Gagarumar dalar da aka boye cikin tsauni

Hakkin mallakar hoto wikimedia

Dalar Cholula ta kere wa babbar dalar da ke Giza, amma turawan mulkin mallaka na Spaniya ba su lura da ita ba. Me ya sa haka?

Lokacin da Hernan Cortez ya jagoranci dubun dubatar dakarun Spaniya zuwa babban birnin Cholula, bayan fama da baraden mayaka da yunwa da kuma cututtuka, ya yi zaton zai fuskanci gagarumar rundunar yaki.

Sai dai kuma birnin, cibiyar addini ne. Maimakon makamai, mazaunansa dakunan ibada su ka tanada; an ce sun gina dalar bauta adadin kwanakin shekara. Don haka sun yi Imani allolinsu za su iya kare su daga kowanne sharri.

A nan kam sun tafka kuskure. Rundunar ta sojojin Spaniya ta mamaye birnin tare da wawashe dakunan bautarsu da kuma rushe dalolin da su ka gina. Cikin sa'o'i uku, Spaniyawa sun hallaka mutane 3,000. 12 ga Oktoban 1519 mummunar rana ce a tarihin Cholula domin kuwa sai da aka kashe kaso 10% na mazaunan birnin.

Daga nan ne Spaniyawa su ka karbe birnin Cholula (wanda yanzu ya ke cikin Mexico), inda su ka yi na su gine-ginen har birnin ya zama ya na da coci-coci adadin kwanakin shekara. Abu na karshe da su ka yi - wanda ke alamta Kiristanci ya yi nasara a birnin - shi ne gina cocin Iglesia de Nuestra SeƱora de los Remediosa, a bisa abinda su ka yi tsammanin wani babban tudu ne.

Hakkin mallakar hoto Getty

Sai dai ba haka lamarin ya ke ba. Karkashin mitsitsin cocin, a boye a cikin turbaya da ciyayi, akwai wani tsohon ginin dala mai matukar girman gaske. Babbar Dalar Cholula mai fadin mita 450 da tsayin mita 66 ta kai girman kwamin ninkaya irin wanda ake gasar Olympics a ciki har guda tara.

Boyayyar dalar Cholula, wacce mafi yawan mutane ba su ma san da zamanta ba, ita ce ginanniyar dalar da tafi kowacce girma a duniya, inda ta nunka Babbar Dalar da ke Giza sau hudu a fadi, kuma sau biyu a tsayi.

Kai bar ta dala - babu wani gini a duniya, da aka yi a kowanne irin zamani, har yau din nan da ya kai girmanta. Mutanen garin kan kira ta Tlachihualtepetl ("tsauni ginin-mutum"). Sakamakon cocin da aka gina a samanta, kuma ita ce ginin da aka fi dadewa ana amfani da shi a gaba daya nahiyar Amurka.

Ba wanda ya san da zaman dalar, sai da aka fara ginin asibitin mahaukata a 1910. Ko a lokacin da Cortez da dakarunsa suka isa Cholula, dalar tafi shekaru dubu guda kuma ciyayi sun rufe ta ruf.

Da aka fara hakarta, an ga abubuwan tashin hankali ciki har da kawunan yaran da aka sassare.

Menene asalin dalar? Kuma me ya sa ta dade a boye?

Hakkin mallakar hoto Getty

Duk da wannan makeken girman na ta, babu tartibin bayanin asalin dalar. Ana jin dai an fara gina ta shekaru 300 kafin haihuwar Annabi Isa; wa ya gina ta? Nan fa daya! Mutanen Cholula na cewa wani katon mutum ne ya gina ta. Abinda zai fi karbuwa shi ne, mazaunan birnin a shekaru aru-aru sun fito ne daga sassa daban-daban. "Da alamu akwai kabilu da yawa, tare da yawan kaura," in ji David Carballo, mai nazarin kayayyakin mutan da a jami'ar Boston da ke Massachusetts.

Ko ma dai su waye su ka gina dalar, da alama su na da tarin kudi. Cholula na kan tsaunukan Mexico ne kuma cibiyar cinikayya ce tun shekaru masu nisa, inda ta zama zango tsakanin daulolin Tolteca-Chichimeca da ke arewa da Maya da ke kudu.

Cortez ya kira Cholula "birnin da yafi kowanne kawai a wajen kasar Spaniya". A lokacin da ya isa birnin, shi ne na biyu a girma a daular Aztec, ko da yake dauloli dabam-daban sun mulki birnin a baya.

Wani kuma abin karin mamaki game da dalar shi ne ba gini daya bane kadai. Dalar guda shida ce; wata a cikin wata, inda 'ya'ya ke kara gini akan abinda su ka tarar na iyayensu.

"Sun yi kokarin su ga sun kare gine-ginen baya inda su ke dora na su ba tare da rushe wancan ba. Wannan sabon abu ne a tarihin gini a duniya, wanda ke nuna yadda su ke danganta kansu da tarihin baya," in ji Carballo.

Hakkin mallakar hoto wikimedia

An ce wai lokacin da mutanen birnin su ka ji labarin dakarun Spaniya sun musu tsinke, sai su ka lullube dalar da turbaya. Sai dai masana na ganin, kasa ta rufe ginin ne kadan da kadan. Saboda kuwa, abin mamaki shi ne, wannan dalar da tafi kowacce girma a duniya, da tabo aka yi ta.

Tubalin da aka yi ginin na tabo ne da aka cakuda da harawa, sannan aka gasa a rana. A lokacin ginin dalar, an shafa wa tubalan waje turbaya domin su yi santsi su yi luwai-luwai. Haka kuma an yi wa dalar ado da kwari jajaye, da bakake da kuma ruwan dorawa.

A busassun kasashe, tubulin kasa na dadewa sosai - inda ya kan kai dubunnan shekaru. A kasar Mexico, mai laima kuwa, ginin na tubulin tabo sai ya zamo mafakar ciyayi. "A cikin karni na 7 zuwa na 8 na kalandar Kirista ne aka daina amfani da dalar. Mutanen Cholula sai suka gina wata sabuwar dalar a kusa da wurin, wacce dakarun Spaniya su ka rusa," in ji Carballo.

Haka kuma dalar ta yi dacen matsuguni; domin kuwa an gina ta ne a cikin kwarin da ke tsakanin wasu manyan tsaunuka.

Yanzu dai mutanen birnin sun sake tono dalarsu, wacce akan ziyarce ta ta hanyar amfani da ramuka masu nisan fiye da mil biyar, wadanda aka haka a farkon karni na 20.

Kimanin shekaru 500 bayan mamayar dakarun mulkin mallaka, yanzu birnin na fama da wasu maziyartan: 'yan yawon bude ido.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The giant pyramid hidden inside a mountain.