Amfanin iya harsuna biyu

Mafi yawan mutanen duniya na iya magana da harshe fiye da daya, abinda ke nuna an gina kwakwalwar mutane kan magana da harsuna da dama. Idan haka ne, wadanda ke amfani da harshe daya tak sun yi asara ke nan?

A wani shagon shan kofi da ke kudancin London, wasu leburori na hira cikin nishadi. Lokaci-lokaci su kan kyalkyale da dariya. Da gani dai hirar mata su ke, amma me su ke cewa ban sani ba. Hirar ta su dai gwanin sha’awa ga mutum mai shisshigi irina. Sai dai ban iya yarensu ba.

Tsabar cusa kai ta sa na katse musu zancen na tambaye su wane yare su ke yi? Cikin murmushi sai su ka karba da harshen Ingilishi cewa su ‘yan Afrika ta Kudu ne kuma su na hira ne da harshen Xhosa. A garinsu, Johannesburg, yawancin mutane na jin akalla harsuna biyar, in ji daya daga cikinsu, Theo Morris. Misali, mahaifiyar Theo ‘yar kabilar Sotho ce, babansa Zulu, ya koyi Xhosa da Ndebele daga abokai da makwabta, yayinda ya koyi Ingilishi da Afrikaaans a makaranta. Ya kara da cewa; “Kafin na zo nan na zauna a Jamus, don haka na koyi Jamusanci.”

Amma dai ya sha wuya kafin iya wadannan harsunan ko? Cikin dariya ya ce; “Sam. Ba wata wuya.”

Da gaskiyarsa. Fiye da rabin mutanen duniya su na jin akalla harsuna biyu. Kasashe da dama na amfani da fiye da yare daya a matsayin harshen kasa – Afirka ta Kudu na amfani da 11. Ga shi kuma ana sa ran mutane su iya magana, karatu, da rubutu da daya daga cikin manyan harsunan duniya kamar su Ingilishi, Sinacni, Indiyanci, Spaniyanci da Larabci. Don haka masu amfani da harshe daya tak, kamar mafi yawan masu amfani da Ingilishi a matsayin harshen asali, ‘yan tsiraru ne, kuma watakila ma su na tafka asara.

An gano cewa kwarewa a harsuna da dama na da dimbin alfanu ta fuskar zamantakewa da halayya da samun damammaki a rayuwa. Haka kuma masu bincike na gano cewa amfani da harsuna fiye da guda na taimakawa ta fuskar lafiya musamman saurin farfadowa daga bugun jinni da kuma dakile saurin kamuwa da gigin tsufa.

Shin dama an yi kwakwalwar mutane ne ta yadda za ta sarrafa harsuna fiye da daya, kuma wanda ke amfani da harshe daya tak na sakaci da damarsa ke nan?

A wannan duniyar da harsuna ke bacewa fiye da kowanne lokaci a baya – akalla duk mako biyu harshe daya na bacewa, wato nan da karshen karni rabin harsunan duniya za su bace – me zai faru idan baki daya harsuna su ka bace ya zama duk duniya na amfani da harshe daya tilo?

Yanzu haka ina zaune a wani dakin gwaji, sanye da bututun sauraron magana a kunnena, ina kallon hotunan dusar kankara a kwamfuta. Duk lokacin da samfurin dusar kankara biyu su ka bayyana a kwamfutar, akan yi min bayani ta bututun maganar da ke kunne na.

Iyakacin abinda zan yi shi ne in nuna wannan daga cikin samfurin dusar kankarar da ake bayyanawa. Matsalar daya ce; bayanin na zuwa ne cikin wani kirkirarren harshe mai suna Syntaflake.

Wannan dai wani bangare ne na gwajin da Panos Athanasopoulos, dan kasar Girka mai tsanani kaunar harsuna ke gudanarwa. Farfesan nazarin yadda kwakwalwa ke sarrafa harshe tare da fahimtar magana cikin harsuna biyu a jami’ar Lancaster, shi ne kan gaba wurin sabon binciken da ake gudanarwa kan kwakwalwar masu amfani da harsuna biyu.

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwajin da ake min na da matukar wuya. Abinda aka saba shi ne, idan ka na amfani da bakon harshe, akwai alamomin da zasu taimaka wurin gane ma’anar me ake cewa. Misali, mai maganar zai iya nuna dusar kankarar a lokacin da ya ke magana, ko ya yi amfani da ‘yan yatsunsa wurin nuna adadi, girma, ko kankantar abinda ya ke zance a kai. A nan, babu wadannan alamomin. Kasancewar yaren kirkirarre ne, babu yadda zan yi in kwatanta shi da wasu harsuanan da na iya.

Bayan wani lokaci, sai na ji na fara gane yadda ake jeranta kalmomi a hada jimla a cikin sautin. Don haka sai na dauko biro da takarda na fara rubuta abinda na ji don ganin ko zan iya fahimtar yaren. Amma dai har aka gama ban fahimci komai ba.

Sai kuma na kara sa wurin Athanasopoulos domin tattaunawa da shi kafin ma’aikatansa su gama tantance sakamakon gwajin da su ka yi min.

Cikin takaici, na bayyana masa wahalar da na fuska wurin koyar sabon harshe. Sai dai kuma da alama a nan na kwafsa: “Wadanda su ka fi yin kokari a wannan jarrabawar su ne wadanda ba su damu da yin nasara ba, su dai kawai su gama su huta.

Dalibai da malamai su ne su ka fi shan kasa,” in ji shi.

“Ba zai yiwu ki fahimci ka’idojin harshe tare da fahimtar abinda ake gaya miki cikin dan kankanin lokaci ba. Amma kwakwalwarki za ta iya cankar ma’anar idan ki ka kyaleta. Shi ya sa kananan yara su ka fi yin nasara a gwajin.”

Kakanninmu dai sun fara furta magana ne kusan shekaru dubu 250 da su ka wuce, tun bayan da su ka koyi tsaya wa a kan kafafuwa biyu, abinda ya dauke wa kirazansu nauyi, ya bada damar sarrafa numfashi da fitar da ingantaccen sauti. Daga lokacinda mutane su ka koyi magana kuwa, samar da wani sabon yare bai zo da wahala ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Za a iya kwatanta tarihin samuwar harsuna da tarihin samuwar halittu, sai dai yayinda sauyin yanayi ke tasiri wurin samuwar halittu, sauyin tsarin zamantakewa shi ne ke tasiri wurin samuwar harsuna. Bayan dan lokaci, sai rukunin mutane dabam-daban su ka fara amfani da harsuna da daban. Amma bukatar sadarwa da wasu – saboda ciniki, tafiya, da sauransu – sai ta tilastawa mutane magana da harsuna fiye da daya.

Muna iya fahimtar yadda amfani da harsuna da yawa ya yadu cikin al’ummomin da can idan mu ka yi la’akari da tsirarin kabilu mayawatan da su ka rage. “Idan ki ka kalli kabilun mayawatan da su ka rage a yanzu, yawancinsu su na jin harsuna da yawa,” in ji Thomas Bak, mai nazari kan yadda kwakwalwa ke fahimtar abubuwa a jami’ar Edinburgh. “Dokar ita ce; dole ne mutum ya yi aure a a wata kabilar dabam. Don haka kowanne yaro zai taso tare da uwa da uban da suke da yaruka mabambanta.”

A cikin kabilun asali na kasar Australia, inda har yanzu su ke da harsuna fiye da 130, kusan kowa ya na jin harshe fiye da daya. “Ku na tafe ku na hirarku da mutum, da kun tsallaka wata ‘yar koramar sai ka ga abokin hirarka ya sauya harshe,” in ji Bak.

Wannan kuma haka ya ke a wasu sassan na duniya ma. Misali, idan ka shiga jirgin kasa a Belgium, a Liege za ka ji ana sanarwa da Faransanci, in ka shiga Loewen sai harshen ya juye zuwa Dutch, a Brussels kuma sai a koma Faransanci.

Wannan dangantaka tsakanin harshe da al’ada da muhalli ita ce ta sa Athanasopoulos ya kirkiro sabon harshe domin gwajin samfurin dusar kankara. Ya bayyana cewa daya daga cikin manufofin bincikensa shi ne rarrabe tsakanin harshe da kuma al’adar da ta dabaibaye shi.

Hakkin mallakar hoto Getty

Saboda harshe ya na da dangantaka da al’ada shi ya sa kuma ya ke da alaka da siyasa. Samar kasashen Turai da tsarin mulkin mallaka a karnin na 19 sai su ka sa amfani da bakon harshe ya zamo tamkar rashin kishin kasa.

