Me ya sa mafi yawan dabbobi ba su da kashin baya?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Koda yake kashin baya na daga cikin muhimman kirkire-kirkire a tarihin halitta, kawo yanzu an kasa tantance asalinsa.

Mafi yawan finafinan da ke kokarin nuna wata duniya ta daban, kan nuna halittu ne masu tsarin halitta bambarakwai. Kama daga halittun duniyar Mars masu kama da kaguwa a fim din War of the Worlds zuwa ga manyan kwarin Starship Troopers, masu shirya finafinan kan nuna cewa halittu mara sa kashin baya na iya zama barazana ga jinsin mutane.

Saboda mu a ganinmu kashin baya shi ne gaba da komai. Duk da dai ba tabbas cewa mu ne halittar da tafi kowacce iko a duniya, amma dai muna da kashin baya, haka kuma sauran manyan dabbobi masu kwarjini, wadanda ke tafiya, ninkaya ko tashi duk su na da kashin baya. Don haka ba mamaki idan mu ka bi abinda Henry Gee, babban edita a mujallar Nature ke kira “fifita dangin halittarmu”.

Tabbas kashin baya, gaba ce mai matukar amfani. Ta na tallafawa jiki, tare da samar da cikakkiyar kariya ga laka. Haka kuma samun kasusuwa a cikin jikinmu maimakon a waje ya bamu damar motsi iri-iri, baya ga cewa dabbobi masu kashin baya na iya girman da babu wata dabba mara kashin baya da za ta taba kai wa.

Hakkin mallakar hoto Graham

Sai kuma ganin cewa fiye da kaso 90% na dabbobin duniya na rayuwa ne ba tare da kashin baya ba, babu wani tartibin bayani na dalilin bullar wannan halitta a karo na farko. Yaya aka yi kashin baya ya bulla a duniyar da a da babu kashin bayan?

Dabbobi masu kashin baya dai sun bayyana a duniya ne kimanin shekaru miliyan 500 da su ka wuce. Kafin wannan zamanin, halittu na gudanar da sassaukar rayuwa ne tsawon daruruwan miliyoyin shekaru; mafi yawansu kwayar halitta daya kurum ke watangaririya cikin teku, in ta yi kamari sai wadannan kwayoyin halittun sun cure wuri guda. Shi ke nan.

Kwatsam! Sai aka wayi gari tekunan duniya na cike da wasu sababbin nau’o’in halitta. Cikin miliyoyin shekaru kadan sai wata bakuwar halitta ta biyo sahun kwari da tsutsotsi. Wato dabbobi masu kama da kifi-kifi, maciji-maciji.

Wadannan dabbobin su ne masu kashin baya na farko. Sai dai kahsin bayan nasu na kaya ne ba na kashi ba. Daga nan ya zama kashi irin wanda ake samu a halittun da su ka kama daga beraye, zuwa kakannin kadangaru, zuwa ga mutane.

Hakkin mallakar hoto Carey

Mun san inda wadannan halittun su ka fara bayyana. An samu kwarangwal din kakannninsu a karkashin teku: wasu dabbobi masu kama da tsutsoti. Su ba su da kashin baya amma su na da kaya.

Wannan ne ya sa mu kan mu kan fara da kayar baya ne kafin ta zama kashi a lokacin da muna ‘yan tayi.

Sai dai kuma su wadancan halittun masu kaya daga ina su ka bullo? A 1909, shekaru hamsin bayan wallafa littafin Asalin Halittu na Charles Darwin, wata kungiyar masana a London ta hada taron tattaunawa da nufin gano asalin dabbobi masu kashin baya.

Ba su sami nasara ba: “Masanan sun amince da abu daya ne kawai,” in ji masanin dabbobi Thomas Stebbing: “wato, abokan jidalinsu sun tafka kuskure.”

A tsawon shekarun da su ka gabata an danganta asalin dabbobi masu kashin baya da kusan kowanne dangi na dabbobi mara sa kashin baya, sai dai har yanzu an kasa samun gamsasshiyar hujja.

Wannan kuwa ya faru ne saboda sabanin dabbobi masu kashin baya, wadanda ke da kwarangwal da hakoran da ke wanzuwa shekaru aru-aru, wadannan halittun su kan zagwanye ne gaba daya su zama kasa. Babu abinda ya rage a yanzu sai shatar jikinsu a duwatsun karkashin teku.

