Yadda ake rayuwa cikin makanta

Nunin rayuwa cikin makanta mai taken Dialogue in the Dark da ake gabatarwa a Isra'ila na da burin kyautata alaka tsakanin mutane masu ido da kuma makafi. Wakiliyar BBC Tiffanie Wen ta ziyarci cibiyar da ake nunin domin koyon hanyoyin da kwakwalwa kan sauya domin rayuwa ba idanu.

Na san ba ko digon haske, amma duk da haka na shiga lalube cikin bakin duhu saboda sabo da yi.

A lokacin da nake tattakawa a hankali cikin dakin da ke shimfide da darduma, tare da dogara sandata irin yadda jagoranmu ya koya min minti guda da ya wuce, ina iya jin saututtukan tsuntsaye, da motsin iska na karkada ganyaye tare kuma da kwararar korama a kusa da ni. Bayan da na yi tuntube da dokin kofa, sai nai sallama da darduma na fito wani fili mai kwazazzabo. Wata kakkarfar iska ta fara bugun fuskata yayin da saututtukan daji su ka kewaye ni ta ko'ina.

"To yara! Yanzu mun shigo daji. Me ku ke iya ganowa a nan?" in ji jagoranmu, Meair Mattityahu, dan shekaru 45, wanda ya makance jim kadan bayan haihuwarsa. "Na gano bishiya!" in ji wata yarinya 'yar shekara 11 wacce ta zo tare da iyayenta daga New York. Ni dai ina can sun bar ni a baya, ina laluben hanya. To kuma tun da na ji cewa akwai bishiyu a wurin sai na shiga fargabar in na kara taki daya zan iya karo da bishiya.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan dai shi ne daki na farko cikin bakwai na cibiyar nunin rayuwa cikin makanta da ake gudanarwa a gidan adana kayan tarihi na Holon da ke kasar Isra'ila.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta kiyasta cewa akwai makafi miliyan 38 a fadin duniya, da kuma karin mutane miliyan 110 da ba sa gani sosai kuma su ke fuskantar barazanar makancewa. Manufar wannan nunin dai, wanda aka kirkira a Jamus a 1988, kuma ake yadawa zuwa kasashe da dama, ita ce kyautata fahimta tsakanin masu gani da makafi, ta hanyar bai wa maziyarta damar dandana yadda rayuwar makafi ta ke. Mattityahu ya ce wasu maziyartan kan firgice, su fara ihu kamar ba za'a iya jin su a cikin duhu ba tare da sun daga murya ba. Wasu kuma su kan kyalkyale da dariya. An ma taba samun wanda ya sume. Ya ce "wasu mutane su kan rude su kasa gane dama da hagu. Idan na ce musu su yi amfani da hannun hagu domin su lalubo bango, sai su kasa."

A cikin ziyarar ta minti 90 dai, mun shiga kwalekwale, mun kewaya wani gida, mun yi tafiya a kan titi, mun sayi kayan marmari a shago, sannan kuma mun sayi lemon kwalba a kanti, duk a cikin duhu dundum! Duk da yake ziyarar na da firgitarwa da farko, lallai ta na da wayarwa. Bayan kimanin rabin sa'a da farawa, sai ji na, na kunne da na tabawa su ka karu. Sai lalube cikin duhun ya fara sauki a lokacin da na ci gaba da kutsawa daga daki zuwa daki.

Hakkin mallakar hoto Getty

An shirya kwakwalenmu ne ta yadda za su yi cikakken amfani da duk abinda aka ba su. Ga masu idanu, bangaren kwakwalwar dake lura da gani yafi bangarorin da ke lura da ji da tabawa yawan jijiyoyi, abinda ke sa idanunsu gane wurararen da su ke cikin hanzari. Ga wadanda ba sa gani kuwa, sai jijiyoyin su tattara a bangaren kwakwalwa mai kula da ji da tabawa. Bincike akan dangantakar makanta da kwakwalwa, ya gano cewa makanta kan sauya yadda kwakwalwa ke aiki, inda masana su ka gano cewa mutanen da suka makance kan yi amfani da bangaren kula da gani na kwakwalensu wurin sarrafa ji da tabawa, kamar yadda wani mai bincike a jami'ar McGill, Patrice Voss ya bayyana.

