Ka taɓa tunanin abin da ke kawo gajiya liƙis?

Mutane da dama suna fama da matsananciyar gajiya, to amma abin tambaya a nan shi ne shin laifin ayyukan da ake yi sakamakon sauyin zamani ko gajiyawar jiki ne ko kwakwalwa ko kuma gajiyawar zuciya ne? Masu nazari a BBC sun yi bincike a kan wannan.

Shekaru kadan da suka gabata, Anna Katharina Schaffner ta zamo wadda ta fuskanci matsalar gajiyar aiki.

Al'amarin dai ya fara ne daga irin gajiyawar da kwalkwalwarta da kuma jikinta kamar yadda ta bayyana da "nauyin jiki" a duk abubuwan da ta ke yi. Ko da ayyukan yau a kullum da take yi suna gajiyar da ita sannan kuma tana fuskantar matsalar mayar da hankali a kan duk abin da ta sa a gaba.

Amma kuma a duk lokacin da take bukatar hutawa, sai ta ga kawai tana kashe awowi a kan kafar imail. Ta ce "ba ni da wani karsashi sannan na zama mara tunanin yin abin da zai amfane ni."

Hakan na faruwa ga mutane da dama. Idan har kafafen watsa labarai abubuwan da za a iya gasgantawa ne, gajiya wata cuta ce ta zamani domin a duk lokacin da Shaffner ta kunna talbijin, za ta ga ana mahawara kan abubuwan da suka shafi al'adunmu, a kowace rana kuma a tsawon mako. Ta ce "duk masu sharhi a lokacin mahawar sa'anninmu, hakan na yin nuni da irin yadda muke tsiyayar da karfin da muke da shi."

Shin dole ne a rayuwa mutane su zama cikin dawainiya yau da kullum?

Masaniyar tarihi kuma wadda ta shahara a fannin sanya ido kan rubutun adabi, Shaffner, ta nemi zurfafa bincike dangane da hakan.

Kuma sakamakon bincike nata ya kasance a kunshe a cikin wani littafi da ta rubuta mai suna 'gajiya' ko kuma 'exaustion' a turance. Littafin dai ya yi nazarin kan yadda likitoci da masu ilimin falsafa suka gano iya karshen wurin da tunanin dan adam da karfin jikinsa da kuma irin kuzarin da yake da shi, suka tsaya.

Babu tantama cewa gajiya wani batu ne da kowa ke neman sanin abin da ke haddasa shi musamman idan aka yi duba ga dimbin yawan mutanen da a kullum ke safa da marwa domin ganin likitoci.

Wani nazari da aka yi a kan likitocin Jamus, ya gano cewa kaso 50 daga 100 na likitocin suna fama da matsalar gajiya.

Likitocin na fadin yawan kokawa da yadda suke samun gajiya a kowacce awa sannan kuma ba sa iya yin wani tunani sosai, bayan kammala aikin ganin marasa lafiya, da safe.

Sai dai kuma wani abin sha'awa shi ne yadda mata da maza suke iya shawo kan matsalar gajiya, ta hanyoyi mabanbanta juna.

Wani bincike da aka yi a baya-bayan nan ya gano cewa maza masu aiki da suke kokawa da matsalar gajiya, sun fi matan da ke da matsalar ta gajiya, daukar hutu saboda rashin lafiya.

Bisa la'akari da cewa matsananciyar damuwa na haddasa rashin karsashi da kauracewa mutane, wasu sun musanta cewa matsalar gajiya da aiki wata aba ce da ke damun ma'aikata.

Shaffner, a littafinta, ta rawaito wata makala a wata jaridar Jamus da ke nuna matsalar gajiyar aiki wani abu da ke sanya ma'aikata samun matsananciyar damuwa.

Zancen da ya fi shahara dai shi ne mas'alolin biyu na Gajiyar aiki da Matsananciyar damuwa abubuwa ne guda biyu da suka sha banban.

Manazarta sun yi ittifakin cewa matsananciyar damuwa na tattare da rashin karfin gwiwa ko kuma mutum ya tsani kansa da kansa ko kuma ya dauki kansa ba a komai ba, wanda ba haka abin yake ba dangane ga Gajiyar aiki.

