Jirgin da ya jawo yaki a Los Angeles

Hakkin mallakar hoto John Campbell

Shekaru sittin da su ka wuce, an fafata yaki a sararin samaniyar Los Angeles – sanadiyyar wani jirgi mara matuki da ya tsere.

Shekaru goma bayan kammala yakin duniya na biyu, an tada jiragen yakin Amurka biyu domin kare birnin birnin Los Angeles daga wani harin sama na ba-zata.

Magidanta sun yi gudun tsira lokacin da suka ga ana luguden bama-bamai. Ba abokan gaba ne su ka kai harin ba, kuma mayakan ba su yi nasara ba. Wannan arangamar ita ce malaman tarihi ke kira Yakin Palmdale.

Wannan shi ne bayanin abinda ya faru da safiyar Alhamis shekaru 60 cif da su ka wuce – da kuma dalilin da ya sa mu ke tare da hatsarin sake afkuwarsa har yanzu.

Da karfe 11:34 na safiyar Alhamis 16 ga Agustan 1956, aka tashi wani jirgin sama mara matuki daga tashar jiragen saman rundunar sojin ruwan Amurka da ke jihar California, domin amfani da shi wurin gwajin wani sabon makami mai linzami.

Abinda aka shirya shi ne bayan jirgin ya yi shawagi a sama, sai a harba masa makamin da zai tarwatsa shi cikin tekun Pacific. Sai dai kuma, maimakon ya bi hanyar da aka tsara masa, sai ya karkata ya nufi birnin Los Angeles mai dimbin jama’a.

Hakkin mallakar hoto Us department of state
Image caption JIrgin yaki samfurin F-89D Scorpions, an tsara cewa zai harbo wani jirgin yakin tarayyar Soviet

Duk kokarin da aka yin a juya akalarsa da na’ura ya gagara, don haka aka tashi jiragen yaki biyu masu jiran ko-ta-kwana domin hana shi fada wa Los Angeles.

Jiragen yakin suka dumfari mara matukin har sai da ya kai wani sarari mara gine-gine. Nan fa dama ta samu ta tarwatsa jirgin kafin ya yi barna. Sai dai kuma kash! Na’urar harba rokokin jirgin ta ki aiki don haka wajibi ne matukan su sarrafa abin harba rokokin da kansu.

Kafin su gama saita rokokin, jirgin mara matuki ya sake juyawa, inda ya yi wa tsakiyar Los Angeles tsinke. Nan fa cikin hanzari su ka bude wuta suka surfa masa rokoki 42 amma ko daya ba ta same shi ba. Kafin mara matukin ya isa yankin Newhall dake bayan garin Los Angeles jirgi na biyu ma ya harba masa rokoki 42.

Abinda aka tabbatar shi ne duk inda guda ya samu jirgin nan sai dai wani ba shi ba, amma samun na sa sai ya gagara.

Daga karshe dai, lokacin da jirgin mara matuki ya tunkari Palmdale, kowanne daga cikin jiragen yakin biyu ya sakar masa rokoki 30; duk ba wanda ya ko karce shi. Baki daya an harba masa rokoki 208 amma ba ko daya da ya same shi.

Daga nan kuma ba su kara kokarin harbinsa ba saboda ya kai garin Palmdale. Haka suka yi ta binsa ya na bilimbituwa har mansa ya kare, abinda ya tilasta masa faduwa a wani fili mai nisan mil takwas gabas da Palmdale, inda ya tsinka wayoyin lantarki yayin faduwar.

Hakkin mallakar hoto Us department od state
Image caption An harba rokoki da dama ga wannan jirgin yakin mai suna Hellcat.- sai dqi babu wanda ya samu shi

Abin mamaki, babu wanda ya samu ko kwarzane. Sai dai rokokin da jiragen yakin su ka harba, ba su fadi a banza ba. Gobara ta barke a filin da ya kai fadin eka 350 kusa da yankin Newhall – kuma sai da aka samu daruruwan ‘yan kwana-kwana kafin a iya kashe ta.