Binciken na Voss ya kuma nuna cewa mutanen da su ka makance tun da kuruciya sun fi masu gani iya gano ta inda sauti ke fitowa musamman idan ta bangaren kunne daya ne. Haka kuma wasu masanan sun gano cewa makafi sun fi masu gani gane muryoyi da kuma hadda.

Koda yake mutanen da su ka makance da girmansu ma, kan samu sauyi a yadda kwakwalwarsu ke aiki, Voss ya ce wadanda su ka makance tun da kuruciya sun fi samun sauyin aikin bangaren gani fiye da wanda su ka makance da girmansu.

Ya ce "Kwakwalwa ma ta na tsufa. Don haka muna girma ikonta na sauya tsarin aikin sassanta na raguwa. Amma wanda ya makance tun da wuri, kwakwalwarsa kan samu kwarewar sarrafa abubuwan da basu shafi gani ba a sassan da ya kamata su sarrafa ganin."

Hakkin mallakar hoto Getty

Mutane kuma kan bada misali da Ray Charles da Stevie Wonder a matsayin makafin da su ka yi matukar kwarewa a fannin kida. To akwai binciken da ya nuna cewa makanta kan kara karfin ji da kuma sarrafa sauti. Ga misali, wani bincike da aka yi a 2004 ya gano cewa makada makafi sun zarta takwarorinsu masu ido kwarewa wurin nakaltar sautin kida tare da maimaita shi ba tare da kuskure ba.

A cewar Mattityhau "Mutane da yawa na daukar rashin gani a matsayin mutuwar tsaye. Amma ni a wuri na ji yafi gani amfani. Ba na iya gani, amma ina iya ji, in rike magana, in isar da sako, in yi tafiya - wato dai ina cikakkiyar rayuwa tamkar kowa."

Mattityahu ya ce baya ga fahimtar yadda rayuwar makafi take kuma, daya daga cikin manufar shirya nunin, shi ne maziyarta su rika kimanta makafi bisa kwarewarsu ba wai su rika kallonsu a matsayin nakasassu ba. Ya ce "Zan so a ce rayuwata a waje za ta yi daidai da ta wurin nunin nan. Babu wanda ya taba ganina cikinku kafin zuwa nan, amma duk kun amince da jagorancina. In da kuwa a cikin haske muka hadu, ba wani daga cikinku da zai tunanin neman taimako daga makaho. Na kan tambayi kai na ko me yasa haka? Yadda na iya jagorantarku a cikin duhu, zan iya jagorantarku a cikin haske."

Hakkin mallakar hoto Getty

Ba wai rayuwar zahiri ce kawai ke zama kalubale ga makafi ba, har ma da duniyar fasahar zamani. Ko yaya makafi ke amfani da fasahar zamani?

Ba mamaki ba ku sani ba, amma mafi yawan wayoyin komai-da-ruwanka da kwamfutoci su na da tsarin da ke bada damar a yi amfani da su ba tare da gani ba. Wayoyin Android suna da manhajar da za ta sarrafa su ta hanyar magana irinsu Talk Back da Vlingo ko kuma ta hanyar tabawa kamar Explore by touch. Wayoyin Apple kuma su na da manhajar VoiceOver.

Haka kuma, akwai manhajojin LookTel Money Reader da Color Identifier, wanda ke amfani da kyamarar wayar salula wurin gane takardun kudi da kuma launuka. Akwai kuma Ray App mai saukaka tsarin wayoyin Android domin amfanin makafi.

Na yi amfani da wayar iPhone bisa tsarin VoiceOver na tsawon mako guda. Sai dai nan take na rikice saboda amfani da waya bisa manhajar VoiceOver ya sha bamban da yadda na saba. Misali, shafar fuskar waya daga sama zuwa kasa da dan yatsa daya, ba ya sa shafin da ake karantawa ya yi sama, sai dai in an yi amfani da yatsu biyu. Don haka sai na yanke shawarar neman taimakon kwararru.

Liran Frank injiniyan kwamfuta ne kafin ya makance sanadiyyar ciwon ido. Ya ce "Ba fasahar taimako kadai makafi ke amfani da ita a wayoyin salula ba. Muna amfani da duk manhajojin da masu gani ke amfani da su irin su Netflix, Google Maps, Moovit, Whasapp, da sauransu. Amfani da VoiceOver na da matukar sauki da zarar ka gane yadda ya ke aiki. Ina amfani da wayata kamar yadda mai gani ke amfani da ta sa."

