Yaran da ke gani tar a cikin ruwa

Sabanin mafi yawan mutane, kananan yara a wata kabilar Thailand na iya gani tar a karkashin kogi. Da ya aka yi su ke iya haka? