Jarirai na fara koyon darasi tun ba a haife su ba

Hakkin mallakar hoto Alamy

Kama daga kifin da ke gane abincinsa tun kafin a kyankyashe kwansa zuwa ga tsuntsayen da kan haddace kukan iyayensu tun su na cikin kwai, a bayyane take jarirai na koyon ilimi tukafin a haife su.

Lokacin da na ke dauke da cikin dana na fari, an bani shawarwari da dama, irin wadanda akan bai wa mata masu ciki.

“Kar ki ci abinci mai yaji,” kuma “ki guji tafarnuwa, musamman lokacin da ki ke shayarwa.” Sai dai a matsayina na mai tsananin cin yaji, ban dauki shawarar ba. Na ga dai kowanne sashe na duniya da irin abincinsu, don haka nake ganin ai ‘ya’yan da aka haifa a garuruwan da iyayensu ba sa rabo da tafarnuwa, haka su ke shan nono ba tare da wata damuwa ba.

Wannan dai zallan hasashe ne daga bangare na, amma gwajin da na yi – ta hanyar amfani da samfur daya tak wanda bai cika ka’aidar binciken kimiyya ba – ya bani kwarin gwiwa kan hasashen.

Dan jaririn na wa ya nuna cewa ya saba da tafarnuwa tun ya na ciki ta hanyar zukar nono ba tare da wani gwalangwaso ba.

Masana kimiyya ma sun gudanar da binciken da ke nuna cewa jarirai kan koyi fifita dandano tun kafin a haife su. A gaskiya ma, abubuwan da jarirai kan koya a ciki sun wuce dandano kurum.

Ba kuma jariran mutane ne kawai su ke fara darasin rayuwa tun daga ciki ba. Abinda binciken ke nunawa shi ne, jinsin dabbobi da dama, manyansu da kananansu kan koyi darussa da yawa game da duniya kafin su shigota ta hanyar la’akari da dandano, kamshi, muryoyi, har ma da abubuwan da su ke gani kafin a haife su.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Idan haka ne, me ye gaskiyar ana iya koyon son tafarnuwa tun a ciki? Peter Hepper na jami’ar Belfast ya yi kokarin samo amsa. Shi da abokan aikinsa sun gwada jariran da iyayensu ke yawan cin tafarnuwa da wadanda ba sa ci sam a watanni ukun karshe na cikinsu.

Binciken na sa ya kunshi yara 33 ne kawai, amma sakamakon ya nuna cewa yara kan ci gaba da rike dandanon da suka koyi amfani da shi bayan shekaru da dama, kasancewar ‘ya’yan matan da ke yawan cin tafarnuwa sun fi son abinci mai tafarnuwa da aka jarrabasu bayan shekaru 10.

Ta yaya jarirai ke dandana abinci a cikin mahaifa? Akwai hanyoyi da dama.

Hanya ta farko, a cewar Hepper, ita ce dandano ya shiga cikin ruwan mahaifa, don haka lokacin da dan tayi ya faru kurba – tun daga mako na goma – “ya kan ji dandanon da ke cikin ruwan”.

Ba kuma sai ta baki kawai dan da ke ciki ke jin dandano ba, domin dandano kan shiga cikin jinin jariri kai tsaye daga jinin uwarsa. Tafarnuwa ce kuwa tafi dacewa da wannan hanyar domin ta kan jima a cikin jininmu bayan cin abinci, abinda ya sa ke nan wadanda ke kusa da mu ke iya jin warinta a jikinmu har washe garin cinta.

Amma fa ba dandano mai irin karfin tafarnuwa ne kurum kan yi tasiri kan dandanon da dan tayi ke so ba. Har ma da mara sa karfin.

Hakkin mallakar hoto Alamy

A wani gwaji da aka gudanar a Pennsylvania, Amurka, masu bincike sun auna tsakanin abinci mai dandanon karas da mara dandano, wane jarirai suka fi kauna. Wasu daga cikin iyayen jariran dai sun kwashe watannin karshen cikinsu da kuma watannin farkon shayar da jariransu su na shan ruwa da lemon karas, yayinda daya rukunin matan ke shan ruwa zalla.

Masu binciken sun gano cewa ‘ya’yan da iyayensu ke shan lemon karas sun fi son abincin jarirai mai dandanon karas, wadanda iyayensu ba su sha ba, su ma ba su so ba.

Wannan zancen sai ku ji kamar shirme, amma ya na da muhimmanci kwarai. A tsakanin dabbobin da ke shayarwa, dandano da kamshi kan taka muhimmiyar rawa wurin karbar nono ga jarirai.

