Shin dabbobi na kashe kansu da kansu?

Hakkin mallakar hoto Dominik

Da gaske ne karnuka, dawaki da sauran dabbobi kan hallaka kansu da gangan? A 1845 jaridar Illustrated London News ta wallafa wani labari mai ban mamaki.

Wani kare da jaridar ta bayyana a matsayin “lafiyayye, kyakkyawa kuma mai daraja ya jefa kansa cikin ruwa” da niyyar hallaka kansa. Kafafuwansa na “tsaye cik”, abinda ba a saba gani ba ga Karen da ke cikin ruwa.

Abinda ma yafi ba da mamaki shi ne, bayan tsamo shi “sai ya sake afkawa cikin ruwan ya na kokarin nutsewa.” Daga karshe dai sai da kyakkyawan karen ya yi nasarar hallaka kansa cikin kogin.

A cewar jaridar, ba wannan karen ne kadai ya kashe kansa da kansa ba. Ba a jima bayan labarin karen ba, aka wallafa wasu labaran biyu; wata agwagwa da ta nutse a ruwa da gangan, da kuma labarin magen da ta rataye kanta a reshen bishiya bayan da ‘ya’yanta su ka mutu.

To amma, me ye gaskiyar wadannan labarai?

Hakkin mallakar hoto alflo
Image caption Wasu karnukan na mutuwa jima kadan bayan mutuwar iyayen gidansu

Mun san cewa dabbobi ma kan samu tabuwar kwakwalwa kamar yadda mutane ke yi: musamman sanadiyyar damuwa da kuma matsananciyar gajiya: abubuwan da ke jawo mutane su kashe kansu da kansu. Mun kuma san cewa dabi’o’in da ada ake ganin mutane ne kawai ke yinsu an gano cewa wasu dabbobin ma na yi.

To amma, har da kashe kai da gangan a cikinsu? Da gaske dabbobi su kan yi kokarin hallaka kansu su na sane?

Wannan ba sabuwar tambaya ba ce: mutanen tsohuwar daular Girkawa ma sun yi nazarinta. Fiye da shekaru 2,000 da su ka wuce Aristotle ya ba da labarin wani doki da ya jefa kansa cikin rami bayan da ta bayyana gare shi ya yi jima’i da mahaifiyarsa ba tare da saninsa ba.

A cikin karni na biyu na kididdigar Kirista, malamin Girkawa Claudius Aelian ya wallafa littafi akan lamarin. Ya kawo labarai 21 da dabbobi su ka kashe kansu da kansu da gangan, ciki har da wani kifin ‘dolphin’ da ya bari aka kama shi da gangan, da karnuka da dama da su ka hallaka kansu da yunwa bayan mutuwar iyayen gidansu, da kuma wata mikiya “da ta hallaka kanta da wuta lokacin da ake kona gawar uban gidanta”.

A zamanin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria cikin karni na 19 na kididdigar Kirista, wani likitan kwakwalwa, William Lauder Lindsay, ya bayyana bacin rai da bakin ciki a matsayin abubuwan da ke muzgunawa dabbobi har su kai ga hallaka kansu su na sane.

Nan take kungiyoyin kare hakkin dabbobi a Burtaniya, irin su RSPCA su ka rungumi wannan fatawar. Masu kare hakkin dabbobi sun yi kokarin kwatanta tunaninsu da na mutane, a cewar masanin tarihin aikin likita, Duncan Wilson na jami’ar Manchester, a Biritaniya, wanda ya yi nazari kan labaran da aka bayar a tarihi game da dabbobin da su ka hallaka kansu da gangan, a wani bincike da ya gudanar a 2014.

Sun yi hakan ne, a cewarsa, domin nuna dabbobi ma “na yin tunani da kulla aniya, abinda ya hada da kulla aniyar hallaka kansu sanadiyyar bakin ciki ko bacin rai.”

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption A 1875 waa barewa ta yi tsalle daga kan tsauni domin hallka kanta, don kada karnuka su farauce ta

Ga misali, mujallar RSPCA mai suna Duniyar Dabbobi ta 1875 na dauke ne da hoton wata barewa da ta daka tsalle daga kan tsauni domin ta hallaka kanta. Sharhin da ya biyo bayan hoton ya ce: “wannan barewar, ta zabi ta hallaka kanta, da ta bari mafarauta su cin mata.”

