Wa ya fi sha'awar jima'i tsakanin mace da namiji?

Shin me ya sa masana ilimin kimiyya suka gaza gano yadda tsarin sha'awa da jima'in 'ya'ya mata yake? Tambayar ke nan da Rachel Nuwer ya yi.

Shin me 'ya'ya mata suke so? Wannan wata tambaya ce da ta kawo wa mutane irin su Sigmund Freud da Mel Gibson, cikas.

Wannan batu dai ya kasance abin mahawara a littattafai da mukaloli da ma rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta kuma babu shakka wannan al'amari yana sa maza da mata tunanin yaya hakikanin abin yake.

Sai dai kuma duk da kwashe shekaru aru-aru da masu bincike suka yi don gano gaskiyar batun, har yanzu masu binciken ba su kai ga cimma matsaya daya ba kan hakikanin abin da sha'awar 'ya mace take, ballantana ma har su gano yadda sha'awar take motsa wa 'ya'ya matan.

To amma za a iya cewa an samu cigaba dangane da irin yadda mutane suka fahimci sha'awar ta 'ya mace a baya, a inda ake tunanin mata ba sa gamsuwa da jima'i sannan suna da mahaukaciyar sha'awa.

Yanzu haka, masana ilimin kimiyya suna tsaurara bincike wajen fahimtar sha'awar mata, a inda suka yanke shawara cewa gano sha'awar mace wani abu ne da ya sha bamban a lokaci daban-daban.

Sun ce ita sha'awa a wurin mace ta bambanta tsakanin mace zuwa mace sannan wata aba ce mai fadin gaske kamar yadda wani farfesa a jami'ar Rutgers ya ce "kowacce mace akwai irin abin da take so."

Mun kuma fahimci cewa sha'awar namiji da mace bai zama lallai ace suna da bambanci ba kamar yadda mutane suke tunani.

Shekaru aru-aru, masu bincike sun yi ittifaki da sauran jama'a da ke da tunanin maza sun fi mata yawan sha'awa sakamakon tabbatar da hakan da nazarce-nazarce masu dama da suka yi.

To amma wasu shaidu na baya-bayan nan sun bayyana cewa gano hakan ba abu ne da za a tabbatar ba a kan mutum daya ko kuma a lokaci guda.

Wasu nazarce-nazarcen ma sun gano cewa maza za su iya samun karancin sha'awa kamar mata.

Nazarce-nazarcen da aka yi a baya sun mayar da hankali ne wajen tambayar mutane kamar haka, "Ya ya sha'awarka ta kasance, a watan da ya gabata? Duk lokacin da aka yi wa mutane wannan tambayar, amsar da suke bayarwa ta kan nuna sun fi mata sha'awa.

Amma a duk lokacin da aka juya tambayar zuwa irin zafin sha'awar da mutum yake ji nan take, to za ka ga ba a iya tantance wane ne ya fi sha'awa tsakanin mace da namiji.

Lori Brotto wani farfesan ilimin likitancin fannin mata ne da ke jami'ar Burtaniya a kasar Columbia kuma mai ba da shawara mai zaman kansa kan halayyar dan adam.

Farfesan ya ce tambayar da ke neman sanin yadda mutum yake jin sha'awa ta jima'i, a lokacin da ake yi masa tambayar, "ta kalubalanci irin kallon da ake yi wa mata cewa ba sa iya magana a kan sha'awar jima'i koma ba sa sha'awa kwata-kwata."

Ya kuma kara da cewa "nazarin yana nuna cewa abubuwan da ka iya tayar wa namiji sha'awarsa nan take, ka iya zama iri daya da wadanda za su tayar wa matan ma tasu sha'awar."

Wasu manazartan ma sun gano cewa sha'awar 'ya mace lokacin al'ada ta sha bamban da lokacin da ba na al'adar ba. "sha'awar jima'i na tsananta ga mata, a lokacin ƙyanƙyasar kwayayen maniyyi, tamkar irin sha'awar da maza suke ji," in ji Lisa Diamond, farfesa a ilimin nazarin halayyar dan adam da jinsi a jami'ar Utah.

Ta kara da cewa "maza ba su fi mata sha'awa ba. Abin da ke akwai shi ne bambancin lokaci da yanayi."

Dangane da abin da farfesa Lisa Diamond ta yi, farfesa Anita Clayton ta sashin nazarin kwakwalwar mutane a jami'ar Virginia, ta ce akwai kanshin gaskiya a waccan maganar musamman idan aka yi tunanin karshen abin da sha'awa take haifarwa wato haihuwa.

A inda ta ce "ilimin kimiyyar halittu wanda yake nuna yadda mace da namiji ke saduwa sannan daga karshe mace ta haifi jariri, yana nuni da sha'awar jima'i," ta kara da cewa "A wannan zamanin ne kawai ake raba tsakanin sama da ɗa da bukatar yin jima'i."

A baya, likitoci sun yi tsammanin cewa sinadarin da ake saki lokacin ƙyanƙyasar kwayaye a jikin mata na da alaka da girman sha'awar da mace take da ita.

