Ko tuntuɓen harshe na da alaƙa da son yin jima'i?

Shin ko tuntuɓen harshe na faruwa ne sakamakon rashin sanin abin da mutum zai fada ne ko kuma kawai dai wani abu ne daga kwakwalwar dan adam? Ga binciken da BBC ta yi a kan haka.

A shekarar 1988, a lokacin da mataimakin shugaban Amurka na lokacin, George H. W. Bush, ya kai ziyara jihar Idaho.

An kuma tsara cewa mista Bush zai gabatar da wani jawabi, kai tsaye ta gidan talbijin wanda ba a rubuta ba, a kan tsarin inganta sha'anin noma sannan kuma ya tattauna kan irin nasarorin da suka samu tare da shugaban kasar, Reagan.

A yayin jawabin wanda ba a rubuta ba Bush ya ce "Mun samu nasarori. Mun kuma yi wasu kura-kurai. Mun kuma yi jima'i da mata.....uh...."

Har yanzu ana tunawa da wannan tuntuben harshe kuma ana danganta tsohon shugaban kasar ta Amurka, George Bush wanda ɗa ne ga George W. H. Bush, da al'amarin.

Tuntuben harshe na faruwa ne a yayin da kake son fadin wani abu amma sai ka fadi wani abu daban wanda ma zai iya zama matsala.

Tuntuben harshe ya kasance wani abun da duk wani wanda zai yi jawabi a taron jama'a yake shakka. To ke mene ne yake haddasa wannan subul-da-baka? Kuma ko suna da wata ma'ana ta musamman?

Sigmund Freud wanda ya kirkiro fannin nazari kan alakar zance da kwalkwalwa, ba ya gamsuwa idan ya tambayi mutanen da suka zo wurinsa domin su tuntube shi kan subutar baki.

Za a iya gano matsalar ne kawai idan aka abun da ke faruwa idan mai magana ya zama bai mayar da hankali ba a lokacin da yake magana.

Tuntuben harshe dai ka iya sanya mai magana ya bayyana wasu abubuwa da ya boye a cikin zuciyarsa kamar sha'awar jima'i.

Freud kamar Darwin wanda shi ma wani manazarcin ne, ya ce gano dalilin da ya sa mai magana yake yin tuntuben baki ba abu ne mai sauki ba..

Amma kuma masu nazarin kan yare da wadanda suka kware a fannin kimiyyar kwalkwalwa sun ce Freud ya yi kuskure ta ko wane fanni. To amma abin tambaya a nan shi ne shin abin da Freud din ya yi ba dai-dai ba ne?

Wani nazari mai cike da fasaha, da aka yi a baya, a inda aka yi amfani da jima'i tare da jan wutar lantarki.

A lokacin da aka fara gwajin, an yi amfani da wata farfesa wadda shekarunta suka dan ja, a inda ta je ta gashe da biyu ko uku daga cikin gungun maza masu son saduwa da mata.

Gungun mazan na uku kuma an shiga da shi cikin wani daki wanda a ciki akwai wata mace wanda ta ci kwalliyar da dole ta ja hankalin maza.

"Abin da ke faruwa a jami'a ne ya faru. Ta dauki hankalin mazan, a inda take sanye da guntun dan tofi da bulawus mai shara-shara." In ji Michael Motley wani mai nazri kan halayyar dan adam a jami'ar California.

An umarci mutanen da su karanta jerin wasu kalmomi da aka rubuta mu su a takarda, a asirce, kuma da sauri da sauri.

Abin da ba su sani ba shi ne an yi mu su hakan ne da manufar sanya su su yi tuntuben baki a wajen furta kalmomin.

Mazan da suke tare da matar da ta yi ado irin na jan hankali sun yi ta yin tuntuben harshe mai alaka da sha'awar jima'i.

Su kuwa ajin mutanen na uku an sanya yatsunsu a cikin wani inji wanda yake da karfin jan mutane kamar wutar lantarki. Mutanen kuma sun ta samun tuntuben baki mai alaka da abin da ake yi mu su wato jan wuta.

A karshe masu binciken sun gwada irin kaifin sha'awar jima'in da kowanne daya daga cikin mutanen ya ke da ita. Kuma sai aka gano cewa masu tsananin sha'awa sun fi yin tuntuben harshe mai alaka da son yin jima'i.

Fyodor Dostoyevsky wani manazarci dan kasar Russia ya fahimci cewa Kokarin dakile abin da mutanen suke rayawa kamar sha'awa, ya sa suke fadawa tarkon yawan tunanin son yin jima'i.

A shekarar 1980, masanin tunanin dan adam, Daniel Wegner ya ba da shawarar cewa matakin da ake dauka wajen gujewa subul-da-baka, shi ne yake haddasa yawan yin tsartsen baka.

Bisa ga nazarin da Daniel ya yi, idan mutum yana cikin halin dimuwa, ya kan zama ba ya iya yin tunanin da ya dace.

Kuma maimakon mutum ya yi shiru, a lokacin wannan yanayi, sai ya fara tunanin abin da zai fada.

Hakan na janyo afkuwar tuntuben harshe. "Idan mutum yana tunanin wani abu, to zai kasance yana zabar kalmomin da yake son yin amfani da su wajen magana." in ji Motley.

Sai dai kuma ba ko wane ya amince da sakamakon binciken na Freud ba. Mutumin da yake matukar sukar ayyukan Freud wato Rudolf Meringer, wanda ya yi aiki a jami'ar Vienna, karni na 19, ya yi nazari a kan dubban tuntuben harshen da jama'a suka yi wadanda kuma ya samu daga wurin abokan aikinsa, a lokacin cin abincin rana.

An tattara bayan nan ne dai ta hanyar nadar kura-kuan magana da mutanen suka yi.

Wannan nazari ne ya sanya Meringer ya yanke cewa tuntuben harshe wani yanayi ne da kalmomi suke yi wa mai magana kutse, ba ma'anar kalmomin ba.

Shi kuwa Rob Hartsuiker, wani masanin fannin ilimin alakar da ke tsakanin kwakwalwa da magana a jami'ar Ghent, ya ce mafi yawancin kura-kuran da mutane ke yi ba da saninsu ba ne.

Rob ya ce hakan na faruwa ne sakamakon neman kalmar da za a yi amfani da ita.

Nazari ya nuna cewa mafi yawancin mutane su na gamuwa da tuntuben harshe, sau akalla 22, a kowace rana.

An gano cewa mutane suna yin kuskure da ke kunya ta su, a kokarin yin bitar jimlolin da mai magana yake yi a zuci kafin ya furta a baka.

Mutane sun fi yin karo da irin wannan matsalar ta subul-da-baka idan mai magana yana cikin yanayin tsoro ko firgici ko idan ya gaji ko ida yana cikin maye ko kuma idan mutum ya tsufa.

Har wa yau, idan mutum yana magana da sauri, to zai iya samun tuntuben harshe. idan kana sha'awar karanta na turanci za ka iya latsa nan What Freaudian Slips Reveal About your Mind