard na da ra'ayin cewa dan adam ya fara girki sama da shekaru miliyan biyu da suka gabata.

Dávid-Barrett ya ce idan dai har mutane suna girki, to dole sai sun yi amfani da wuta, kuma da daddare za su ringa jin dumi da wutar da suke girki da ita.

To sai da fa wani bincike da aka wallafa a 2016 ya nuna cewa girki ya zama gama gari ne kawai shekaru dubu dari biyar da suka gabata.

To amma duk da wadannan sabanin tsakanin masana, an amince cewa gumi shi ne babban dalilin da ya sa jikin mu bashi da gashi kamar na sauran dabbobi. To sai dai fa duk da haka akwai sauran ra'ayoyi.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Ya kamata mu godewa yawan gumin da muke yi idan mu ka ji zafi

Wasu ra'ayoyin sun nuna cewa mutanen farko na shafe mafi yawan lokutansu ne a cikin ruwa, dan haka suna bukatar jiki mara gashi domin samun damar nunkaya kamar yadda mari babban kafi ke yi. To amma dai wasu sun yi watsi da wannan ra'ayi, inda suka ce akwai dabbobin ruwa masu gashi da suke nunkaya.

Wani ra'ayin kuma shi ne cewa muna zubar da gashi ne sabo da mu kubuta daga kwarkwata. To amma wannan ra'ayin ma ya samu suka domin cewa ai mutane farko suna da gashi kuma sun rayu lami-lafiya.

To sai dai sama da sherkaru 20 da suka gabata, msana kimiyya sun zurfafa bincike dan gano ainihin dalilin da ya sa mutane ba su da gashi.

Wani nazari da aka futar a 2004 ya gano cewa akwai kwayar halitta dake sa fata ta yi baki sama da shekaru miliyan daya da dubu dari biyu da suka gabata.

Hakan na nufin cewa, fata za ta yi baki ne kawai idan rana na dukan ta. Wannan dai na nuna cew watakila nau'in fatar mu a farko ya kasance ruwar hoda, bayan nan kuma zafin rana, ya sa ta zama baka.

Wata shedar kuma da ta bayyana ita ce ta yin duba kan kwarin da ke makalewa a jikin mutane, kamar Kwarkwata da Kaska.

Wani bincike da aka wallafa a 2004 ya yi duba kan yadda kwarin suka samo asali daga gashin jikin dan adam.

Akwai irin wadannan kwarin da ke rayuwa a gashin mara ga kuma gashin kai.

Babbar matslar duka wadannan binciken dai ita ce sun kasa gano mana dalilai na gado da suka sa mutum ya zama ba shi da gashi a jikin sa.

Masana sun gaza yin bayanin dalilin da ya sa mutum ya ke da kwayoyin halittar da ke sa shi yin gumi.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Zubar gashi daga jikin mu shi ya bamu damar zama mutane irin yadda muke a yau

To sai dai abin da ya ke a zahiri shi ne karancin gashi a jikinmu ya na da dangantaka da yadda mu ke yin gumi.

Yana Kamberov ta jam'ar Pennsylvania ta gano cewa kwayoyin halittar gumi da na gashi suna da dangantaka da juna. Kuma dukkannin su suna samo asali ne daga tushe daya. Fatar jiki ita ce ta ke yanke hukunci wanne za ta samar, domin kuwa dukkanin su suna futowa ne ta waje daya.

To sai dai babu cikakken bayani kan yadda lamarin ke faruwa. "ba mu san yaushe ne aka samu sauyi ba" a cewar Kamberov. " Ta ce " ba mu sani ba, shin gajin jikin mutum ya fara zubewa ne sannan kwayoyin halittar gumi suka bunkasa, ko kuwa dai a lokaci daya abin ya faru".

To amma ita ma ta goyi bayan ra'ayin Wheeler na cewa, rashin gashi a jikin dan adam yana da alaka da gumin da muke yi. Kuma hakan yana da dangantaka da yadda mutane farko ke yin gudu domin farautar manyan dabbobin daji, dan cin abin da zai bunkasa musu kwakwalwar su.

A yanzu sake duban abokin ka da ke da sanko a jikin sa. Za ka ga banbarakwai cewa mu bil adama ba mu da gashi sosai .

To sai dai hakan fa ba haka kawai ya faru ba. hakan ya faru ne sabo da sauye-sauye na halitta da suka ringa faruwa, wadanda kuma suka kawo mu yadda mu ke.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Our wired lack of hair may be the key to our to our success.