Bisa la'akari da wata mahawara, ba a gina kwalkwalwar dan adam ba ta yadda za ta rungumi ayyukan zamanin nan. Bukatar da ake da ita ga ma'aikata na su zama masu kwazo a kan ayyukansu da kuma tunanin ma'aikatan na ganin sun yi abin da ake neman su yi, suna jefa su cikin firgici na din-din-din.

Ga wasu, damuwa ba ta tsaya kawai a aiki ba. A kullum, mutane suna fama da fadi-tashi na rayuwa a birane, har ma wasu ba sa iya samun lokacin da za su dan sarara, walau da rana ko dare. Hakan kuwa na nufin rashin lokacin hutu a gare mu matsala ne.

Sai dai kuma Schaffner ta gano cewa tuntuni a kwai gajiya, kafin ma bayyana ayyukan zamani.

Daya daga cikin rubuce-rubuce na farko-farko shi ne wanda wani likita dan Roma ai suna Gale, ya rubuta. Kamar yadda marubucin likitancin nan Hippocrates ya rubuta, Gale ya ce duk wasu cututtuka na fili da na boye da dan adam ka iya fuskanta, suna da nasaba da daidaiton abubuwa guda hudu.

Abubuwan hudu dai su ne:

  • Gudanar jini
  • Yadda sinadari mai ruwan dorawa da hanta ke fitarwa domin niƙe maiƙo yake ɗiga.
  • Yadda bakin sinadarin da hanta ke fitarwa domin niƙe maiƙo yake ɗiga.
  • Majina

Gale ya ce idan baƙin sinadarin da hanta ke fitarwa wajen markade maiƙo, hakan zai kawo tsaiko wajen jujjuyawar sassan jiki sannan zai toshe hanyoyin kwalkwalwa. Hakan kuma zai haifar da rashin karsashi da lalaci da saurin gajiya da kuma zama cikin bakin ciki ( huzunu).

Duk da cewa wannan jawabi ba shi da makama a kimiyyance amma za mu iya fahimtar cewa kwalkwalwar dan adam tana cike da wani sinadari da ke kawo cikas a tunani irin matsalar da masu fama da gajiyar aiki suke kokawa a kai.

Sahihiyar magana dai a nan ita ce, ko da mutanen da suka gabace mu sun yi fama da matsalar gajiya, abin da ke nufin cewa gajiya da rashin karsashi, wasu abubuwa ne da Allah Ya halitta a jikin dan adam.

Gaskiyar magana dai ita ce har yanzu ba a iya gano abun da ke sanya mutane samun kuzari a jikunsu ba da yadda kuzarin yake yin rauni ko da kuwa ba tare da sun yi wani aiki a zahiri da zai sa su gajiyar ba.

Ba a kai ga fahimtar ko abubuwan daga zuci ne ko kuma daga gangar jiki suke ba ko kuma suna faruwa sakamakon yadda al'umma take ko ma hallayarmu ce take sanya su. Zance mafi shahara shi ne abubuwan na faruwa ne sakamakon kowanne abu da aka lissafa.

Schaffner ba ta kore yiwuwar samun gajiya ba sakamakon amfani da kafafen sada zumunta na zamani. Ta ce "ta hanyoyi da dama fasahar zamani da aka yi da manufar ta sanya mutane su samu hutu, ta zama wani dalilin da ke haddasa wa mutane gajiya."

Idan za mu yi la'akari da tarihi, za a iya cewa matsalar gajiya ko kuma matsananciyar damuwa ba su da magani kamar yadda mutanen da ba su iya magance cutar damuwar ba.

Masu fama da matsalar gajiya ko matsananciyar damuwa ka iya tuntubar masana domin sanin yadda za su shawo kan matsalolin.

Ita kanta, Schaffner ta gano yadda za ta kubuta daga gajiya da damuwa.

Idan kana son karantawa da harshen Ingilishi sai ka latsa wannan The reasons why exhaustion and burnout are so common