Mece ce haƙikanin ƙyamatar mutane?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Mutane da dama ba sa iya gane suna ƙyamatar wasu banbancin launin fata ko kuma na jinsi. Ba kuma sa fahimtar illar yin hakan har sai sun ga shaida a kimiyyance. Ga shaidar za mu kawo:

Kasar da nake zaune a ciki, tana da dokokin da suke hana kyamatar wani walau dai saboda da addininsa ko jinsinsa ko kuma saboda irin kyamar da nake da ita ta hanyar biyan bukatar jima'i.

Mun wuce zamanin nuna wariyar musamman lokacin da ake daukar luwadi a matsayin haramtaccen abu.

A baya an haramtawa mata yin zabe. Duk da cewa yanzu an kawar da dukka wadan nan abubuwan a yanzu, hakan ba yana nufin cewa kyamatar mutane ta zama tarihi.

Har yanzu akwai ragowar nuna banbanci da ke tasiri a zukatan mutane. Misali idan har kana jin kana kyamar wani wanda kuke da banbancin wani abu da shi to hakan nuna banbanci ne.

Hanyar da ake gane tasirin nuna kyamar ita ce kin jinin wani abu a zuciya ko kuma kushe ra'ayin da ya saba da naka.

Mai yiwuwa ne masu irin wannan nuna kyama ba su son suna dauke da dabi'ar ba a tare da su.

Masana hallayyar dan adam sun banbance tsakanin abubuwan da zukatanmu suke kudirtawa da kuma abubuwan da muke bayyana a fili ta fuskar ayyukanmu.

Misali, mutum zai iya cewa shi ba ya son yin jima'i ko kuma zai iya kiran kansa wanda ya tsani masu sha'awar jima'i amma kuma idan ka hadu da mata sai ka rinka nuna halayyar masu yin jima'i.Hakan kuma ya sha banban da hakikanin abin da ka kudurta a zuciyarka.

Wadan da abin ya shafa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani wanda aka nunawa kyamata

Har yanzu dai akwai ragowar kyamatar mutane a zuciyar wasu kuma hakan na nuin nuna fifiko ga wasu bisa wasu.

Wannan ya sa magance matsalar kyama ba abu ne mai sauki ba.

Abin da zan mayar da hankali akai dai shi ne yadda kabilar mutum take tasiri kansa musamman dangane da mu'amalarsa da sauran jama'a.

A farkon shekarar 1970, wani gungun mutane da Carl Word na jami'ar Princeton yake jagoranta, ya debi dalibai turawa domin yin wani gwaji, a ina aka fada musu cewa ana son gano hazakar masu neman aiki ne.

duk da rashin gasgata cewa aikinsu shi ne zakulo daliban da suka fi hazaka, mutanen wadanda fararen fata ne sun nuna kyama ga wasu masu neman aikin saboda launin fatarsu. Sun ki yarda su zauna a kusa da su da kuma kin yin mu'amala da su kamar kallon su ko jingina a jikinsu a lokacin tattaunawa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna har yanzu batun nuna kyama gaskiya ne.

binciken da Princeton ya gudanar bai fadi cewa an kyamaci wani mutum saboda launin fatarsa.

To amma an nuna wa bakake masu neman aikin wariyar launin fata, ta hanyoyi da dama da suka hada da ba su kankanin lokacin zaman yin jarrabawa.

Irin wadan nan gwaje-gwajen ba sa bayar da hakikanin gaskiyar abin da ma'anar kyamata ke nufi.

Abin da wannan nazari ya nuna shi ne. idan kana son karanta wannan labarin a harshen turanci sai ka latsa wannan Prejudice is always not overtly