Jan labulen fasaha

Bayan kwarya-kwaryar darasi a wurin Frank, wanda ke koyawa makafi yadda za su yi amfani da wayoyin komai-da-ruwanka da kuma na'urorin kwamfuta tare da samar da darussan sauraro na dabarun amfani da VoiceOver, sai na fara amfani da manhajar VoiceOver a wayata tare da jan labulen fasaha wanda ya mayar da fuskar wayar dundum kamar a kashe ta ke.

Cikin yini guda, sai hannuna ya fada kan amfani da wayar da take dundum. Saututtuka daban-daban da wayar ke bayarwa su na taimakawa kwarai wurin sarrafata. Misali akwai sautin da ke nuna ka gama goge rubutun da ka ke gogewa, akwai mai nuna ka bude abinda ka ke son budewa ko kuma ka fita daga kan iyakar fuskar wayar. Ana kuma sarrafa wayar ne ta hanyar shafarta da 'yan 'yatsu daga daya zuwa hudu ta sigogi dabam-daban.

Misali, kwankwasar fuskar wayar sau biyu na tsayar da karatu, kamar idan wayar na karanta wani sako da ka riga ka saurara. Haka kuma idan ka mintsini fuskar wayar sai ta baka jerin abubuwan da zaka iya yi cikin manhajar da ka bude kamar lissafo sauran shafukan da ke cikin gidan da ka shiga ko kuma karanto maka bakaken rubutun da ka yi daya bayan daya domin tabbatar da cewa ka rubuta kalmomin daidai.

Ta kai ina iya duba sakonnin i-mel, aikawa da sauraron rubutattun sakonni, bude shafukan intanet, kiran waya da kuma sauraron wakoki. Bayan kuma na saurari darasin Frank, ina iya amfani da Google Maps.

Hakkin mallakar hoto Getty

Hakan ba ya nufin ban fuskanci matsaloli ba. Baya ga lokacin da na dauka wurin koyon amfani da manhajar, akan samu kalubale duk lokacin da aka sake inganta wata sabuwar manhajar wayar salula. Yayinda ake tsara wasu manhajojin domin su dace da tsarin VoiceOver, wadansu manhajojin kan dace ne ba tare da sanin masu kirkirarsu ba. Frank ya ce akwai wata manhajar motocin sufuri da ya ke amfani da ita akan tsarin VoiceOver amma da aka kara ingantata sai ya zama an dora ma ta abubuwan da VoiceOver ba zai iya dauka ba. "Muka hada kai mu ka rubuta mu su wasika. Sai su ka aiko mana cewa ba su taba sanin makafi na iya amfani da manhajar ta su ba amma tun da haka ne za su so makafi su ci gaba da amfani da sabuwar manhajar. Don haka su ka hada kai da mu, mu ka dauko wani mai shirya manhajar salula ya yi wa sabuwar manhajar ta su tsarin da za ta iya ci gaba da aiki a VoiceOver."

Frank na ganin zai fi kyau a mai da hankali wurin tsara manhajojin da masu gani ke amfani da su ta yadda makafi ma za su iya amfani da su maimakon a ce za'a kirkiro wa makafi wayoyinsu na dabam. "Irin wadannan wayoyin yawanci ba sa iya yin komai da komai da sauran wayoyi ke yi. Ina ganin hakan kamar raini ne domin kuwa muna da basirar da zamu iya amfani da wayoyin yau da kullum matukar a ka dora musu manhajojin da za su ba makafi damar amfani da su. Kuma wannan yafi bamu damar a dama da mu."

Koda yake karkatar da tunanin kamfanonin wayar salula izuwa samar da manhajojin da makafi za su iya amfani da su babban kalubale ne, makafi da yawa na ganin wannan na daya daga cikin abubuwan da ya kamata su sa a gaba.

Ni kuwa, zan so a ce akwai wata manhajar salula da za ta yi min jagora wurin ziyarar nunin rayuwa cikin makanta. Zan so a ce masu shirya nunin za su yi tunanin samar da wannan manhaja nan gaba. Amma abinda yafi ba ni mamaki shi ne barin wurin nunin. Domin kuwa bayan kwashe sa'o'i a cikin duhu tare da kara saitin ji na, abubuwan da idona ke gani bayan na fito cikin haske sai su ka yi min yawa har sai da na runtse idanuna lokacin da nake komawa gida. A sannan ne na fahimci irin tsananin dogaron da mafi yawanmu muka yi akan gani - da kuma irin yadda rayuwa za ta iya yin armashi ba tare da ganin ba.

