Ka san dabbar da ta fi zafin cizo?

Hakkin mallakar hoto naturepl

Dabbobi da yawa na da manyan baki cike da hakora masu tsini, amma guda daya ce tak tafi zafin cizo.

Ka yi tunanin wawakeken baki shake da daruruwan hakora masu kaifin reza, tare da karfafan gabban da za su fasa tsoka, su karya kashi cikin gaggawa.

Mun saba ganin irin wadannan bakuna a finafina irin su Jaws da Godzilla. Amma a rayuwar zahiri, wacce dabba ce tafi kowacce mugun cizo?

Maganar ba wai ta katon baki ba ce kawai. Kifin ‘bowhead whale’ ne yafi kowacce dabbba girman baki a duniya amma sam ba ya cizo da shi. Dalili kuwa: ba shi da hakora.

Sai dabba ta hada abubuwa uku kafin ta iya mummunan cizo; babban baki, kwarararan hakora, da kuma karfafan tsokokin da za su iya sarrafa bakin.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Kifin Whale

Ba kowacce dabba mai hakori ce ke iya cizo ba. Misali, dodon kodi na da dubunnan hakora a kan harshensa, amma ba ya iya cizo da su sai dai ya karci abincinsa.

A cewar Olivier Lambert na cibiyar nazarin kimiyya ta Belgium, dabbar da za ta iya lashe gasar cizo ta duniya ita ce Orca.

Ya ce: “Dabbar da tafi kowacce girma a duniya cikin wadanda ke amfani da hakoransu wurin farautar abinci ita ce kifin ‘Orca’.”

Kifin ‘orca’ kan yi girman kafa 31. Ya na da hakora 50 da yake amfani da su wurin kacaccala abincinsa tun daga ayu zuwa ga ‘ya’yan ‘whale’.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Kifin Orca ko makashi

Sai dai kifin ‘orca’ su kan yi farauta ne cikin rukuni guda don haka mi yiwuwa cizon kowanne dayansu ba zai ka ga zama gwarzon cizo na duniya ba.

In haka ne bari mu dubi mafi girman kifin da ke farauta shi kadai a fadin duniya, wato ‘shark’. Kifin dai ya shahara da hakoransa 300 masu kaifin reza, wadanda wasu ke maye gurbinsu da zarar sun fara dakushewa. Hakika cizon ‘shark’ na cikin wadanda aka fi tsoro a duniya.

Sai dai kuma da yake mukamikinsa na kaya ne ba kashi ba, yaya karfin cizonsa zai kasance? Ya zama wajibi a auna adadin karfin da ya ke sa wa a cizon kafin ba shi lambar girma a fagen cizo.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Kifin Shark da ke farauta shi kadai

Amma kuwa gwada karfin cizon makashi irin kifin ‘shark’ kamar neman tikitin barzahu ne. Da alama masana kimiyya ma sun amince da hakan shi ya sa suke gudanar da gwajin a cikin ofisoshinsu.

A 2008. Stephen Wroe na Jami’ar New England da ke Australia ya yi amfani da kwamfuta domin kiyasta karfin cizon kifin ‘shark’. Sakamakon kiyasin nasa ya nuna cewa manyan kifayen ‘shark’ na iya yin cizo mai karfin ma’aunin Newton 18,216. Domin gane wannan adadin sai mu kwatanta da bil’adama wanda mafi karfin cizonsa shi ne ma’aunin Newton 1,317.

Duk da haka an samu masu binciken kimiyyar da suka gwada karfin cizon dabbobi a zahiri.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Rikakkiyar kadar teku

Mafi karfin cizon da aka taba samu daga dabba mai rai shi ne na kadar teku, wacce aka auna a wani bincike a 2012 karkashin jagorancin Gregory Erickson na jami’ar Florida State da ke Tallahassee.

Masu binciken sun gwada dangin kada 23, inda su ke sa su cizi wata na’ura da ke auna karfin cizon. Sakamakon ya nuna rikakkiyar kadar teku na iya cizon da ya kai karfin ma’aunin Newton 16, 414, abinda ya nunka na wacce ke rike da kambun cizo na duniya a baya (wato kura) har sau uku da rabi.

Ba hakora ko dogayen mukamikin kada ke sa cizonta ya yi karfi ba, in ji Laura Porro ta kwalejin ilimin lafiyar dabbobi da ke London.

“Muna jin karfin cizonsu ya dogara ne da manyan tsokokin da su ke da su a mukamukinsu,” in ji Porro. “Idan ka kalli hoton babbar kada za ka ga wasu manyan tsokoki sun yi malolo a mukaminsu.”

Hakkin mallakar hoto naturepl

Wannan shi ne dalilin da ke sa kada karfin cizo. Sai dai kadajoin da su Erickson su ka gwada ba su ne su ka fi girma a duniya ba, don haka ba mamaki akwai wasu manyan kadajoin da karfin cizonsu ya zarta haka.

Kimanin shekaru miliyan tara da suka wuce, an yi wani garnakeken kifi a Amurka ta Kudu mai suna Megapiranha paranensisthat wanda tsawonsa ya kai mita guda. Manazarta sun kiyasata cewa karfin cizon kifin ya kai ma’aunin Newton 1,240-4,749, kuma hakoransa na da karfin da zasu karya kashi.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Ba za ka so haduwa da kura ba

Wannan na kara tabbatar da cewa girman dabbobi na kara musu karfin cizo. Don haka ake hasashen cewa manyan kakannin kadoji da kifayen ‘shark’ da ‘whale’ su ne suka fi kowacce dabba a tarihin duniya karfin cizo. Kakan kifin ‘shark’ mai suna Carcharodon megalodon a kimiyyance, ya kare a duniya kimanin shekaru miliyan biyu da dubu 600 da su ka wuce.

Masu binciken karfin cizon ‘shark’ sun yi hasashen cewa wancan kakan shark din na da karfin cizon da ya kai Newton 108,514-182,201. Wato karfinsa ya kai ya tauna mota ya gutsuttusura ta.

Hakkin mallakar hoto naturepl

Kawo yanzu dai shi ne karfin cizo mafi yawa da aka kiyasta a kimiyyance. Sai dai ba lallai ne shi ne yafi kowanne ba.

A lokacin da Carcharodon megalodon ke sharafinsa a tekunan duniya, akwai wani na’uin manyan kifayen ‘whale’ mai suna Livyatan melvillei, wanda tsawon kansa kawai ya kai mita uku.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Kwarangal din kan kakan kifin Whale

Baya ga wannan kuma ya na da hakora a bakinsa, sama da kasa. An kiyasta cewa ba’a taba samun wata dabba mai girman hakora kamarta ba: domin kuwa sun kai inci 14 kowanne.

Ashe ke nan in dai za’a bi tarihi ne za a tarar cewa babu wata halitta mai karfin cizo kamar kifin ‘whale’.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. One creature had a bit more powerful than any other.