Me ya ke saka mu sosa jikin mu?

Rashin jin daɗi ne ya ke sa mu ringa sosa jikin mu, mu sosa, mu kuma ƙara sosawa. To in haka ne me ya ke sa faratan mu su ke ringa kawar mana matsala a jiki, suna kuma saka mana jin dadi?

J R Travert wata mata ce da ta gamu da matsalar ƙaiƙayin jiki a lokacin da take kimanin shekaru 40 a duniya, sannan har ma bayan wasu shekarun arba'in. Masaninyar ta ma'adanai ta gama gamasuwa cewa ita da wasu matan biyu danginta cewa suna da wasu 'yan ƙananan halittu da ke addabar su a jiki. Bayan shekaru goma sha bakwai ta na yunƙurin raba kansu da wannan ƙaiƙayi, masana kimiyya sun buga wata maƙala dangane da matsalar da ta addabi fatar ta su, da nufin ko za a samu wani da zai iya nemo makarin matsalar.

A wani yunƙuri na magance larurar, Travert ta ziyarci likitoci, da ƙwararrun likitocin fata, da ma wasu likitocin.

Ta yi amfani da waƙan su magungunan ƙwari masu illa a matakai daban-daban duk a yunkurin raba kanta da ƙwarin da a rayawar ta suke sa mata kaikaiyi.

Ta kuma yi anfani da faratanta ta ringa kartar jikinta har ma ta na fitar da jini.

A wasu lokutan ta kan aika burbushin fatar da ta futar daga jikinta da kuma jini zuwa masu gudanar da binciken cututtuka ta amfani da sassan jikin mutum.

Wani likita mai dabara ya taba tura ta a bincika ko tana da matsalar tunani, to amma ta shedawa likitan da zai yi binciken cewa kar ma ya bata lokacin sa.

"Har yanzu duk magungunan da ake yi min sun kasa magance min matsalar ta ƙaiƙayi," A cewar ta.

A yanzu an gano cewa ashe dai babu wasu ƙwari da ke addabar Traver da dangin ta har tsawon shekaru 40. Suna fama ne da wata larura ce a ƙwaƙwalwalar su da ke sa mutum ya ringa neman maganin wata matsala da ya ke rayawa a zuciyar sa, kuma yake neman shedar da zai gano haƙiƙanin matsalar ta sa. A lokuta da dama hakan na jefa mutum cikin wasu matsaloli.

Hakkin mallakar hoto iSTock
Image caption Kusan kowa daga cikin mu yana jin kaikayi a kullum, to amma ba mu san dalilin hakan ba

Labarin Traver ya na kama da na waɗanda suke fama da irin wannan larura. To amma fa ba kasafai aka fiya samun masu irin wannan matsalar ba.

Ƙorafi a kan ƙaiƙayi yana ɗaukar ƙasa da kaso biyu da rabi cikin dari na lokacin likitocin fata. To sai dai susa abu ne da kowa ke yi a kowa ne lokaci a duka faɗin duniya. Babu wanda ya san dalilin da ya sa muke jin ƙaiƙayi.

Ta'arifin da yake karɓaɓɓe dangane da ƙaiƙayi har yanzu a wajen likitoci da masu bincike shi ne wanda wani likita ɗan ƙasar Jumus Samuel Hafenreffer ya ya yi shekaru 350 da suka gabata.

A cewar sa ƙaiƙayi shi ne "wani rashin jin daɗi da ke haifar da buƙatar kartar wajen". Kamar yadda wannan bayani ya nuna wannan kartar ita ce susa. Wannan ta'arifin na iya zama abin dogaro, to sai dai ba a ko wane lokaci ne hakan ya ke zama daidai ba.

A matakin farko, ƙaiƙayi da kuma jin ciwo a wajen tamkar suna da dangantaka. Wasu 'yan halittu ne ke baibaye wani bangare na fata, wadanda aikin su shi ne su aike da wani saƙo zuwa laka da kuma ƙwaƙwalwa cewa akwai wasu matsaloli a wajen, wanda hakan ne ke haifar da ƙaiƙayi.

Sosa jiki.