Nunin rayuwa cikin makanta mai taken Dialogue in the Dark da ake gabatarwa a Isra'ila na da burin kyautata alaka tsakanin mutane masu ido da kuma makafi. Wakiliyar BBC Tiffanie Wen ta ziyarci cibiyar da ake nunin domin koyon hanyoyin da kwakwalwa kan sauya domin rayuwa ba idanu.

Na san ba ko digon haske, amma duk da haka na shiga lalube cikin bakin duhu saboda sabo da yi. A lokacin da nake tattakawa a hankali cikin dakin da ke shimfide da darduma, tare da dogara sandata irin yadda jagoranmu ya koya min minti guda da ya wuce, ina iya jin saututtukan tsuntsaye, da motsin iska na karkada ganyaye tare kuma da kwararar korama a kusa da ni. Bayan da na yi tuntube da dokin kofa, sai nai sallama da darduma na fito wani fili mai kwazazzabo. Wata kakkarfar iska ta fara bugun fuskata yayin da saututtukan daji su ka kewaye ni ta ko'ina.

"To yara! Yanzu mun shigo daji. Me ku ke iya ganowa a nan?" in ji jagoranmu, Meair Mattityahu, dan shekaru 45, wanda ya makance jim kadan bayan haihuwarsa. "Na gano bishiya!" in ji wata yarinya 'yar shekara 11 wacce ta zo tare da iyayenta daga New York. Ni dai ina can sun bar ni a baya, ina laluben hanya. To kuma tun da na ji cewa akwai bishiyu a wurin sai na shiga fargabar in na kara taki daya zan iya karo da bishiya. Wannan dai shi ne daki na farko cikin bakwai na cibiyar nunin rayuwa cikin makanta da ake gudanarwa a gidan adana kayan tarihi na Holon da ke kasar Isra'ila.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta kiyasta cewa akwai makafi miliyan 38 a fadin duniya, da kuma karin mutane miliyan 110 da ba sa gani sosai kuma su ke fuskantar barazanar makancewa. Manufar wannan nunin dai, wanda aka kirkira a Jamus a 1988, kuma ake yadawa zuwa kasashe da dama, ita ce kyautata fahimta tsakanin masu gani da makafi, ta hanyar bai wa maziyarta damar dandana yadda rayuwar makafi ta ke. Mattityahu ya ce wasu maziyartan kan firgice, su fara ihu kamar ba za'a iya jin su a cikin duhu ba tare da sun daga murya ba. Wasu kuma su kan kyalkyale da dariya. An ma taba samun wanda ya sume. Ya ce "wasu mutane su kan rude su kasa gane dama da hagu. Idan na ce musu su yi amfani da hannun hagu domin su lalubo bango, sai su kasa."

A cikin ziyarar ta minti 90 dai, mun shiga kwalekwale, mun kewaya wani gida, mun yi tafiya a kan titi, mun sayi kayan marmari a shago, sannan kuma mun sayi lemon kwalba a kanti, duk a cikin duhu dundum! Duk da yake ziyarar na da firgitarwa da farko, lallai ta na da wayarwa. Bayan kimanin rabin sa'a da farawa, sai ji na, na kunne da na tabawa su ka karu. Sai lalube cikin duhun ya fara sauki a lokacin da na ci gaba da kutsawa daga daki zuwa daki.

An shirya kwakwalenmu ne ta yadda za su yi cikakken amfani da duk abinda aka ba su. Ga masu idanu, bangaren kwakwalwar dake lura da gani yafi bangarorin da ke lura da ji da tabawa yawan jijiyoyi, abinda ke sa idanunsu gane wurararen da su ke cikin hanzari. Ga wadanda ba sa gani kuwa, sai jijiyoyin su tattara a bangaren kwakwalwa mai kula da ji da tabawa. Bincike akan dangantakar makanta da kwakwalwa, ya gano cewa makanta kan sauya yadda kwakwalwa ke aiki, inda masana su ka gano cewa mutanen da suka makance kan yi amfani da bangaren kula da gani na kwakwalensu wurin sarrafa ji da tabawa, kamar yadda wani mai bincike a jami'ar McGill, Patrice Voss ya bayyana.

Binciken na Voss ya kuma nuna cewa mutanen da su ka makance tun da kuruciya sun fi masu gani iya gano ta inda sauti ke fitowa musamman idan ta bangaren kunne daya ne. Haka kuma wasu masanan sun gano cewa makafi sun fi masu gani gane muryoyi da kuma hadda.

