Ka san wurin da yafi ko’ina gishiri a duniya?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Tafkin Bahar Mayit ‘Dead Sea’ ya yi matukar shuhra kan tsananin gishirin ruwansa, amma a duniya shi ne na biyar a jerin wurare masu yawan gishiri.

Idan ka na zaton teku ne yafi ko’ina gishiri a duniya, ka na bisa turba. Kaso biyu cikin uku na duniya ruwane, kuma kaso 96% na ruwan da ke duniya ya na cikin teku. Akwai biliyoyin ton na narkakken gishiri a cikin ruwan teku.

Sai dai yawan gishirin kan bambanta, a kuryoyin arewa da kudu, dusar kankara kan narke ta salanta gishirin, a yankunan da ke tsakiyar duniya kuma zafin rana na sa ruwa ya ragu, don haka sai dandanon gishirin ya karu.

Duk da haka akwai wasu wurare a cikin duniyar nan da su ka fi ruwan teku yawan dandanon gishiri.

Hakkin mallakar hoto naturepla
Image caption Sararin Sossusvlei ke nan mai dimbin gishiri a Namibia

Wanda yafi shahara a cikinsu shi ne tafkin Bahar Mayit ‘Dead Sea’ da ke kan iyakar Jordan da Isra’ila. Dandanon gishirin kogin ya nunka na teku sau 10. Sai dai a jerin wurare masu tsananin gishiri a lamba ta biyar ya tsaya.

Kalmar ‘sea’ a Ingilishi na nufin babban ruwan gishiri da kasa ta yi wa katanga. Shi kuwa ‘Dead Sea’ kasa ta yi masa kawanya ne baki daya, don haka tafki ne amma saboda tsananin gishirinsa ake kiransa ‘teku.’

Duwatsun da ke gabar tafkin na kyalkyali da rana saboda hasken gishirin da ya damfare musu daga ruwan. ‘Bahar Mayit’ shi ne tafki mai tsananin gishiri mafi zurfi a duniya, inda ya ke da zurfin kafa 1,080 daidai da mita 330.

Amma ruwan da yafi kowanne dandanon gishiri shi ne Kududdufin Don Juan da ke nahiyar Antarctica inda kaso 44% na ruwansa gishiri ne. Ba shi da zurfi ko kadan domin kuwa iyakarsa inchi hudu daidai da santimita 10.

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Kududddufin Don Juan a yankin Antaktika

An gano kududdufin ne a kwarin McMurdo Dry Valley, wani yankin hamada da tsaunuka su ka tare, inda ko dusar kankara ba ta sauka.

“Ba a dai kai ga tantance dalilin da ya sa ya ke da wannan tsananin gishirin ba,” in ji masanin yanayin kasa Jay Dickson na Cibiyar Fasaha ta California da ke Pasadena, wanda ya kwashe shekaru ya na nazarin yankin.

“Wani muhimmin abu game da Don Juan shi ne ba shi da hanyar da ruwa ke zurarewa,” in ji Dickson. “Don haka duk ruwa ko gishirin da ya shiga ciki ba shi da hanyar fita.” Don haka sai dai ruwan ya daskare ko kuma rana ta kona shi.

“Yawan gishirin Don Juan ya sa ruwan ba zai iya daskarewa ba har sai tsananin sanyi ya kai -53C, don haka sai dai ruwan ya kone ya bar gishirin da dan ruwa kadan.” Wannan na daga cikin dalilan yawan gishirin kududdufin.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Wasu tsunstsaye na yin shekarsu a kan ruwan gishiri

Yayin da raguwar kududdufan da ke Antarctica ke cike da ruwan dadi daga tsaunukan kankarar da kan narke a lokacin zafi, Don Juan ba ya samun wannan ruwan dadin. Dickson ya ce masu bincike na nan su na kokarin gano daga inda ruwan gishirin ya samo asali.

Amma in dai neman wurin da yafi tsananin gishiri a duniya mu ke yi, sai mun bar cikin ruwa mun koma kan daskararrun abubuwa.

Mafi girman wurin da ake samun gishiri a duniya ya na kasar Bolivia. Salar de Uyuni ya kai fadin murabba’in kilomita 10,500 kuma ya samo asali ne daga kafewar wannan tafkeken tafki shekaru aru-aru da suka wuce. A yanzu haka fegin cike ya ke da bangoran gishiri iyakar ganin mai gani.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Yankin Solar de Uyuni A Bolivia

‘Yan yawon bude ido kan yi tururwar ziyarar wurin domin kallon ikon Allah, yayinda tsuntsayen ‘flamingo’ ke yin kwanci a wurin.