Sai dai kuma ci gaban da aka samu a kimiyyar lafiya cikin karni na 20 ya sa mutane na kallon kashe kai da kai a matsayin cuta, don haka sai labarin gwarazan dabbobi masu hallaka kansu ya fara raguwa.

Sai a ka mai da hankali kan yadda akan samu garken dabbobi sun hallaka kansu, a mafi yawan lokuta sakamakon matsi, a cewar Wilson. Sai ake kallon hallaka kai a matsayin wata cuta da kan shafi al’umma.

Misali shi ne berayen hamadar kankara da ake kira ‘lemming’ da turanci, wadanda kan yi tsalle daga kan tsauni su na dira cikin teku kungiya-kungiya ko kuma kifayen ‘whale’ da kan fito gabar teku inda rashin ruwa kan hallaka su.

Sai dai binciken Wilson bai yi kokarin gano ko da gaske dabbobi kan yi kokarin hallaka kansu da kansu ba. Abinda aikinsa ya bayyana shi ne yadda labarin dabbobi masu hallaka kansu ke sauyawa daidai da yadda mutanen zamanin labarin ke kallon mutanen da ke kashe kansu da kansu.]

Hakkin mallakar hoto istock
Image caption lemmings’ ba hallaka kansu su ke ba

Amma an samu wani mai binciken da ya yi kokarin samo amsar kai tsaye.

Bai kamata irin wadannan labarai su kidima mu ba, in ji Antonio Preti, mai nazarin kwakwalwa a jami’ar Cagliari da ke Italy, wanda ya yi nazari akan littattafan kimiyya na baya da aka wallafa game da dabbobin da aka ce wai su na hallaka kansu da gangan.

Ya yi nazarin sakamakon bincike kusan dubu guda da aka wallafa tsawon shekaru 40, amma bai samu hujja ko daya da ke nuna wata dabba a dawa da ta hallaka kanta da gangan ba. A cewarsa, irin labaran da ke cikin littafin Aelian “tatsuniyoyi ne kurum”.

Masu bincike a yanzu sun gano cewa berayen ‘lemmings’ ba hallaka kansu su ke ba, illa dai su kan mutu ne sanadiyyar kokarin yin kaura cikin lokaci guda.

A lokutan da kuma dabbobin da ke ajiye a gida ke mutuwa bayan mutuwar iyayen gidansu, Preti ya ce, warwarewar alakar da su ka saba da ita ce kan jawo musu mutuwa.

Hakkin mallakar hoto Tim Cuff
Image caption Kifayen Whale ba yunkurin hallaka kansu suke ba

Wato dabbar ba ta kulla kudirin hallaka kanta; amma, sabonta da uban gidanta kan sa ta ki karbar abinci daga kowa, inda daga karshe sai yunwa ta hallaka ta.

Wannan bayani ya nuna wani abu mai muhimmanci; wato damuwa kan sauya dabi’ar dabba ta yadda za ta iya barazana ga rayuwarta.

Hakan ya faru a dandalin SeaWorld da ke Tenerife a Mayun 2016.

An yayata wani hoton bidiyo a intanet wanda ke nuna wani kifin ‘whale’ wanda ya fito daga kwamin da ake kiwonsa a dandalin SeaWorld tsawon mintuna goma. Daga nan fa sai marubuta su ka hau sharhin cewa kifin ya yi kokarin hallaka kansa ne.

Hakkin mallakar hoto ImageBroker
Image caption Dabi'ar kifayen da aka tsare daban take da wadanda suke sake

Mun san cewa dabi’ar kifayen ‘whale’ da ke tsare ta bambanta da wadanda ke sake. Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne kasancewar kwamin da ake ajiye su bai ko kama kafar girman teku ba.

A baya dai bincike ya nuna cewa takura kan kuntatawa tsararrun kifayen ‘whale’, ta yadda su kan gogi gefen tankin ko kuma su yi ta cije hakoransu.

Abu na farko a cewar Barbara King ta kwalejin William & Mary da ke Virginia, US, shi ne mu fahimci yadda tunanin irin wadannan dabbobin ya ke kafin mu kai ga gano abinda ke sa su sauya ta dabi’a ta yadda za su iya cutar da kansu.