Koda yake mutanen da su ka makance da girmansu ma, kan samu sauyi a yadda kwakwalwarsu ke aiki, Voss ya ce wadanda su ka makance tun da kuruciya sun fi samun sauyin aikin bangaren gani fiye da wanda su ka makance da girmansu.

Ya ce "Kwakwalwa ma ta na tsufa. Don haka muna girma ikonta na sauya tsarin aikin sassanta na raguwa. Amma wanda ya makance tun da wuri, kwakwalwarsa kan samu kwarewar sarrafa abubuwan da basu shafi gani ba a sassan da ya kamata su sarrafa ganin."

Mutane kuma kan bada misali da Ray Charles da Stevie Wonder a matsayin makafin da su ka yi matukar kwarewa a fannin kida. To akwai binciken da ya nuna cewa makanta kan kara karfin ji da kuma sarrafa sauti. Ga misali, wani bincike da aka yi a 2004 ya gano cewa makada makafi sun zarta takwarorinsu masu ido kwarewa wurin nakaltar sautin kida tare da maimaita shi ba tare da kuskure ba.

A cewar Mattityhau "Mutane da yawa na daukar rashin gani a matsayin mutuwar tsaye. Amma ni a wuri na ji yafi gani amfani. Ba na iya gani, amma ina iya ji, in rike magana, in isar da sako, in yi tafiya - wato dai ina cikakkiyar rayuwa tamkar kowa."

Mattityahu ya ce baya ga fahimtar yadda rayuwar makafi take kuma, daya daga cikin manufar shirya nunin, shi ne maziyarta su rika kimanta makafi bisa kwarewarsu ba wai su rika kallonsu a matsayin nakasassu ba. Ya ce "Zan so a ce rayuwata a waje za ta yi daidai da ta wurin nunin nan. Babu wanda ya taba ganina cikinku kafin zuwa nan, amma duk kun amince da jagorancina. In da kuwa a cikin haske muka hadu, ba wani daga cikinku da zai tunanin neman taimako daga makaho. Na kan tambayi kai na ko me yasa haka? Yadda na iya jagorantarku a cikin duhu, zan iya jagorantarku a cikin haske."

Ba wai rayuwar zahiri ce kawai ke zama kalubale ga makafi ba, har ma da duniyar fasahar zamani. Ko yaya makafi ke amfani da fasahar zamani?

Ba mamaki ba ku sani ba, amma mafi yawan wayoyin komai-da-ruwanka da kwamfutoci su na da tsarin da ke bada damar a yi amfani da su ba tare da gani ba. Wayoyin Android suna da manhajar da za ta sarrafa su ta hanyar magana irinsu Talk Back da Vlingo ko kuma ta hanyar tabawa kamar Explore by touch. Wayoyin Apple kuma su na da manhajar VoiceOver.

Haka kuma, akwai manhajojin LookTel Money Reader da Color Identifier, wanda ke amfani da kyamarar wayar salula wurin gane takardun kudi da kuma launuka. Akwai kuma Ray App mai saukaka tsarin wayoyin Android domin amfanin makafi.

Na yi amfani da wayar iPhone bisa tsarin VoiceOver na tsawon mako guda. Sai dai nan take na rikice saboda amfani da waya bisa manhajar VoiceOver ya sha bamban da yadda na saba. Misali, shafar fuskar waya daga sama zuwa kasa da dan yatsa daya, ba ya sa shafin da ake karantawa ya yi sama, sai dai in an yi amfani da yatsu biyu. Don haka sai na yanke shawarar neman taimakon kwararru.

Liran Frank injiniyan kwamfuta ne kafin ya makance sanadiyyar ciwon ido. Ya ce "Ba fasahar taimako kadai makafi ke amfani da ita a wayoyin salula ba. Muna amfani da duk manhajojin da masu gani ke amfani da su irin su Netflix, Google Maps, Moovit, Whasapp, da sauransu. Amfani da VoiceOver na da matukar sauki da zarar ka gane yadda ya ke aiki. Ina amfani da wayata kamar yadda mai gani ke amfani da ta sa."