Kuma haka ma wasu nazarce-nazarcen suka gano dangane da mata masu sha'awa da ma masu matsalar rashin sha'awar.

Duk da sakamakon nazarin, mata sun cigaba da danganta rashin fitar sinadarin da ake saki a jikin mace lokacin ƙyanƙyasa da abin da ke haifar da karancin sha'awa a gare su, sannan su ma likitocin suna biye musu wajen ba su magani.

Mafi yawancin lokuta, likitocin na yin hakan ne a dakin gwaje-gwaje sannan bisa dogaro da irin sinadarin da ake saki a jikin namiji wanda ke sa mazan sha'awa. Wannan dai kuskure ne.

Idan kuma aka yi la'akari da wanda ya fi jin dadin jima'i tsakanin mace da namiji ta fannin kaiwa kololuwa ko kuma yin inzali, za a iya cewa mata ba su kai maza ba. Da yawa wasu ba su fahimci hakan ba.

Batun jima'i wani abu ne da motsa sha'awa ko kuma ya sa a yi inzalin farko wanda shi kuma zai haddasa inzali na biyu.

" A mafi yawancin lokuta, sha'awar da ke bayyana ta farjin mata da kuma nuna hakan a fuska, tana riga bukatar sha'awar jima'in da ke zuwa kwakwalwarsu," in ji Diamond.

Ta kuma kara da cewa "Saɓanin maza wadanda sha'awar jima'i a zuciyarsu ko kuma kwakwalwarsu take zuwa tun kafin a fara taba sassan jikinsu da ke sanya hankalinsu ya tashi."

Sha'awar dai ba wai kawai tana nufin bukatar jima'i tsakanin mace da namiji ba.

Kowane dan adam mace ko namiji ya bambanta da wani ko wata wajen abin da yake bukata kuma abubuwan da yake so su kan sauya lokaci zuwa lokaci.

Wani lokacin wasu matan sun fi son su sanya kansu da kansu inzali ta hanyar shafa da taba sassan jikinsu. Wasu kuma za su fi son saduwa da namiji amma ba lallai sai azzakarin namijin ya shiga farjin matan ba. Sannan ba wai lallai sai sun yi inzali ba.

Saboda haka van Anders ya ce "A hasashena sha'awa ta danganta da yanayi da kuma shi kansa mutumin, da lokaci da kuma alakarsu da abokin jima'i ko kuma ta wace hanya za a biya bukatar jima'in."

Yadda sha'awar jima'i take

Har yanzu ba a kai ga fahimtar hakikanin yadda sha'awar jima'i take ba ko kuma mene ne yake motsa ta.

"Ba ma a iya fayyace mece ce ita kanta sha'awar, ballantana a gano abin da ke kawo ta." in ji Barry Komisaruk wani babban farfesan nazarin halayyar dan adam a jami'ar Rutgers.

Sai dai kuma ana iya fahimtar dalilan da ke kawo yawan sha'awar jima'i ko kuma karancinta.

Duk mutumin da ya dade da aure ko kuma rayuwar jima'i zai san cewa ita sha'awa wata aba ce da take sauyawa daga lokaci zuwa lokaci.

Bincike ya tabbatar da cewa sha'awa na raguwa yayin da ma'aurata ko kuma masu jima'i da juna suka dade tare.

Amma hakan ya fi tasiri a tare da mata, watakila kuma saboda sinadarin da ake yawan saki a jikin ɗa namiji da ke kore masa damuwa da gajiya.

Sabanin maza, gajiyar aikin gida da zirga-zirga na haifar musu da koma baya a bangaren sha'awar jima'i da suke da ita.

"Mata da dama suna wahalar da farjinsu," in ji Nan Wise, wata masaniyar ilimin mata a jami'ar Rutgers. Ta kara da cewa " Ba wata cuta ba ce take janyo wa mata rashin sha'awar yin jima'i, illa yawan dawainiyar da ke kansu."

A wasu lokutan, rashin sha'awar yin jima'i ka iya faruwa ga mace sakamakon abokin jima'in ya fi ta yawan sha'awa, har ma ta kai macen ta ji ba ta son al'amarin.

"Zance mafi shahara shi ne mata masu karancin bukatar yin jima'i ba sa yi wa hakan kallon matsala ce har sai lokacin da suka hadu da jarababben namijin." In ji farfesa Diamond Clayton.

Hakan ne ya sa farfesa Clayton ke ganin ma'aurata ko kuma masu zaman dadiro da su nemi hanyar da za su yi jima'i ba tare da korafi ba saboda kowa akwai yadda Allah ya halicce shi.

Idan da ace akwai abin da manazarta suka gano kan hakikanin ma'anar sha'awar jima'i, to da zai zama wannan bambancin da ke tsakanin masu saduwa biyu.

Sha'awa za ta iya kasancewa mai tsanani ko kuma akasin haka, walau ga namiji ko 'ya mace daga lokaci zuwa lokaci, saboda haka, ba a iya gane irin yawan sha'awar jima'i da mutum yake da ita.

"A saboda haka, ya kamata ma'aurata ko masu zaman dadiro su rinka yin hakuri da juna."

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The enduring enigma of female sexual desire