Yadda za ka koyi harasa 30

Wasu mutanen suna magana da yarukan da idan ka ji sai sha mamaki. Ta ya suke iya yin hakan? Tambayar ke nan da David Rabson ya yi.

Tim Keeley da Daniel Krasa na zaune a wata baranda a birnin Berlin, babu abinda suke sai musayar kalamai cikin harasa daban daban. Da farko suna magana da Jamusanci, sai suka juya Indiyanci, sai harshen Nepal, sai yaren Poland, sai na Crotia, haka dai suka ringa yi daga wannan yare su koma wannan, har sai da suka yi magana da yaruka sama da 20.

A can cikin ɗaki kuma, wasu mutane ne ke zaurace a harsuna daban-daban. Lamari ne dai mai daure kai. To sai dai fa su a nutse suke. Mu wannan ai abu ne mai sauki a wajen mu". A cewar Alisa wata mata dake cikin mutanen.

Koyar wani harshe zai iya zama abu mai wahala. Duk da haka dai na je Berlin ne dan wani taro na waɗanda suka iya harasa da dama. Wasunsu ka iya ce musu 'yan baiwa, domin suna iya magana da harasa sama da goma. Ɗaya daga mutanen da na haɗu da su shi ne wani gangaran mai suna Richard Simcott, wanda ya ke jagorantar wani kamfani na kwararru a harasa da dama da ake kira eModeration. Shi kaɗai yana jin yare kimanin 30.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Idan ka yi la'akari da kwakwalwa, za ka ga cewa babu mamaki yadda da daman mu kan sha wahala wajen koyan wasu harasan. Muna da banbanci wajen yadda muke haddace abubuwa.

Idan har kana so ka naƙalci ko wane irin yare, to dole ka haddace aƙalla kalmomi dubu goma. Hakan dai ba ya na nufin ka naƙalci nahawun harshen ba. Dole ne ya kasance wadannan kamlmomi za su iya zuwa kan harshen mutum cikin gaggawa a duk lokacin da yake magana, ba tare da wani jinkiri ba.

Yin magana da wani harshen yana jinkirta matsalar komabaya da ƙwaƙwalwa ke samu da shekaru biyar ko ma sama da haka.

Bincike da aka gudanar daban daban ya nuna cewa yin magana da wasu yarukan na inganta saurin faɗaka da kuma hadda.

Ellen Bialystok na jami'ar York a Canada ya yi wani nazari, inda ya gano cewa idan mutum ya iya harsuna uku, yana samun jinkirin mastalar ƙwaƙwalwa da shekaru huɗu zuwa shida, wanda ya iya yaruka huɗu kuma zai samu jinkiri da

Hakkin mallakar hoto Getty

Koyon sabon harshe a lokcin da mutum ya ke ƙara manyanta ya fi sauƙi fiye da yadda muke zato.

A da masana na cewa mun yi girman da ba za mu iya koyon wani sabon yare ba, kuma mu yi magana da shi sosai.

Akwai wasu nazarce nazarce da suke nuna cewa yara ba sa iya saurin karya harshen su a wani yaren da suka koya kamar yadda manya ke yi. To sai dai binciken da Bialystok ta yi ya nuna cewa wannan zulaƙe ne, ita ta gano cewa idan shekarun mutum suna ƙara yawa, ikon sa na koyar sabbin abubuwa na daƙushewa.

To sai dai fa ni duka wadanda na haɗu da su a Berlin da suka iya yaruka da dama sun koya ne bayan sun girma. Keenly ya taso ne a Florida, inda ya hadu da Spaniyawa a makaranta. A lokacin da yake yaro, yana kamo gidajen radiyon kasashen waje, - duk kuwa da cewa ba ya iya fahimtar ko da kalma ɗaya. A cewar sa, yarukan tamkar waka ce. Sai da ya girma ne ya fara yawo a duniya, inda ya fara zuwa Colombia, ya koyi Faransanci, da Jamusanci da yaren Portugal a makaranta.

Sannan kuma ya koma Switzerland da gabashin turai, daga nan kuma sai Japan. A yanzu yana maganan da harasa 20 ba gargada, kuma kusan dukkanin su ya koye su ne bayan ya girma.

Hakkin mallakar hoto Getty

Abin tambaya a yanzu shi ne ta ya irin waɗannan mutane ke iya sarrafa harasansu zuwa yaruka da dama? Kuma ko za mu iya kwaikwayon su? Babu abinda zai hana. Kawai dai wataƙila waɗannan mutanen da muka sani sun fi wasu himma ne. To amma fa a wajen mutanen ba wai lallai sai mutum ya zama ɗan baiwa ba kafin ya koyi wasu yarukan.

Masana halayyar ɗan adam tun daɗewa sun bayyana cewa kalmomin da muke furtawa suna da alakƙa da nuna ko mu su waye. Kuma kowane harshe na da alaƙa da al'adu da ke shafar yadda mu ke mu'amalolin mu.

Hakkin mallakar hoto Getty

Harasa daban daban na iya tunawa mutum abubuwa daban daban na rayuwar sa, kamar yadda wani marubuci na Rasha Vladmir Nabokov ya gano lokacin da yake rubuta tarihin sa.

Da farko dai ya yi rubutun ne a harshen sa na biyu wato Inglishi, wanda kuma ya yi shi da gumin goshi. Lokacin da aka buga littafin ya yi tunanin fassara shi zuwa harshen sa na yarinta. To sai dai yayin da ya fara amfani da kalmomin Rashanci sai wasu sababbin abubuwa suka ringa shiga cikin rubutun. Kuma a nan ya ga cewa akwai buƙatar ya sake fassara su zuwa Ingilishi.

