Kana jin kamar kanka na tarwartsewa da daddare?

Hakkin mallakar hoto SPL

Wani rubutu da da BBC ta yi a kan larurar da ke damun wasu mutane wadanda a wani lokaci da daddare sukan ji kamar bam ya tashi a kansu, ta sa masu karatu da dama sun bayyana mana labarai masu daure kai a kan larurar.

Kamar yadda William Park ya sheda mana

A kasidar da BBC ta rubuta kwanan nan kan yadda ake rayuwa da larurar da mutum kan ji kamar kansa ya tarwatse, mun tattauna da Niels Nielsen yadda yake rayuwa da larurar.

Duk da cewa kusan ba a san wannan larura ba sosai, abin mamaki mutane da dama na da ita, kusan kashi 18 cikin dari na daliban da aka yi wani nazari a kansu sun ce sun taba samun matsalar.

Nielsen ya bayyana larurar da cewa, '' za ka ji wani kara ne kwatsam da kuma wani hasken wuta". Wannan bayanin ya sa yawancin mutane sun bamu labarin yadda su ma suka taba jin wannan abu yadda ya faru da su.

Misali Garry Fowler, ba shi da masaniya kan yadda larurar take:

"abin ya faru da ni sau da dama amma ban san abin da ke haddasa shi ba ko kuma ma a ce wata larura ce da aka san da ita."

Kuma ba shi kadai ba ne ba shi da masaniya a kan larurar. Mat Porton ya bayyana cewa sai da ya ji ana tattaunawa akan matsalar ne a tashar Rediyon BBC 4 ya san cewa matsala ce da aka san tana faruwa.

Jess Dominguez shi ma ya yi karin bayani da cewa, '' na ji dadi da na san cewa ba larurar tabin hankali nake da ita ba kuma wannan abu ne na gaske wanda ya faru da ni.''

Ga wasu mutanen irinsu Kimia Mokhtari Aubin, sau daya matsalar ke faruwa ga mutum a rayuwa, amma kuma wasu na zama da tunani da kuma fargabarta shekaru da dama bayan ta faru

Ta hanyar email Aza Mohammed ya ba mu labarin yadda abin ya faru da shi tun yana yaro a Iraki. A lokacin yakin Iran da Iraki, an kwashe shi da 'yan ajinsu daga makarantarsun saboda fargabara tashin bam.

A wannan daren wata kara mai tsanani ta tashe shi daga barci, inda ya tashi ya gudu zuwa wurin iyayensa yana kuka, inda suka gaya masa cewa ba wani bam da ya tashi.

Har bayan shekara 30 da aukuwar lamarin bai iya bayar da bayanin dalilin da ya sa kunnensa yake rugugi ba na wanna kara tsawon lokaci bayan ya tashi daga barci.

Hakkin mallakar hoto Thinstock

Mutane da dama kamar Ivy Deseaux Putnam, sun ce karar da mutum ke ji ta wannan larura kamar ta harbe-harben bindiga ko tashin bam ce.

Ya ce, '' kara ce kamar ta harbin bindiga a dakina, ko wata kofar gilas aka fasa ko wata gagarumar fashewa a saman gidana.''

Wendy Derbyshire ta kara da cewa:

" A gaskiya na dauka bam ne ya tashi a unguwarmu, amma sai na ga ba haka ba ne, lokacin da na duba waje na ga ba wata hatsaniya ko gujeguje. Karar ta wuce hankali."

Irene McNeil ta email ta bayyana mana yadda abin ya same ta da yadda ta ji. Ita ma ta ce ta ji abin ne kamar karar harbin bindiga, amma kuma ita abin ya sa mata tsananin ciwo da wani yanayi a makogaronta wanda sai bayan watanni da aukuwar abin ya fara raguwa.

Ba wani kuma cikin wadanda suka ba mu labarin yadda abin ya same su, wanda ya gaya mana yadda ya yi musu tsanani haka. Ta gaya mana cewa har yanzu tana jin wani abu a makogwaronta bayan shekara 30 da aukuwar abin.

Hakkin mallakar hoto SPL

Ana ganin matsalar rashin barci na iya kara hadarin gamuwa da wannan larura ta jin kamar kanka ya tarwatse.

Ana danganta matsalar da kasa barci, kuma ana ganin dukkanin larurorin kusan suna da sanadi iri daya ne, saboda haka da dama daga cikin mutanen da suka ba mu labarinsu na matsalar, kamar Zoe Stewart ya hada larurorin biyu.

Ya ce, ''ina da duka matsalolin biyu. Matsalar kasa barci tana min in ji kamar ruwa na ci na, ina ta kokarin in yo sama, amma na kasa. Tarwatsewar kai kuwa, mutum zai ji ne kamar wani yana kunna wani kara ne mai tsanani, da ya cika ma kunne ta ko'ina.''

Idan ka hada wannan larura da ta kasa yin barci za ka ji abin ya kai tsanani matuka. Kuma bayan karanta labarin Rachael Roseann Blythe mun ma rasa yadda za mu iya kwatanta karfin tasirin da hadakar larurorin biyu za su yi wa jikin mutum.

Hakkin mallakar hoto SPL

Idan mutum ya yi tunanin haduwar wannan matsaloli a kansa a lokaci daya, wato ganin haske mai tsanani, da jin kara mai tsananin gaske, da kasa motsi, sannan kuma da jin tarwatsewar kanka duk a lokaci daya.

To hakan zai sa wasu su yarda da irin labarin nan na kunne ya girmi kaka (na yadda wasu aljanu ko dodanni za su sace mutum su tafi wata duniya da shi).

Bayan karanta rahoton matsalar da BBC ta fara rubutawa, wasu mutanen sun bayyana yadda suke rayuwa da larurar, tun da yanzu sun san yadda za su gane ta.

Emily Rose Matthews ta ce, ''a yanzu tana iya gane alamun larurar da ta fara taso mata'' saboda tana samunta akai akai, kuma tana iya daure wa cutar da ta taso mata don kada ta kai ga tsananinta.

Rubutun ya sosa wa yawancin mutane inda yake musu kaikayi, kuma ta fito fili cewa kowa da yadda yake jin irin tasa larurar (wadanda suke da ita).

Nielsen ya ce yanzu larurar ba ta damunsa sosai, amma ga wasu masu larurar matsala ce da za su ci gaba da rayuwa da ita yau da kullum.Kai ma kana da wannan larura?

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Does your head explode at night?