Yadda Facebook ya zama makekiyar makabarta

A nan gaba, matattu za su fi rayayyu yawa a Facebook, abinda ke zama wani babban kalubale game da yadda mu ke tunawa da mutuwar wadanda mu ke tare da su.

Washe garin rasuwar gwaggo na, na gano cewa ta rubuta sako, a kundin littafan Shakespeare da ta bani kyauta. “Na san muhimmancin littattafai a wurinka, don haka na baka wannan kyauta. Mai kaunarka koda yaushe, Jackie.”

Wannan ya sa shaukinta ya kama ni har na shiga intanet na budo shafinta na Facebook. Niyyata ita ce in karanta abubuwan da take wallafawa a shafin ina kallon hotonta ina riyawa a raina kamar ita ce ke magana.

Abinda na fara gani shi ne wani sakon bidiyo da danta ya aika dauke da wasu giwaye biyu su na wasa a cikin ruwa, kasancewar gwaggon tawa akwai ta da son giwaye. Kasan wannan kuma sai sakonnin ta’aziyya da dalibanta su ka rubuta. Kasa da wannan kuma sai sanarwar rasuwarta da surukarta ta wallafa.

Daga nan sai na koma sama. A cewar Facebook Gwaggo Jackie ta sami horon koyar da Ingilishi a jami’ar Frostburg, tsohuwar shugabar sashen koyar da Ingilishi ce a hukumar makarantun Baltimore, Maryland kuma ta na rayuwa a garin Baltimore.

Rayuwa kuma? Na tambayi kai na. Ai ta rasu.

Amma idan ka duba shafinta na Facebook ba za ka gane hakan ba, har sai ka bibiya inda aka rubuta sanarwar rasuwarta.

Wato ke nan ta wata fuskar a iya cewa ta na raye amma rayuwar Facebook.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Sai na tuno ranar da ni da ‘yan uwana mu ka kewaye gadon asibitin da Gwaggo Jackie ke kwance tare da wayoyi da aka jona mata da na’urori lokacin ta na kan gargarar ajali har aka zare ranta.

Shaidar fitar ran mutum wani abu ne mai tayar da hankali. Ga ta nan kwance, ka na yi mata magana, ka na rike hannayenta, ka na yi mata godiya kan hidimar da ka yi mata a rayuwa, ka na kallon motsin bugun zuciyarta a na’ura har ta tsaya cik; rai ya yi halinsa.

Ashe kuma a wata na’urar, ta na nan da ranta.

A bayyane ta ke, rayukan mutane ba sa makale wa cikin na’urorin fasahar zamani bayan mutuwar gangar jikinsu amma dai mutane kan ci gaba da haduwa da su a shafukan sada zumunta irin yadda su kan hadu da su kafin rasuwarsu.

Ko yaya wannan ci gaba da wanzuwa a intanet ke shafar yadda mu ke mutuwa? Kuma wane tasiri hakan ke yi ga wadanda ke makokinmu bayan mun mutu?

Hakkin mallakar hoto Getty

Adadin matattun da ke Facebook kullum dada karuwa ya ke. A 2012, shekaru takwas kacal, da bude Facebook, an samu masu shafuka a dandalin miliyan 30 wadanda su ka mutu. Wannan adadin na matukar karuwa, inda wani kiyasin ke cewa kimanin masu shafin Facebook 8,000 ne kan mutu a kullum.

A na kan haka, sai an kai inda matattu za su fi rayyayu yawa a dandalin, wato ke nan Facebook ya zama wata makekiyar makabarta a intanet wacce kullum kara girma ta ke.

Akwai shafukan Facebook da dama da ke sanar da cewa masu su sun rasu. A kan buga kalmar “domin tunawa”, don haka sai a daina ganinsa a wurare na yau da kullum, irin su tunatarwar zagayowar ranar haihuwarsu.

Sai dai ba kowanne matacce ne a Facebook a ke buga masa wannan tambarin ba.

Kerry, wani dan dakinmu a jami’a ya hallaka kansa ‘yan shekarun baya, amma matarsa da ‘yan uwansa da ma abokai na ci gaba da wallafa bayanai a shafinsa. Kuma duk san da su ka yi rubutun na kan gani a shafina.

Amma Kerry da Gwaggo Jackie ba’a buga musu tambarin mutuwa a shafukansu ba, don haka su na nan a raye a Facebook.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Amfani da shafukan zumunta dai kan bamu damar kulla alaka nan take da mutane a fadin duniya a lokacin da ake wani biki, ko gasar wasanni ko shirye-shiryen talabijin da sauransu. Yanzu kuma lokaci ya yi da zamu duba abinda ke biyo bayan an gama komai da komai: wato bayan mutuwarmu.

A baya can, wasu fitattun mutane ne kadai kan bar wani abin tunawa bayan mutuwarsu, ko dai saboda sun ajiye rubutattun bayani ko kuma saboda wani dan ganin kwakwa ya yi aikin binciken tarihinsu. Amma fasahar kere-keren zamani ta sauya wannan tsarin. A yanzu, kowannenmu na shafe sa’o’i da dama a kowanne mako – fiye da sa’a 12 in ji wasu masanan – muna rubuta tarihin rayuwarmu.