Ƙaiƙayin zai iya kasncewa sabo da dalilai da dama, kuma hakan ya sa aka kasa samun wata hanya guda daya ta magance shi.

Akwai kaikayin da zai iya faruwa sabo da wani abu da ya faru haka kaiwa, kamar cizon kwari.

Akwai kuma kaikayi mai tsanani da zai iya faruwa wanda ake danganta shi da wasu dalilai kamar bushewar fata, ko borin jini, ko kuraje, ko ma wasu ciwukan fata, ko matsala wajen rabon jini a jiki, ko tsananin ciwon hanta, ko ciwon sida (AIDS) duk suna da dangantaka da kaikayi kamar yadda masana cututtuka suka bayyana.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Ana iya rage zafin kaikayi ta hanyar shan magungunan rage radadi

Sosa wajen da yake kaikayin shi ma yana taimakawa, kamar yadda shafa wasu magungunan rage radadi ke yi, a wasu wuraren ma har a kan iya amfani da lantarkidan rage matsalar.

Rudani tsakanin kaikayi da kuma jin zafin susa har yanzu abu ne da aka kasa yin bayanin sa.

Yayin da wani abu ya faru, jiki yana saurin maida martani. Ga wani gajeren misali. Saka hannun ka jikin harshen wuta, za ka ji kana so ka dauke hannun.

To amma dangane da susa, ita tana gayyato wasu halittu da sinadarai ne wajen da aka sosa, kuma hakan na nuna cewa mai yuwuwa a samu wata illa ta susar.

Duban kurilla da kuma susar jiki na matukar tasiri wajen magance kwari fiye da yadda suke dauke radadi. Susa ba wai kawai tana raba fata da kwari ba ne, ta na ma kore wasu tsirrai a jikin fata da kuma wasu abubuwa da ba a bukata da ke addabar fata ko kuma gashi.

Ga yadda abin ke faruwa: Idan wani abu ya faru a fata, kamar cizon sauro, kwayoyin jini suna sakin wasu sinadarai kamar na histamine. Hakan kuma na sanya wata halitta a jikin fata ta aike da wani sako zuwa laka, da ita kuma ke aikewa da wannan sakon ta cikin jijiyoyi har zuwa kwakwalwa.

Hakkin mallakar hoto iStock

Shin kana jin kaikayi a jikin ka har yanzu? Idan haka ne, watakila sabo da kamar hamma ita ma susa na iya yada cututtuka.

Likitoci na cewa suna jin kaikayi idan suka duba mutanen da suka zo da matsananciyar larurar fata.

Sannan masu bincike sun taba bada wata makala kan susa dan kawai su gano ko za su iya saka mahalarta bukatar sosa jikin su, hakan kuwa aka yi.

Wasu na'urorin daukar bidiyo da aka bobboye sun nuna cewa mahalarta sun shafe lokaci mai tsawo suna sosa jikin su a lokaci da ake ci gaba da gabatar da makalar.

Bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar mutum yana iya kama sosa jikin sa da zarar ya ga wani yana susar.

Ana dai ganin zafin da ake ji yayin kaikayi bai kai jin radadi idan an yi susa ba.

A wata makala da aka buga a mujallar zuzzurfan bincike kan al'amuran fata a jami'ar Washington, wani kwararre George Bishop ya nuna cewa, "kartar da mutum zai iya yi wa kan sa yayin susa mai tsanani na iya zama sauki da kuma jin dadi idan aka kwatanta da kaikaiyin da yake ji".

Yayin da mutum ya ke jin dadi idan ana yi masa susa, hakan na kuma iya haifar da babbar matsala musamman idan ka yi wa mutuma da yake fama da ciwukan fata susa.

Wasu marasa lafiya da ke fama da ciwon fata na cewa suna sosa jikinsu har ma su daina jin dadin susar.

Dan haka ne ma wani mawaki ya ke cewa Babban abin jin da dai shi ne da ka ji kaikayi kawai ka sosa wajen.

Idan kana so ka karanta wannan a cikin harshen Ingilishi latsa nan. Why it feels good to scratch an itch