Wane dalili ne ke sa kwarmi a ƙasan ido?

Rashin baccin dare da wuri, da kuma yin bacci kadan na daga abubuwan da suke haifar da kwrmi a kasan idanun mutane.

Daga cikin amfanin rashin gashi a jikin ɗan adam akwai cewa 'yan kananan ƙwari kamar su Kwarkwawta da kuɗin cizo da kaska ba za su damar ɓuya a jikin mu ba.

Ƙarancin gashi na bamu damar fitar da gumi da kuma sanyaya mana jikinmu.

A zahiri ta ke cewa fatar ka ta yi fes, yayin da hakan ke nunfin za mu iya isar da sakwannin cikin sauki daga fukar mu zuwa wasu mutanen, hakan na kuma na da ta sa illar; domin wani cikin sauƙi zai gane cewa ka gaji liƙis ko kuma kana cikin wata damuwa, domin kuwa; labarin zuciya a tambayi fuska.

A liktance dai ba ko yaushe ne kwarmin da ke futowa a ƙarƙashin idanun mutane ke da wata illa ba. sai dai wani rahoto da aka buga a wata mujallar gyaran fata a shekarar 2007, wani mai bincike ɗan ƙasar Brazil Fernanda Magagnin Freitag ya bayyana cewa mutane da dama za su iya damuwa sosai da kwarmin na ƙarƙashin idanu, har ma su ringa danganta baƙin da wajen ke yi da rashin samun ingantacciyar rayuwa.

Dan haka ya kamata a bincika matsalolin fata da za su iya kaiwa ga irin wannan tunanani, da kuma haifar da matsananciyar damuwa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Abunda ba mu sani ba shi ne fatar da ke ƙasan idanunmu ba ta da ƙwari. Kuma hakan ya sa ta zama mai fale-fale. Wannan dai ya sa jijiyoyin jini da ke a fuska ba su da wata kariya sosai, sannan hakan na maida fatar ta zama baƙa.

Baƙin da ake gani yana kasancewa ne sakamakon yadda hasken rana ya ke dukan fatar fuskar mai rauni.

"Idan wani ya zo ya ce min yana da kwarmi a ƙasan idanun sa, ina so in duba shi," a cewar Haley Goldbatch wata ƙwararriyar likitar fata. Ta ce sabo da rashin ƙarfin fatar na iya zama ɗaya daga dalilan da za su iya sa kwarmin ƙasan ido da kuma baƙi a wajen.

Domin kau da duk wani shakku, Goldbach ta ce ta na so ta ringa yi wa fatar wajen aiki. Idan har baƙin ya ci gaba to hakan na nufin cewa akwai matsala a zubin jijiyoyin wajen. Idan kuma ana samun raguwa, to hakan na nuna cewa raunin fatar ne kawai ke janyo kwarmin da kuma baƙi a ƙarƙashin idanun.

A fuska, akwai hanyar da hawaye ke bi tsakanin hanci da ido da kuma kumatu, wanda likitocin fata ke ambata 'hanyar hawaye.

A duk lokacin da shekarun mutum su ka tura, kaurin fata yana raguwa a cewar masaniya Goldbatch, kuma a cewar ta hakan yana sa hanyar hawayen ta ƙara rarakewa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Masaniyar ta ƙara da cewa babban dalilin da ya ke sa ƙasan idon mutum ya yi baƙi shi ne sauyin da jikin mutum ke samu, musamman ma raguwar kitsen da ke ƙarƙashin fatar mutum idan shekarun sa su ka yi nisa. Kuma a cewar ta wannan ne ya sa ƙarƙashin idonun ke yin kwarmi, kuma wajen ya yi baƙi, sannan alamun gajiyawa su bayyana a fuskar mutum.

To sai dai wannan bayani ba zai haɗa da matasan da ke samun wannan mastala ba sabo da rashin bacci, da karancin hutu.

Haka kuma wasu bayanai na nuna cewa yawan shiga wajen da ake amfani da tsananin hasken na'ura domin ɗaukar hotunan jiki ko ƙona wasu cututtuka, na daga abinda ke haifar da kwarmin a idanu. Haka ma shan giya da shana taba na haifar da wannan matsala.

Wani dalilin kuma da ke sa wannan matsalar shi ne taruwar ruwa a fuskar mutum, musamman kusa da idanun sa, a cewar Goldbach.

Wani lokacin kuma da zarar ka tashi daga bacci za ka tarar da fatar ƙarƙashin idanun ka ta yi rauni.

Yawan cin abinci mai gisihir da yawa ma na iya haifar da wannan matsala. Idan ka ci abincin ada aka zabgawa gishiri ka kuma kwanta za ka iya tashi da kwarmi a ƙasan idon ka.

Akwai ma wasu hujjojin da ke nuna cewa idan mutum ya sosa idanun sa, ko ya yi kuka na iya haifar da wannan matsala ta kwarmin ƙasan idanu.

Hakkin mallakar hoto Getty

An kuma tabbata cewa mayukan ƙara hasken fuska su ma na haifar da kwarmin na ƙasan idanu.

To sai dai fa duk da waɗannan bayanai, babu wasu isassun hujjoji na kimiyya da za su yi bayani kai tsaye kan hanyar magance larurar kwarmin a ƙarƙashin idanu, sabo da dalilan wannan matsaloli suna da yawa, kuma likitocin fata na ganin matsala ce ta shafe shafe.

To amma duk da haka ana ƙoƙarin nemo magungnan wannan matsala, kamar amfani da ruwan da aka tatso ta jikin wasu bishiyoyi.

Haka kuma akwai wasu sindarai da ake yi wa mutum allurar su da, sannan a wasu lokutan ma ana tiyata.

Wani mai bincike ya taɓa bada shawarar cewa allurar wasu sinadarai da ke ƙunshe da carbon dioxide sau ɗaya a sati har tsawon wata biyu zai iya taimakawa. Kuma masanin ya ce wannan mujarra bi ne.

Wasu masu binciken sun yi ƙoƙarin amfani da sinadarin vitamin C.

To amma matuƙar ba a samu wani magani kaifiyyan na wannan matsala ba, a dai dai lokacin da masanan ke lalube cikin duhu kamata ya yi jama'a su yi hakurin rayuwa da wadannan kwarmin a idanunun su a matsayin wani ɓangare na hlittun jikin su.

Idan kan so ka karanta wannan a cikin harshen Ingilishi latsa nan. Why do we get bags under our eyes?