Karkashin bangoran gishirin akwai wani gurbataccen ruwan gishiri da ke makil da sinadirai masu amfani.

Daga cikinsu, akwai rabin sinadirin ‘lithium’ na duniya baki daya. Gwamnatin Bolivia ta fara hako sinadirin, wanda ake amfani da shi wurin yin batirin kayayyakin laturonin da muke amfani da su.

Ana hakar gishiri a Salar de Uyuni tsawon daruruwan shekaru. Sai dai, mahakan, da ke amfani da diga da shebur wurin hakar gishirin tsawon shekarun nan kamar sakace su ke masa idan aka kwatanta da yawansa.

Hakkin mallakar hoto naturepls
Image caption Yankin na Salar de Uyuni yana da fadi

Wasu wuraren, inda ake matukar bukatar gishiri – domin abinci ko barbadawa a hanya domin narka kankara da sanyi – sun hako gishirin fiye da Salar de Uyuni.

Daya daga cikin kasashen da tafi kowacce fitar da gishiri a duniya ita ce Australia. Duk shekara ta kan samar da ton miliyan 11 na gishiri, inda ta kan fitar da kaso 90% zuwa kasuwannin duniya.

Mutanen Australia kan kwaso ruwan teku ne su zuba shi cikin kwami, inda zafin rana kan kafar da ruwan ya bar gishirin.

China ma na daga cikin wadanda su ka yi fice wurin samar da gishiri a duniya. Wasu alkaluma da aka fitar a Amurka a 2016 sun nuna cewa China na samar da ton miliyan 70 na gishiri a kowacce shekara.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Yankin da ke da dimbin gisihiri a Australia

Abinda ba za su iya kwasa a ban kasa ba, sai su haka rami su sa na’urar tunkudo ruwan gishiri ko kuma su hake tsaunukan gishiri ta hanyar amfani da nakiyar fasa dutse.

Mafi girman ramin hakar gishiri a duniya ya na Goderich, Canada. Ramin, mallakar kamfanin Compass Minerals ya kai zurfin kafa 1,800 da fadin murabba’in kilomita bakwai, inda ya kan samar da ton miliyan bakwai na gishiri a kowacce shekara.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Yankin da ake hakar gisihiri na Goderich shi ne mafi girma a duniya

Kasancewar ramin a yankin Manyan Tafkuna shi ne sirrin samar da gishirin da yawa. Saboda a yankin an yi wani makeken teku da ya kafe kimanin shekaru miliyan 420 da su ka wuce.

A nahiyar Turai kuwa, manyan cibiyoyin samun gishiri sun hada da arewacin Burtaniya, zuwa kogin Tekun Arewa ‘North Sea’ har zuwa ga Netherlands da Denmark da Jamus da kuma Poland.

Sai dai kuma tsaunukan gishiri mafiya girma a duniya, su na kasar Rasha ne a yankin Upper Kama da ke yamma da tsaunukan Urals. Tun cikin karni na 15 kididdigar Kirista aka kafa garin Solikamsk a yankin domin hakar gishiri. Har yanzu kuwa ana samar da kanwa daga wurin.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Tsuanukan Rasha da ke da gishiri dankare

“Zai yi wuya mu san inda yafi gishiri a duniya,” in ji Ted Nield, editan mujallar kungiyar masu nazarin karkashin kasa. “Matsalar ita ce; mafi yawan bayanan da ake samu game da samuwar gishiri ya ta’allaka ne da inda ake hakarsa, mai yiwuwa ne kuma babbar mahakar gishiri ta duniya ba a wurin da yafi yawan gishiri a duniya aka haka ba.”

Don haka iyakar abinda za mu iya cewa a yanzu shi ne; wurin da yafi kowanne gishiri a duniya wani kududdufi ne a yankin Antarctica, ko kuma karkashin wani kwari da ke Rasha.

Hakkin mallakar hoto naturepl
Image caption Wajen hakar gishiri a Salar de Uyuni

Zai iya yiwuwa kuma wani wurin ne dabam da ba wanda ya sani saboda babu wanda ya yi tunanin ya yi nazarinsa.

Idan kana so ka kaanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Earth’s saltiest place make the dead sea look tapwater.