Wannan dabi’ar kuma tabbas haka take ga zomaye, gafiyoyi, karnuka da maguna.

Ba mamaki hakan na faruwa ne domin taimaka mana gane abinci mara hatsari, sannan kuma ‘ya’ya su gane mahaifiyarsu. “Daidai ne,” in ji Hepper, “a halicce mu na da dabi’ar gane babbar mai bamu kulawa, wacce ita ma aka dabi’antar da ita kan kulawa da mu.”

Hakkin mallakar hoto Alamy

Wannan tsarin na gane uwa ga jaririn da ba a ma haife shi ba, na da matukar muhimmanci musamman a jinsin dabbobin da wasu jinsunan ke yaudara, su dora musu nauyin kula da na su ‘ya’yan, misali tsuntsuwar nan dangin benu da turawa ke kira cuckoo.

Jinsin benun da ake kira wren, su ne cuckoo ke yaudara. Tsuntsuwar cuckoo kan dasa kwanta a shekar wren – amma darasin da tsutsayen kan koya tun su na cikin kwai kan taimakawa tsutsunwar wren ta gano an damfareta.

Diane Colombelli-Négrel ta jami’ar Flinders da ke Adelaide, Australia ce ta gano hakan.

A wani bincike da ta gudanar game da dabbobi masu cinye ‘ya’yan tsuntsuye, ta na nadar sautukan da ke fitowa daga shekar tsuntsayen wren yini da kwana. Lokacin da take sauraron saututtukan da ta nada, sai ta lura cewa matan tsuntayen kan fitar da wani sauti na musamman a lokacin da su ke kwanci.

Wannan sai ya bata mamaki ganin uwar da ke kwanci kuma take kokarin tsare ‘ya’yanta daga masu fyauce su, bai kama ta a ce ta na fitar da sautin da zai iya jan hankalin masu cin ‘ya’yan ba.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Amma da Colombelli-Négrel ta kwatanta kukan da tsuntsuwa mai kwance ke yi, da kukan da kyankyasassun ‘ya’yan ke yi idan su na jin yunwa, sai ta same su iri daya sak.

To ko dai kukan da masu kwancin ke yi, darasi su ke bai wa ‘ya’yansu dake cikin kwai, domin su koyi irin kukan da za su yi bayan kyankyasa idan su na bukatar abinci?

Domin gwada wannan hasashe – tare da tabbatar da cewa kamanceciniyar kukan ‘ya’yan tsuntsuwa na da uwarsu dalilin koyo ne ba wai saboda tsarin kwayoyin halitta ba, sai Colombelli-Négrel da abokan aikinta su ka gwada sauyawa iyaye ‘ya’yan da za su raina.

Su ka yi musayar kwayaye tsakanin shekar tsuntsayen don ganin ko ‘ya’yan za su rinka yin irin kukan uwar da ta dasa kwansu ne ko kuma uwar da ta kyankyashe su. Sakamakon sai ya nuna ‘ya’yan su na yin irin kukan tsuntsuwar da ta kyankyase su ne ba na wacce ta yi kwansu ba, abinda ke nuna cewa sun koyi kukan ne su na cikin kwai, a lokacin da su ke sauraronta yayin da take kwanci.

Hakkin mallakar hoto David Tipling

Abokin aikin Colombelli-Négrel, Mark Hauber da ke Hunter College, New York, ya bayyana cewa binciken na su ya kuma yi nazarin ko tsuntsaye na gane bambancin kukan ‘ya’yansu?

Sakamakon gwajin ya nuna cewa tsuntsaye su na amsa kukan ‘ya’yansu fiye da na ‘ya’yan wasu tsuntsayen da aka saka cikin shekarsu, abinda ke nuna cewa kukan da su ke koya wa ‘ya’yan da ke cikin kwai na tasiri wurin nuna musu wa za su ciyar.

Binciken ya tabbatar musu da cewa jinsin tsuntsayen dangin benu da dama na da wannan dabi’a ta koyon sauti tun su na cikin kwai. Hakan ya sa su hasashen ko wannan dabi’ar ta yadu tsakanin wadansu dangin tsuntsayen kuma?

Ba su su ka fara wannan tunanin ba. A shekarun 1970 Gilbert Gottlieb ya gudanar da binciken da ya nuna cewa ‘ya’yan agwagwi da ‘ya’yan fakara ma na koyon sauti tun su na cikin kwai.