Bangorin rokoki sun fasa tagogin mutane har zuwa cikin gidaje. Wani matashi da ke tuki a Palmdale, sai dai bangorin su ka fasa masa gilashin gaban motarsa; cikin sa’a ya tsira ba ciwo.

Wasu rokokin da yawa kuma sun fadi kasa ba tare da fashewa, sai dai akwai hadarin cewa komai kankantar motsi zai iya sa su fashe. Hakan ya tilasata wa rundunar sojin saman Amurka gudanar da gangamin wayar da kan mazauna yankin domin gudun afkuwar hatsari.

“Allah dai ya tsare,” in ji manzarcin tarihin jiragen sama, Peter Merlin, wanda ya samu labarin faruwar lamarin shekaru 20 da su ka wuce.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka yi amfani da jirgi mara matuki domin gwajin makamai ba.

“An yi amfani da irinsu wurin gwajin makamin nukiliya,” in ji Merlin.

Hakkin mallakar hoto Getty

Merlin na nazari ne kan jiragen yakin da aka yi amfani da su a jihar California a wancan lokacin. Kawo yanzu ya tattara bayanan faduwar jirage 700 tun daga shekarun 1930. Ya ce: “Yawancinsu jiragen yaki ne ko na gwaji.”

A 1997, Merlin da abokin bincikensa Tony Moore su ka gano wurin da jirgin nan mara matuki ya fadi a Palmdale. Ya ce sai da su ka ga alamar gyaran da aka yi wa wayoyin lantarkin da jirgin ya tsinka lokacin faduwarsa.

Wannan lamarin da ya faru a Palmdale dai ba shi kadai ne a tarihin yakin soja inda jirgin sama mara matuki ya daina jin linzami ba. A 2009, rundunar sojin saman Amurka ta yi nasarar harbo wani jirgi mara matuki da ya tsinke a Afghanistan.

Jiragen da ke da matuka ma, a wasu lokutan su kan gagari matukan na su. A 1970, wani jirgin samfurin Convair F-106 ya yi wa matukinsa tutsu a jihar Montana, abinda ya sa shi dire wa da laima.

Abin mamakin shi ne yadda jirgin ya saukar da kansa cikin dusar kankara ba tare da tarwatsewa ko kamawa da wuta ba. Ba yan ‘yan gyare-gyare an ci gaba da amfani da shi.

Wani tsautsayin ya kuma faruwa a 1989, inda wani matukin jirgin tarayyar Soviet ya yi amfani da lema ya fice daga wani jirgin yaki samfurin MiG-23 bayan da na’urorin lantarkin cikinsa su ka daina amfani. A lokacin da abin ya faru, ya na sararin samaniyar kasar Poland, amma bayan da matukin ya fice, sai jirgi ya ci gaba da tafiya ya nausa yamma.

Ya ketare Jamus ta gabas ya shiga Jamus ta yamma. Daga sansanin sojojin saman Amurka da ke Netherlands aka tashi jiragen yaki don su tarwatse gudajjen jirgin a saman kogin North Sea. Sai dai kafin ya isa nan, sai ya juya kudu, bayan kuma da mansa ya kare, ya fada kan wani gida inda ya kashe matashi a kasar Belgium.

Hakkin mallakar hoto Los angeles
Image caption Sojoji da jami'n gwamnati na yin duba a wajen da jirgin mara matuki ya fado, kusa da Palmdale

A cewar Merlin, sababbin jirage su na tattare da hadurra da dama, amma afkuwar hatsarin shi ke haska matsalolinsu tare da bai wa masana damar samar da matakan da za su kara inganta su.

Cikin hukuncin Allah dai, babu wanda ya rasa ransa, a Yakin Palmdale, kamar yadda ake kiransa daga baya. Amma dai an ga tashin hankali; yaki tsakanin mutane da na’ura, shekaru 60 da su ka wuce, a sararin samaniyar Los Angeles.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The runway drone that caused a Cold War air battle.