Wannan shi ne asalin ra’ayin nan da ya yadu musamman a Burtaniya da Amurka cewa tarbiyantar da yara kan amfani da harsuna biyu zai yi musu illa a kansu kuma zai iya jawo matsala cikin al’umma.

A baya ma an sha gargadin cewa yaran da ke amfani da harsuna biyu za su tashi cikin rudani, da dakikanci, da raina kansu, har ma da yiwuwar su kamu da tabin hankali. Wannan ra’ayi ya yi tasiri har zuwa shekarun baya bayan nan, abinda ya sa mutanen da su ka yi kaura su ka ki koya wa ‘ya’yansu harshensu na asali.

Hakan kuwa na faruwa ne duk da gwajin da aka yi a 1962 wanda ya nuna cewa yaran da ke amfani da harsuna biyu sun fi ma su amfani da harshe daya kokari da fahimtar karatu.

Sai dai binciken da masu nazarin kwakwalwa da halayyar dan Adam da fidar harshe su ka gudanar cikin shekaru goman da su ka wuce, ta hanyar amfani da na’urorin daukar hoton kwakwalwa na zamani sun nuna cewa masu amfani da harshe biyu na da karfin fahimta fiye da masu harshe daya. Wannan kuwa ya samu asali daga yadda kwakwalwa ke koyon yin ayyuka da yawa a lokaci guda.

Rabuwar hankali

Idan ka tambaye ni da Ingilishi, abincin da na fi so, sai hankalina ya tafi London ina fara tunanin irin abincin da na kan samu a can. Amma idan ka tambaye ni da Faransanci sai hankalina ya tafi Paris, inda irin abincin da zan zaba ya bambanta da na London. Wato ke nan tambaya daya na da amsoshi dabam-daban daidai da harshen da ka tambaye ni da shi.

Gano cewa dabi’ar mutane kan sauya daidai da harshen da su ke amfani da shi, ilimi ne mai matukar amfani.

Athanasopoulos da abokan aikinsa sun dade su na nazari kan yadda amfani da harshe ke sauya tunanin mutane. A wani gwaji da su ka yi, sun nuna wa masu jin Ingilishi da Jamusanci hotunan bidiyo na mutane masu motsi, kamar wata mata da ta tunkari motarta da kuma wani mutum da ke tuka keke zuwa kanti.

Masu jin Ingilishi kan mai da hankalinsu kan aikin, inda su kan ce “mace na tafiya” ko “mutum na tuka keke”. Masu jin Jamusanci kuwa su kan hada da manufar aikin inda su kan ce “mace na tafiya zuwa motarta” ko “mutum na tuka keke zuwa kanti”.

Hakkin mallakar hoto g

Daya daga cikin abubuwan da ke kawo wannan bambancin shi ne nahawun kowanne harshe, kamar yadda Athanasopoulos ya bayyana. Harshen Ingilishi ya na da kalmomin ayyuka da ke karuwa da –ing, abinda babu a Jamusanci. Wannan ya sa masu jin Ingilishi ba sa danganta aiki da manufarsa kamar takwarorinsu masu jin Jamusanci.

Amma da ya gwada masu jin harsunan biyu gaba daya domin gano ko za su mai da hankali kan aikin ne ko kuma makasudinsa, sai ya gano cewa wannan ya danganta da kasar da su ke ciki; a Ingila, sun a mai da hankali ne kan aiki, ko da wane yare su ke magana kuwa, amma a Jamus su na mai da hankali ne kan manufar. Wannan ya nuna yadda al’ada da harshe ke cudewa wurin yin tasiri kan tunanin mutane.

A shekarun 1960, daya daga cikin jagororin nazarin dangantakar halayyar dan Adam da harshe, Susan Ervin-Tripp, ta gwada matan da ke jin harsunan Japananci da Ingilshi, inda ta neme su da su kammala wasu jimloli.

Ta gano cewa harshen da matan su ka yi amfani da shi na da tasiri kan yadda su ke karasa jimlolin. Ga misali, “Idan abin da na ke so ya saba da abinda dangina ke so…” sai su karasa da Japananci “wannan lokaci ne na bakin ciki”; amma da Ingilishi sai su karasa da “Sai in yi abinda na ke so”. Wani misalin kuma shi ne “Ya kamata kawayen kwarai…” da Japananci su ka karasa da “su taimaki juna” da Ingilishi kuma “su gaya wa juna gaskiya”.