Hakkin mallakar hoto David Welling

Amma fa in ban da wadannan tsirarun manazartan, masana ba su mai da hankali sosai kan yadda ‘ya’ya ke koyon ilimin sauti da kamshi da dandano tun kafin su zo duniya ba.

Halitta guda daya ce tak ta samu wannan tagomashi: mutum.

Shin kwayoyin halitta ne ke sa jariran mutane son wasu sautuka ko kuma koya su ke tun su na cikin mahaifa?

A jami’ar New York, mai nazarin dabi’ar mutane, Athena Vouloumanos na gudanar da bincike kan yadda ‘ya’yan mutum ke fara koyon yare.

Ta ce abu ne mai wuya a gwada fahimtar yare a tsakanin ‘yan tayi. Don haka masana kan gudanar da binciken ne kan jarirai sabbin haihuwa tare da bambanta irin sautukan da suka saba da su kafin haihuwa don gano ko da akwai bambanci tsakaninsu bayan haihuwa.

Vouloumanos ta nazarci martanin jarirai ga muryar mutane da kuma sautukan da ba muryar mutane ba.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Binciken ya nuna cewa jarirai na fifita muryar mutane a kan sautukan da ban a mutum ba, dalilin kwayoyin halittarsu, amma kuma su na fifita harsunan da iyayensu ke magana da su fiye da wasu harsunan, abinda ke nuna koya su ka yi tun su na ciki.

To ya batun kida kuma? Shin ‘yan tayi a ciki kan koyi son kida?

Wani gwaji da aka yi a Finland, wani rukunin mata masu ciki sun saurari kidan “Twinkle Twinkle Little Star” a kullum, cikin watanni ukun karshen cikinsu. Wani rukunin dabam kuma ba su saurari kidan ba.

Da aka gwada kwakwalwar jariran da ka haifa lokacin da aka saka musu kidan, wadanda ke jin kidan a ciki kan nuna sun gane sautin yayin da wadanda ba su saba da shi ba kan yi biris da shi, a cewar Minna Huotilainen ta jami’ar Helsinki.

Tasirin wannan binciken shi ne gano cewa wajibi a kula da saututtukan da bakwaini ke ji a lokacin da ake kula da su a asibiti. A cewar Huotilainen, “idan akwai karar na’urori da dama, yaran za su saba da wannan, har su fifita shi a kan muryoyin mutane, abinda zai iya haifar musu da matsalar kwarewa a magana nan gaba”.

Hakkin mallakar hoto YAY

Sai dai kuma Huotilainen na ganin babu wani amfani a sawa ‘yan tayi kida ta hanyar na’urorin da ake tallatawa a yanzu, irinsu na’urar da ake kafa wa a ciki ko kuma ake zurawa ta bakin mahaifa. Ta ce “Babu wani amfani da su ke da shi sam.”

Dandano, kanshi, da saututtukan da ke tattare da dabbobi kafin a haife su, ba su ne kadai abubuwan da su ke koyo ba.

Ludovic Dickel ya gudanar da bincike kan wata dabbar ruwa da ake kira ‘cuttlefish’ da turanci, don ganin ko za ta iya koyon ilimi ta hanyar ganin kaguwa ba a kyankyashe kwanta ba.

Hakkin mallakar hoto David Fleetham

A wani gwajin, Dickel da abokan aikisa sun nuna wa kwayayen ‘cuttlefish’ hotunan kaguwa ba tare da sinadiran da kaguwa ke fitarwa ba, saboda ba sa son warinta ya yi tasiri a kan kwayayen.

Bayan da su ka kyankyashe, ‘cuttlefish’ din da su ka kalli hoton kaguwa su na matsayin kwai sai su ka fi wadanda ba su ga hotonta ba zafin farautarta da cinyeta.

Tun ana sauran makonni hudu kafin kyankyasa ma, ‘cuttlefish’ kan koyi warin kifayen da za su iya cinyesu, kuma ya guje su bayan kyankyasa.

Hakkin mallakar hoto Visualas Unlimited

Kwadi da kozaye ma kan koyi kanshin dabbobin da ke halaka su tun su na cikin kwai, domin su guje su lokacin da suka zama talibamban har zuwa cikar halittarsu.

A takaice dai, ilimin kimiyya na nuna mana cewa abinda mu ka koya game da duniya kafin shigarta, na iya taimaka mana fiye da yadda mu ka zata a baya.

Idan kana so ka karanta wannan da Ingilishi latsa nan babies start learning before they are even born.