Ko kallon wasanni na iya sa mana ƙarin san wasannin?

'Yan wasannin Olympics na ci gaba da ƙayatar da mutane a duka fadin duniya. To amma ko nawa ne daga cikin mu za su bar shinfiɗin su su bazama filayen wasanni sakamakon kallon da su ka yi?

Ga nazarin da Claudia Hammond ya yi mana.

A da, na kan shafe rana ɗaya a ƙarshen mako ina zaune a kan kujera mai laushi ina kallon gasar wasan Tennis ta duniya. A lokacin ji nake kamar na tashi na ruga a guje a lokacin da na ke kallon, to amma kuma ba na so wasan ya tsere min.

Hakkin mallakar hoto Getty

A duk lokacin da na ke kallon kowane irin wasan Tennis, ina tunanin cewa ya zan samu kai na a ce ni ma gashi ina fafatawa? Na kai shekaru 20 ina wannan tunanin, to amma fa ko sau ɗaya ban taɓa ko da saka ƙafa ta a cikin filin wasan ba. Kuma hakan na nuna ba wai ni kaɗai ba ne ke cikin irin wannan yanayi.

A duk lokacin da wata ƙasa ta ke fafutukar samun damar ɗaukan baƙuncin wasu wasanni, ɗaya daga tsare tsaren da suke yi shi ne suna so su ga ƙarin mutane na shiga harkokin wasannin.

Lokacin da hukumomi a Birtaniya ke ƙoƙarin samun damar karbar baɓuncin wasannin Olympics a birnin London, minstar wasanni Tessa Jowell ta ce suna fatan a karon farko su tsara wasu manufofi da su ja hankalin sama da mutane miliyan biyu su shiga harkokin wasanni zuwa shekarar 2012. Wasu miliyan ɗaya kuma za su shiga al'amuran wasanni na aƙalla sa'o'i biyar a mako. To sai dai daga ƙarshe ba haka ne ya faru ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Birtaniya ba ita kaɗai ba ce ke da irin wannan rashin cikar burin ta fuskar wasanni. Domin maimakon wasannin su ƙara sa jama'a sha'awar wasanni, tamkar rage musu karsashi su ke yi.

Bayan wasannin da aka yi a birnin Sydney a shekarar 2000, 'yan Australia sun rage yadda suke taka rawa a wasanni, sannan teɓa ta ƙaru ga mutane, musamman matasa.

Bayan wasannin Olympics da aka yi a birni Athens, abubuwa sun fara kyautata, domin adadin mutanen da ke wasannin ya ƙaru da kaso 6, sai dai shekaru biyar bayan haka adadin ya rage da kashi 13, abinda hakan ya sa al'amuran wasannin su ka samu koma baya fiye da gabanin wasannin na Olympics.

Haka kuma bayan wasannin Olympics da aka yi na lokacin hunturu a Vancouver a shekarar 2010, babu wani sauyi na adadin mutanen da suke yin wasannin zamiya.

Wasannin da suka zama zakka su ne na Olympics da aka yi a Barcelona cikin 1992, inda mutane da dama su ka shiga harkokin wasanni sosai bayan wasannin.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wataƙila zai zama kuskure idan aka zaci cewa akwai alaƙa kai tsaye tsakanin kallon wasanni da kuma yin wasannin kansu.

A lokacin da ake wasannin, za ka ga hankulan mutane na tafiya wajen wasu abubwuan daban. Za ka samu wasu maimakon a ce sun fita fili suna ta guje-guje a rana, za ka same su zaune a kan kujerun alfarma, suna karkaɗa ƙafa, yayin da suke ci gaba da kallon talabijin cikin yanayi na alfarma.

A nazarce dai akwai hanyoyi uku da kallon wasa zai iya ingiza mutum ya shiga wasannin. Hanya ta farko ita ce ƙarfafawa mutane masu sha'awar wasanni gwiwa su ƙara ƙaimi fiye da da.

Hanya ta biyu ita ce, ka ƙarfafawa mutanen da a baya su ke da sha'awar wasannin su farfaɗo da sha'awar da suke da ita, su koma fili.

Hanya ta uku kuma ita ce zaburar da mutanen da sun jima da sha'awar wasanni -amma ba su taɓa yin wasannin ba- su fara shiga al'amuran wasannin.

Hakkin mallakar hoto Getty

Za ma ka iya cewa, tsofaffin 'yan wasa suna cire mana sha'awar wasanni, domin muna ganin ba za mu taba iya zuwa da inda suka je ba. Muna tunanin cewa ko da mun jima muna atisaye to da wuya mu je kusa da su.

Shin kana da lafiyar yin irin abin da ka ke gani a talabijin ko kuma a filin wasanni? Kuma shin kana ji za ka iya kwatantawa?

Wani bincike da aka gudanar kan kwaikwayo ya bamu haske kan dalilin da ya sa al'amuran wasanni ba su da wani tasiri kan matasa wajen saka su rige-rigen shiga al'amuran wasanni.

Wani masanin halayyar ɗan adam a jami'ar Stanford Albert Bandura ya gano cewa jama'a suna saurin kwaikwayon wata ɗabi'a da suka gani. To sai dai shin haka lamarin ya ke a wasanni ma?

Bandura ya bayyana wasu abubuwa da ke sa mutum ya kwaikwayi wasu abubuwa. Na farko, sai mutum ya maida hankali. Domin idan mutum bai yiwa wata ɗabi'a duban tsanaki ba, to babu yadda za a yi ya kwaikwaye ta.

Na biyu kuma dole mutum ya ringa tuna abin da ya gani ɗin.

Hakkin mallakar hoto Getty

Sannan kuma ka na buƙatar wanda zai ringa sa maka karsashi ka yi wannan abin da kan ka. hakan na iya zama ta hanyar samun wani tukwici kamar ka ji kana ƙara samun lafiya ko kuma ka na samun nasara.

Hakan dai na iya kasancewa idan kana kallo kana kuma buga wasanni.

To amma akwai abu na huɗu, shine shin ka na da lafiya kuma ka yarda za ka iya?

Irin rawar da 'yan wasanni ke takawa cikin zafin nama, za mu iya cewa da ba za mu iya kwaikwayon su ba.

Da daman mu za mu iya zama kan kujeru muna sha'awar yadda Usain Bolt ke falfala gudu, to amma nawa ne daga cikin mu su ke iya sawa kan su lokaci dan ganin cewa sun yi gudun mita 100?

Hakkin mallakar hoto Getty

Duk da cewa ana buƙatar samar da kayan wasanni, akwai wasu abubuwa da ya kamata a duba da suke sa mutanen ba sa ƙaunar wasanni a baya, a kuma duba me ke cire musu sha'awar wasannin? Sannan shin mutum zai iya haɗa wasa, da aiki da kuma kula da iyali?

Idan kana so ka karanta wannan labari a Inglishi latsa nan. Do big sporting events make us do more sport?