A cewar Keeley ƙoƙarin da mutum ke yi na hana shigar da wasu al'adu za su iya hana shi koyon wasu sababbin harasan. A baya bayannan ya gudanar da wani bincike kan masu magana da Sinanci da ke koyon harshen mutanen Japan dan gano yadda wasu al'adu ke shiga cikin wasu. Ya nemi ra'ayin mutanen kan wasu tambayoyi da ya tsara kamar, "Ina kokarin kwikwayar mutanen da ke kusa da ni dan gano irin yadda suke ji", " Zan iya burge wasu mutanen" da kuma tambayar cewa "ko za ka iya sauya ra'ayin ka dan dacewa da na mutanen da kake tare da su? Sakamakon binciken ya gano masa cewa, mafi yawan mutanen da suka bada amsar 'eh' a kan wadannan tambayoyin sun naƙalci sababbin harasan da suka koya.

A zahiri take cewa idan ka rabu da wasu mutanen, akwai yiwuwar cewa za ka kwaikwaye su, kuma hakan wani mataki ne da zai ƙarfafa koyan wani harshe.

Masani Keeley na cewa dole ne mutum ya samar da wani ɓangare a kwakwalwar sa da zai ringa adana kowane harshe da al'adar sa da kuma abubuwan da ka koya dake tattare da harshen, in har yana so ya ringa amfani da shi ba tuntube, ya kuma guji cuɗanya shi da wasu harasan . "Ba wai tsawon lokacin da aka ɗauka ana koyon wani harshe shi ne yake da muhimmanci ba, yadda aka yi amfani da lokacin na da matuƙar amfani". A cewar sa.

Wani abu mai muhimmanci a cewar Harris shi ne kowa zai iya koyar yadda zai saje da wata ɗabi'a, kuma ya zama yana da 'yan wasu dabaru na yadda ya kamata ya fara.

Abu mafi muhimmanci shi ne mutum ya fara kwaikwayon yadda ake magana da harshen, ba tare da ya damu da yadda ake haɗa harufan kalmomin ba. Ya kuma bada shawarar cewa ya kamata mai koyar wasu harasa ya lura da yadda ake motsa baki yayin furta sauti, hakan a cewar sa zai sa mutum ya furta harufan daidai.

Daga ƙarshe ya ƙara da cewa dole ne mutum ya yi ƙoƙari ya kaucewa kunyata kansa wajen furta baƙin kalmomi kamar wasu kalmomi na larabci. Kada ka ringa ɗauka cewa ba yarenka ba ne, dan haka kana iya furta shi duk yadda ka ga dama.

Ya kamata ka ringa jin cewa wannan harshen naka ne, kamar yadda jarumi a finafinai yake ƙoƙarin gamsar da masu kallon sa cewa duk abin da yake yi da gaske ne, to haka kaima dole ka ringa furta kalmomin tare da ƙarfin gwiwa, ta haka ne mutane za su saki jiki su ringa magana da kai da harshen.

Hakkin mallakar hoto Thnkstock

To amma fa duk da haka, dole ne ka yarda cewa ba za ka iya zama kamar mai magana da harshen na asali ba, musamman ma a lokacin da ka ke fara koyon harshen. Idan akwai wani abu ɗaya da zai hana mutane koyon wani harshe kamar yadda ya kamata, bai wuce mutum ya ɗauka cewa sai ya yi magana da harshen kamar yadda masu shi ke yi ba.

Kuma dole ne ka ringa yin magana da harshen da ka koya a kai a kai ko da kuwa kaɗan-kaɗan ne - ko da minti 15 sau huɗu a kullum -, kamar yadda wani masani Alex Rawlings ya ce. Ya kara da cewa ko da ba ka da damar yin magana da harshen sabo da gajiya ko rashin samun abokin yin hira, za ka iya sauraron gidajen radiyon da ke yaɗa shirye shirye da harshen, kuma jin waƙoƙi ma zai taimaka.

A Birtaniya, da Australia da Amurka abu ne mai sauƙi ka ga mutum ya ce shi ba ruwan sa da yin wani yunƙurin koyon wani harshe. Ko nima gabanin haɗuwa da waɗanda suka ƙware wajen magana da harasuna daban-daban, ina ganin ba lallai ne sai muutum ya ɓata lokacin sa wajen koyon wani harshe ba. To sai dai daga baya na gano cewa akwai alfanu mai yawa, ciki har da yin abokai da suke magana da harshen.

Alal misali, Harris ya bayyana zaman sa a Dubai - a matsayin bayahude da ke zaune a gabas ta tsakiya - da cewa zama ne da ya fuskanci ƙalubale. To sai dai daga ƙarshe babban abokin sa ya kasance ɗan ƙasar Lebanon. Kuma ya ce lokacin da za su rabu abokin na sa ya ce masa, da farko bai taɓa tsammanin za su zama abokai ba, dan haka ba ya jin daɗin rabuwar da su yi.

Wacce ta shirya taron na Berlin Judith Meyer, ta bayyana cewa, ta ga 'yan Ukrain da Rashawa, da Isra'ilawa, da Palasaɗinawa tare suna tattaunawa, suna koyon sababbin harasa a wajen taron. Shi kuwa koyon wani yaren yana buɗe wata kofa ce ta sabuwar duniya.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to learn 30 languages.