Jan labulen fasaha

Bayan kwarya-kwaryar darasi a wurin Frank, wanda ke koyawa makafi yadda za su yi amfani da wayoyin komai-da-ruwanka da kuma na'urorin kwamfuta tare da samar da darussan sauraro na dabarun amfani da VoiceOver, sai na fara amfani da manhajar VoiceOver a wayata tare da jan labulen fasaha wanda ya mayar da fuskar wayar dundum kamar a kashe ta ke.

Cikin yini guda, sai hannuna ya fada kan amfani da wayar da take dundum. Saututtuka daban-daban da wayar ke bayarwa su na taimakawa kwarai wurin sarrafata. Misali akwai sautin da ke nuna ka gama goge rubutun da ka ke gogewa, akwai mai nuna ka bude abinda ka ke son budewa ko kuma ka fita daga kan iyakar fuskar wayar. Ana kuma sarrafa wayar ne ta hanyar shafarta da 'yan 'yatsu daga daya zuwa hudu ta sigogi dabam-daban.

Misali, kwankwasar fuskar wayar sau biyu na tsayar da karatu, kamar idan wayar na karanta wani sako da ka riga ka saurara. Haka kuma idan ka mintsini fuskar wayar sai ta baka jerin abubuwan da zaka iya yi cikin manhajar da ka bude kamar lissafo sauran shafukan da ke cikin gidan da ka shiga ko kuma karanto maka bakaken rubutun da ka yi daya bayan daya domin tabbatar da cewa ka rubuta kalmomin daidai.

Ta kai ina iya duba sakonnin i-mel, aikawa da sauraron rubutattun sakonni, bude shafukan intanet, kiran waya da kuma sauraron wakoki. Bayan kuma na saurari darasin Frank, ina iya amfani da Google Maps.

Hakan ba ya nufin ban fuskanci matsaloli ba. Baya ga lokacin da na dauka wurin koyon amfani da manhajar, akan samu kalubale duk lokacin da aka sake inganta wata sabuwar manhajar wayar salula. Yayinda ake tsara wasu manhajojin domin su dace da tsarin VoiceOver, wadansu manhajojin kan dace ne ba tare da sanin masu kirkirarsu ba. Frank ya ce akwai wata manhajar motocin sufuri da ya ke amfani da ita akan tsarin VoiceOver amma da aka kara ingantata sai ya zama an dora ma ta abubuwan da VoiceOver ba zai iya dauka ba. "Muka hada kai mu ka rubuta mu su wasika. Sai su ka aiko mana cewa ba su taba sanin makafi na iya amfani da manhajar ta su ba amma tun da haka ne za su so makafi su ci gaba da amfani da sabuwar manhajar. Don haka su ka hada kai da mu, mu ka dauko wani mai shirya manhajar salula ya yi wa sabuwar manhajar ta su tsarin da za ta iya ci gaba da aiki a VoiceOver."

Frank na ganin zai fi kyau a mai da hankali wurin tsara manhajojin da masu gani ke amfani da su ta yadda makafi ma za su iya amfani da su maimakon a ce za'a kirkiro wa makafi wayoyinsu na dabam. "Irin wadannan wayoyin yawanci ba sa iya yin komai da komai da sauran wayoyi ke yi. Ina ganin hakan kamar raini ne domin kuwa muna da basirar da zamu iya amfani da wayoyin yau da kullum matukar a ka dora musu manhajojin da za su ba makafi damar amfani da su. Kuma wannan yafi bamu damar a dama da mu."

Koda yake karkatar da tunanin kamfanonin wayar salula izuwa samar da manhajojin da makafi za su iya amfani da su babban kalubale ne, makafi da yawa na ganin wannan na daya daga cikin abubuwan da ya kamata su sa a gaba.

Ni kuwa, zan so a ce akwai wata manhajar salula da za ta yi min jagora wurin ziyarar nunin rayuwa cikin makanta. Zan so a ce masu shirya nunin za su yi tunanin samar da wannan manhaja nan gaba. Amma abinda yafi ba ni mamaki shi ne barin wurin nunin. Domin kuwa bayan kwashe sa'o'i a cikin duhu tare da kara saitin ji na, abubuwan da idona ke gani bayan na fito cikin haske sai su ka yi min yawa har sai da na runtse idanuna lokacin da nake komawa gida. A sannan ne na fahimci irin tsananin dogaron da mafi yawanmu muka yi akan gani - da kuma irin yadda rayuwa za ta iya yin armashi ba tare da ganin ba.

Idan kana so ka karanta wannan a cikin harshen Ingilshi latsa nan. How it feels to live in darkness