“A sanina, mafi yawan lokuta wani aikin dan Adam ne ke harzuka su, misali farauta ko tsarewa,” in ji King, wacce ta yi rubuce-rubuce game da bakin ciki da hallaka kai a tsakanin dabbobi.

Dabbobin da aka fi ba da misali da su domin nuna cewa dabba kan hallaka kanta da gangan, su ne kifayen ‘whales’ wanda su kan fito gabar teku su kasa numfashi har su mutu.

Hakkin mallakar hoto Dominik
Image caption Karnuka kan shiga damuwa

Kawo yanzu babu wanda ya san dalilin da ke sa kifayen ‘whales’ fitowa daga teku. Wasu masanan na ganin abinda ke faruwa shi ne, akan samu ‘whale’ mara lafiya ne da kan matso kusa da wurin da ruwa bai da zurfi sosai domin yin jiyya, amma da yake danginsa su na da zumunci sai su ma su biyo shi. Wannan shi ake kira ‘ra’ayin shugaba mara lafiya’ amma ba a daukar hakan a matsayin kashe kai da gangan.

Baya ga wannan kuma, akwai wasu kananan halittu da kan tare a jikin dabbobi su jirkita musu tunani ta yadda su dabbobin za su hallaka, halittun kuma su amfana.

Misali, halittar Toxoplasma gondii na kama beraye ta sa su daina tsoron mage. Idan mage ta cinye beran, sai halittar ta ci gaba da hayayyafa a cikin magen. Wani bincike a 2013 ya gano cewa T. gondii na hana bera tsoron mage har abada, ko da bayan an raba beran da shi.

Haka kuma, akwai wata funfuna mai suna Ophiocordyceps unilateralis wacce ke iya juya akalar tururuwai. Ta kan sa tururuwan su hallaka kansu a wurare masu danshi, inda funfunar za ta rayu.

Hakkin mallakar hoto Visualas Unlimited
Image caption Wannan tururwar ta makara, domin tuni funfuna ta cimmmata

Bugu da kari, matan gizo-gizo kan bari ‘ya’yansu su cinye su. Koda yake su kan mutu sanadiyyar hakan, wannan sadaukarwa ce ba hallaka kai da gangan ba, domin kuwa wannan na nuna tsananin kaunar da uwar ke yi wa ‘ya’yanta. Mata kan ciyar da ‘ya’yansu jikinsu ne domin ba su sinadiran da za su taimaka musu a rayuwa.

Cewar ba za a kira wannan dabi’ar hallaka kai da gangan ba, na bukatar mu bayyana me ake nufi da hallaka kai da gangan. Shi dai ana daukarsa ne a matsayin “kashe kanka da kanka bisa niyyar yin hakan”.

Mun san cewa wasu dabbobin su kan kashe kansu. Tambayar ita ce; da niyya su ke hakan? Misali matar gizo-gizo na iya yin haka ne don ciyar da iyalinta ba don ta mutu ba.

Zancen gaskiya shi ne, kawo yanzu ilimin dan Adam bai kai yadda zai iya gane tunanin dabba ba, a cewar King.

Hakkin mallakar hoto Naturepl
Image caption Dabbobi na jin tsoron wadanda ke farautarsu

Sai dai wasu masanan ba su yadda da bayaninta ba. Sun ce dabbobi ba za su iya kashe kansu da gangan ba saboda kwakwalwarsu ba ta kai ta yi tunanin halin da suke ciki a duniya tare da neman mafita ta hanyar mutuwa ba.

Thomas Suddendorf, masanin dabi’un halittu a jami’ar Queensland da ke Australia, ya ce “akwai bambanci mai nisa tsakanin tunanin mutane da na dabbobi: mu mu kan tada hankali kan abinda mu ke hasashen zai iya faruwa amma su ba sa yi.”

Hakkin mallakar hoto Bin Yang
Image caption Birrai na shiga damuwa idan abokansu su ka mutu

Ajit Varki, na jami’ar California da ke San Diego ya goyi bayansa, inda ya ce: “Mutane sun san mutuwa amma dabbobi ba su santa ba.

“Menene ma kashe kai da kai?” in ji Varki. “Shi ne ka jawo sanadin mutuwarka da kanka, amma ta yaya za ka yi haka idan ba ka san za ka iya mutuwa ba? Don haka babu wanda zai iya kashe kansa da gangan sai mutum.”

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Many animals kill themselves, but it is not suicidal.