Me ya sa babu na'urar fassara mafarki?

Mutane suna ta faman tattara bayanai kn mafake-mafarken a jama'a ke yi, shekara da shekaru. To amma shin me tattara bayanan mafarkin yake nufi ga tunanin dan adam? Kuma ko fasahar zamani za ta iya gano hakan?

Wata rana, ana tsaka da Yakin Duniya na Biyu, Lars, wani dan kabailar Hopi a Amurka, mai shekara 36, yana shirin tafiya aiki. Mutanen da ke yankin su Lars ba su fuskanci matsala ba sakamakon yakin.

To amma al'ummar yankin na su Lars suna sauraron abin da ke faruwa dangane da yakin ta kafar radiyo, a kowane dare. Lokacin da Lars ya kwanta barci, a wannan daren, ya yi mafarkin labaran yakin da ya saurara a radiyon.

Ya kwanta a kan gadonsa yana mafarki kan wani birni a Turai. Lars dai bai taba zuwa birnin ba amma kuma birnin ya yi masa kama da birnin Paris na Faransa.

Kuma a mafakin nasa, Lars ya kasance yana zagaya wani wuri da bam ya lalata sosai. Ya yi mafarkin ne dai a kan birnin Paris, amma kuma da ya ci gaba da mafarkin, daga baya sai ya fuskanci cewa, a wani kwari ne kusa da unguwar da yake. Daga bisani dai Lars ya farka.

Yanzu haka dai Lars ba ya duniya, to amma an fahimci abin da ya yi mafarki a kai a wannan dare.

An tattara bayanai kan mafarke-mafarke da dama daga sassa daban-daban na duniya ta hanyar nadar sa .

A yanzu haka, a duniya, fasahar sadarwar zamani ta bayar da damar kirkirar mafarke-mafarken.

Hakkin mallakar hoto Getty

Bugu da kari, ana amfani da wasu manhajoji a kan wayoyin komai-da-ruwanka da suke fassara adana mafarki.

To amma tambayoyin a nan su ne wace irin ma'ana wadan nan manhajojin za su sanar da mu dangane da fassarar mafarke-mafarken? sannan kuma wane mutum ne ya fara tunanin tattaro mafarke-mafarken?

Za a iya cewa kishirwar sanin ma'anar mafarki ta fara ne tun lokacin da dan adam ya fara magana.

To amma an fara kokarin tattaro mafarke-mafarken jama'a ta yadda mutane za su iya samun bayanan a duk lokacin da suka bukaci haka, tun a lokacin yakin duniya na biyu.

Yanzu haka, an wallafa irin wannan aiki na tattara bayanan mafarke-mafarke wanda Bert Kaplan, wani Ba-Amurke masanin ilimin halayyar dan adam, ya tattara.

An wallafa mafarke-mafarken a cikin wani littafi mai suna Kundin Mafarke-mafarke wanda aka yi wa lakabi 'Database of Dreams' a turance.

Shekaru da dama da suka gabata, masana zamantakewar dan adam sun taimaka wajen aikin yi wa mutane daga sassa daban-daban na duniya, tambayoyi.

Hakkin mallakar hoto istock

Kuma ana adana bayanan da aka tattara na hirar da aka yi da mutane, a katunan adana bayanai na kamuta, a wurare daban-daban.

Lemov ta kwashe shekaru takwas tana zirga-zirga tsakanin dakunan karatu domin neman bayanan na mafarki.

A wasu lokuta ba a taba kundin bayanan ba shekara da shekaru kuma har ta kai ga masu kula da dakunan karatun suka fara zubar su a cikin juji.

Amma a lokacin da Lemov ta samu wasu bayanan da take nema, ta samu mafarke-mafarke daga mutane daban-daban daga fadin duniya.

Shirmen mafarki

Bayanin kan mafarkin wata mace 'yar Lebanon wadda ta yi mafarkin ta-ci-barkatai, a lokacin da take fama da zafin zazzabin Typhoid.

A mafarkin nata dai, matar ta yi hasashen mahaifinta ya karbi kayan marmari na tufa daga hannunta, a inda ya sauya mata da kudin kasar Turkiyya da aka yi da zinariya.

"A lokacin da na farka daga barci na ga ban ga kudin ba, sai na fara kururuwa," in ji matar.

Hakan ne ya sa Lemov fadin cewa "mafarki ba ya tafiya kai tsaye domin suna bacewa," kuma "ba na tunanin fasahar sadarwa ta zamani za ta iya hana hakan."

sai dai akwai masu ganin cewa fasahar zamani za ta iya taimakawa wajen gano ma'anar mafarki.

Misali manhaja kamar Dreamboard da ta Shadow suna ba wa masu amfani da su damar nadar tare da adana mafarke-mafarkensu.

Su dai wadanda suka kirkiri manahajar sun yi hakan ne domin sanya mutane su fahimci ma'anar mafarki da darasin da mutum zai iya samu daga mafarkin.

Gane ma'anar mafarki

Image caption Likitocin kwakwalwa na kokarin gano ma'anar mafarki

Hunter Lee Soik, wanda ya kirkiro manhaja ta Shadow ya yi tambaya cewa ko mutane za su iya kwarewa wajen gano ma'anar mafarki?

Hakan tunanin Patrick McNamara ne wani masani kimiyyar kwakwalwa da halayyar dan adam da ke jami'ar Boston.

McNamara yana son gano banbance-banbance tsakanin mafarkib mutane kamar alakar abubuwan da mutum yake gani a mafarkin.

Hakan zai ba da damar sanya mafarke-mafarken a ma'auni iri guda wajen fahimtar ko mafarke-mafarke suna da ma'ana ko babu.

Sai dai kuma "ban ce mafarki ba shi da ma'ana ba, abin da nake cewa shi ne kawo yanzu dai ba mu kai ga gano hakan ba."

ya kara da cewa "ilimin kimiyya bai amince da wata fasaha da za a iya fahimtar ma'anar mafarki ba."

Maganar dai da ta fi shahara ita ce mafarki wani abu ne da ba za a iya cewa ga yadda yake ba kuma har yanzu ba a iya yin gamsasshen bayani a kansa.

Biliyoyin mutane suna mafarki a duk dare. kuma neman sanin ma'anar abin da mafarkin yake nufi ba zai taba karewa ba.