Kamar yadda na shaidawa mahaifiyata, jikokina za su santa ciki da bai ta hanyar nazarin shafinta na Facebook. Saboda ba wai muhimmin abubuwan rayuwa da akan tattara a rubutattun littattafai kawai za su gani ba, ta hanyar Facebook za su ga bayanin abubuwa na yau da kullum na rayuwarta, masu muhimmanci da mara sa muhimmanci. Za su ga me ke sa ta dariya, wadannan irin hotuna ke burgeta, wane gidan abinci su ke zuwa da babana, wadannan labaran ban dariya ne ke burgeta. Kuma za su sami dimbin hotuna da za su kara haska musu rayuwarta. Ta hanyar nazarin wadannan bayanai, jikokina za su iya sanin wacece kakar kakarsu.

Muna iya kallon bayanan da muke bari a shafukan sada zumunta a matsayin ranmu na fasahar zamani: wadanda duk ke bibiyata a Facebook sun san akidata ta addini, ra’ayina na siyasa, soyayyata da mijina, da kuma irin littattafan da nake so. Da zan mutu a yau raina zai ci gaba da wanzuwa a Facebook.

Cikin shekarun baya-bayan nan, kamfanonin fasahar zamani da dama sun kaddamar da tsare-tsaren da za su bada damar ci gaba da hulda da mutane bayan rayuwarsu. Eterni.me, wanda aka kafa a 2014, ya zo da tsarin samar da makwafinka, wanda zai ci gaba da rayuwa bayan mutuwarka.

Mawallafin shafin ya ce mutuwa dole ce amma za ka iya rayuwa har abada ta hanyar makwafinka na intanet, “mutane kuma su ci gaba da hulda da kai ta hanyar tunaninka da labarurrukanka kusan tamkar yadda su ke tattaunawa da kai a lokacin rayuwarka ta duniya.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Idan kamfanoni irin su Eterni.me su ka yi nasara, jikokina, ba bayanin mahaifiyata dalla-dalla kurum zasu iya gani ba, har ma su na iya tambayar makwafinta na intanet, kuma su sami amsoshin da in da sun risketa kan ta mutu abinda za ta ce nan.

Masana ma na hasashen cewa za a iya samar da fasahar dawwama a rayuwa wacce ma ta zarce makwafin mutum a intanet. Misali, wani dan kasuwa Martine Rothblatt ya kera wani mutum-mutumi mai amfani da fasahar zamani mai suna Bina 48. An kera mutum-mutumin ne bisa siffar matar Rothblatt, kuma ya na dauke da muryarta da kuma bayanai game da abubuwan da ta yi a rayuwa.

Rothblatt, shugaban kamfanin United Therapeutics, wanda takensa shi ne “mutuwa zabi ce”, na ganin cewa nan gaba matattu za su iya wanzuwa ta hanyar shirya manhajar kwamfuta, wacce za ta bai wa mutum-mutumi damar yin tunani tare da amsa tambayoyi tamkar mutanen da su ke kwaikwaya.

Hakkin mallakar hoto Getty

Idan har hakan ta tabbata, ya zamo masoyanmu na ci gaba da rayuwa bayan mutuwarsu, wane tasiri hakan zai yi kan yadda mu ke makoki?

Daya daga cikin manyan littattafan da su ka yi bayani game da jimamin mutuwa shi ne ‘Death and Dying’ wanda Elisabeth Kubler-Ross ta wallafa a 1969. A cikinsa ta wassafa matakai biyar na makoki: rashin amincewa, fusata, daidaitawa, damuwa, sai kuma amincewa. Tun bayan wallafa littafin, masanan zamani sun soki matsayarsa musamman ma da yake nuna cewa karshen jimamin mutuwa shi ne amincewa mamata sun tafi ke nan ba za su dawo ba, don haka mu ma mu rabu da jimaminsu mu ci gaba da rayuwarmu.

Masana a yanzu kuwa na nunawa masu jimami cewa wadanda su ka mutu na nan tare da su cikin zukatansu. Dangantakarsu ce kan sauya amma dai ta na nan.

Duk da haka, wani bangaren na jimamin mutuwa ya hada da mu ci gaba da harkokin rayuwarmu tare da mancewa da mamatan. Ba wai mu manta cewa sun taba rayuwa ba, amma dai mu manta cewa muna tare da su cikin wannan duniyar.

A nan gizon ke sakar: a wannan zamanin, intanet ba za ta bar mu manta ba.

Hakkin mallakar hoto iStock

A baya dai tuna mamata wani abu ne na zahiri. Kafin ka ga kushewarsu sai ka tashi ka je makabarta ko kuma ka dauko littafan adana hotuna. Wato dai sai ka dauki wani lokaci da za ka tuna baya.

A Facebook komai a yanzu yake faruwa. Don haka Gwaggo Jackie na rayuwa a shafin kamar yadda nake rayuwa, babu batun cewa ta mutu sai dai labari. Haka kuma duk miliyoyin matattun nan na Facebook ba su zama sai labari ba.

A yanzu dai babu wata hanya da za ta magance matsalar wanzuwar matattu a matsayin fatalwoyin intanet. Fatana daya shi ne nan gaba ita ma intanet ta fara manta abubuwan baya.

Idan kana so ka karanta wannan a harshe Ingilishi latsa nan. Facebook is growing and unstoppable digital graveyard.