Daga nan ne, Ervin-Tripp ta gano cewa dan Adam ya na tunani ne ta cikin yare, kuma masu yare biyu su na tunani dabam-daban da kowane yare – wannan muhimmiyar magana ce wadda nazarce-nazarcen da aka yi daga baya su ka tabbatar.

Haka kuma masu amfani da harsuna biyu da dama kan ce su kan ji su kamar wasu mutanen dabam a lokacin da su ke magana da harshe na dabam.

Sai dai kuma a ko da yaushe wadannan tsarin tunanin mabambanta na kara wa da junansu, a yayin da kwakwalwar mai jin harshe biyu ke kokarin ware da wane yaren za ta yi aiki.

A wani gwaji da Athanasopoulos ya gudanar kan masu jin Ingilishi da Jamusanci, ya kan sa su yi kidaya a bayyane da daya daga cikin harsunan biyu a lokacin da ya ke nuna musu hotunan bidiyo.

Wannan kidayar kan toshe tasirin daya harshen da su ke ji, don haka su kan wassafa abinda su ke gani cikin bidiyon bisa la’akari da aikin ko manufar aikin ta mahangar harshen da su ka yi kidayar a cikinsa.

Hakkin mallakar hoto Getty

To me hakan ke nufi? Ta tabbata ke nan tunani na bambanta bisa bambancin yare? Wannan shi ne abinda gwajin wassafa dusar kankara ke kokarin gano wa. Ina dai dan jin dar-dar bisa abinda gwajin zai bayyana game da ni, amma Athanasopoulos ya tabbatar min da cewa sakamakona ya yi daidai da na mutanen da ya gwada a baya.

Domin fahimtar tasirin da yaren Syntaflake ya yi wa kwakwalwata, an yi min jarrabawa kafin, da bayan, gwajin tantance samfurin dusar kankarar. Amfaninsu shi ne yi wa kwakwalwata atisaye domin ta kara basirar fahimtar sabon harshen.

A cikin jarrabawar a kan rubuta sunayen launuka da haruffa masu launuka dabam (misali “shudi” a rubuta da jajayen haruffa). Abinda ake so, shi ne ka fadi launin haruffan, to amma abin da wuya, saboda muna riga karanta rubutu kafin fahimtar launi. Don haka sai ka dage kwarai kafin ka danne abinda ka karanta ka fadi abinda ka gani.

Bangaren kwakwalwar da ke lura da wannan aikin ana kiransa (ACC), wanda ke gaban goshin kwakwalwa. Wannan bangaren shi ne ke ba mu damar mai da hankali kan wani aiki mu toshe wasu tunaninka ba tare da mun rude ba.

Nazarurruka da dama cikin shekaru goman da su ka wuce sun nuna cewa masu jin harsuna biyu sun fi masu jin harshe daya tak kokari wurin shirya magana da kuma fahimtar mutane. Ana ganin hakan ya biyo bayan kwarewar da bangaren ACC na kwakwalwarsu ya samu ne sanadiyyar daidaitawa tsakanin harsuna biyu.

Tsokar kwakwalwa

A cewar manazarcin yadda kwakwalwa ke fahimtar abubuwa, Jubin Abutalebi, da ke jami’ar San Raffaele a Milan, ana iya gane masu jin harshe daya da masu jin harsuna biyu ta hanyar kallon hotunan kwakwalwarsu. Ya ce: “Bangaren ACC na kwakwalwar masu jin harsuna biyu yafi na masu jin harshe daya girma, saboda yawan atisayen da su ke masa.”

Misali asalin yaren Thomas Bak shi ne harshen Poland, ya na Spananci da matarsa, kuma su na zaune a Edinburgh don haka ya na jin Ingilishi. Ya ce: “Idan ina yi wa matata Ingilishi, na kan tsarma kalmomin Spananci, amma ban taba kuskuren yi mata harshen Poland ba.

Kuma idan ina yi wa surukata magana da Spananci ba na kuskuren cusa kalmomin Ingilishi saboda na san ba ta ji. Ba wai kuma tsaya na ke in yi wani dogon tunani ba, sashin ACC na kwakwalwata ne lura da wannan lamari.”

Hakika wannan wata babbar ni’ima ce ga masu jin harsuna biyu amma babbar ni’imar ita ce: jin harsuna biyu na dakile gigin tsufa.

Masaniyar dangantakar harshe da kwakwalwa Ellen Bialystok ce ta gano hakan a jami’ar York da ke Toronto lokacin da ta kwatanta tsakanin tsofaffi masu jin harshe daya tak da masu jin harsuna biyu.

Ta ce: “Masu jin harshe daya tak kan riga masu jin harsuna biyu fara gigin tsufa da kusan shekaru hudu zuwa biyar.”

Haka kuma jin harsuna biyu kan bada kariya ga wadanda su ka samu rauni a kwakwalwa. A wani bincike na baya bayan nan da a ka gudanar kan mutane 600 da su ka warke daga cutar bugun zuciya a India, Bak ya gano cewa masu jin harsuna biyu sun fi masu jin harshe daya tak saurin farfadowa.

Ko da yake wasu masanan sun musanta wadannan alfanun na iya yaruka da dama, Bak ya yi musu martani da cewa sun tafka kurakurai a hanyoyin da su ka bi wurin nazarinsu. Haka kuma babu daya a cikinsu da ya ce hakan na da illa. Wato dai akalla ko babu karin lafiya, akwai karuwar zamantakewa.

Hakkin mallakar hoto Getty

To ko ta wacce hanya za a iya amfani da wannan ilimi?

Hanya ta farko ita ce a koya wa yara harsuna da yawa. A kasashe da yawa na duniya, dama abinda ake yi ke nan: misali yaran India na koyon karatu a yaren da ba shi su ke yi a gida ba.

Amma a kasashen da ke amfani da Ingilishi, ba a cika samun hakan ba. Amma dai yanzu akwai masu gwadawa, kamar jihar Utah ta Amurka inda ake koyar da yara da harshen Mandarin na China or kuma Spananci.

“Mu kan koyar da su da bakon yare da safe, da yamma kuma mu yi mu su Ingilishi, washe gari kuma sai a juya saboda wasu sun fi koyon karatu da safe, wasu kuma da yamma,” in ji Gregg Roberts, jami’i a ma’aikatar ilimi ta Utah wanda ya ke kula da wannan tsarin.

Ya kuma ce sun gano yaran da ke amfani da harsuna biyu sun fi mai da hankali da fahimtar karatu fiye da masu amfani da harshe daya tak.

A yanzu an fara gwajin wannan tsarin na darasi a harsuna biyu a Ingila. A makarantar sakandaren Bohunt da ke Liphook, Hampshire, hedimasta Neil Strowger ya kaddamar da tsarin koyar da wasu darassun da harshen Mandarin na China.

Strowger ya ce daliban sun kara kokari, kuma sun samu jarin rayuwa tun da yanzu za su iya huldar kasuwanci da sauran kasashen Asiya fiye da masu jin Ingilishi kawai.

To mu kuma da mu ka kammala makaranta an bar mu a tasha ke nan? Amfanin ilimi dai aiki da shi, don haka ga masu son amfanuwa da jin harsuna biyu kuma ba su da damar tattaunawa da masu jin yaren, za su iya yin dabarar kafa dandalin hira da yaren da su ka koya.

Bak ya yi wani binciken gwaji da wasu tsofaffi masu koyon harshen Gaelic a Scotland kuma cikin mako guda da kafa dandalin hirar ya ga kwakwalensu sun fara samun ci gaba. Yanzu dai ya na shirin zai kara zurfafa binciken.

Duk mai son koyon sabon yare dai bai makara ba, kuma zai cimma moriya da yawa, in ji Alex Rawlings wani mutumin Burtaniya wanda ya kware a harsuna 15.

Ya ce: “Kowanne harshe kan bude maka wata sabuwar rayuwa da kuma wata sabuwar hanyar kallon al’amura.” Ya kara da cewa: “Mutane kan ce wai koyon sabon harshe na da wuya idan ka girma amma ina ganin yafi sauki bayan ka haura shekaru takwas. Jariri na daukar shekaru uku kafin ya koyi yare amma babba zai iya cikin watanni.”

Kamar dai yadda bincike ya nuna, iya harsuna biyu zai bai wa kwakwalwarmu damar aiki da kyau har zuwa tsufa don haka ba karamar dabara ba ce ka koyi yadda za ka yi magana, hablar, parler, sprechen, beszel, berbicara, a cikin iya yarukan da za ka iya koya.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The amazing benefits of being bilingual.