Hakkin mallakar hoto whiteford

Sai dai a baya bayan nan, masana kimiyyar samuwar halittu sun bullo da wata hanyar gano asalin inda kashin baya ya bulla.

Masanan sun ce muna da dangantaka ta kusa da wasu dabbobin ruwa da kuma tsutsotsi saboda a lokacin da muke ‘yan tayi, muna fara samun kofar kashi kafin mu samu baki.

Wato ke nan dai ta-kashinmu ita ce siffar da ake amfani da ita wurin gano dangantakarmu. Koda yake babu wata kama da muka yi ta zahiri da wadancan dabbobin ruwan da tsutsotsi, alamu na nuna cewa kakanninmu daya, wadanda Linda Holland, mai nazarin dabbobi a cibiyar binciken ilimin teku ta Scripps da ke Amurka ke cewa za su iya yin kama da tsutsa, ko dabbar ruwan ko kuma kamarsu dabam.

Daga cikin dangin dabbobin da kan fara yin kofar kashi kafin baki, a lokacin da su na ‘yan tayi ne aka samu wani da ya fara yin kaya.

Nori Satoh, mai bincike a cibiyar kimiyya da fasaha ta Okinawa, Japan ya ce ya gano lokacin da aka fara samun dabba mai kayar baya. Ya ce: “Ina ganin samuwar halittu masu yanayin talibamban ne asalin fara samun dabbobi masu kayar baya.”

A farkon rayuwarsu, dabbobin da kofar kashi kan riga baki fitowa lokacin su na ‘yan tayi, kan sauya daga kwai zuwa wata halitta mai kamar tsutsa, yayinda wasu daga cikinsu ke da wasu irin kananan gasu da ke taimakonsu ninkaya a ruwa, dabbobi masu kayar baya na da jela ne. Don haka Satoh ya ce: “Kayar ta bullo ne domin ta ba su damar buga jelar yayin iyo.”

Hakkin mallakar hoto naturepls

Bayan shudewar zamani ne sai tsarin jikin dabbobi masu kayar baya ya fara sauya kadan-kadan.

A cewar Holland: “Ina ganin garin girman jikin dabbobin ne ya sa su ka fara bukatar wata gabar wacce tafi kaya kwari wurin yin iyo a ruwa.”

A yanzu sai mu ga cewa sassauyawar halitta daga kakannin kakanninmu masu kayar baya, zuwa kifaye, zuwa ga dabbobin tudu masu kafafu hudu, wanda daga bisani suka mike tsaye su ka zama mutane wani abu ne dake nuna ci gaban halittu.

Sai dai kuskure ne mu dauka cewa tarihin sassauyawar halittu ya faru ne kai tsaye.

Lokacin da masu bincike a cibiyar nazarin halittu ta nahiyar Turai su ka gano wata tsutar teku a 2014 mai kayar baya, sai su ka rike ta a matsayin hujjar ra’ayin da ke ganin dabbobi masu kaya sun samo asali ne daga tsutsotsi.

Wannan ya nuna cewa ba kai tsaye halittu kan sauya daki-daki kamar yadda muka dauka a baya ba. Mai yiwuwa ne ma tun tuni kakannin kakannin kakanninmu su ka fara yin kaya amma daga bisani su ka yi watsi da ita da su ka fahimci cewa babu wani amfani da za ta yi musu a rayuwarsu ta karkashin teku.

Ashe ke nan finafinan da ke nuna daukakar dabbobi masu kaya kan mara sa kaya sun kauce hanya, tun da akalla ko dai a yawan adadi, dabbobi marasa kashin baya sun fi masu kashin bayan. Wasunsu ma ba su da dabi’o’in da muke dangantawa da dabbobi irin su motsi ko kuma mallakar kai.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Sassauyawar halittu ba shi da magaryar tukewa. Babu wani mataki da halittu ke kokarin kai wa. Kifin da ke cikin ruwa daidai ya ke da dan Adam a cikar halittarsa, kuma idan har shekaru aru-aru kafin samuwar mutane, wadansu kifayen sun yi amfani da kashin baya kuma sun yi watsi da shi, ashe ke nan babu wata daukaka da ta rataya ga mallakar kashin baya.

Don haka a kula, babu wani ci baya a kasancewa dabba mara kashin baya.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why we have a spine, when over 90% of animals don’t.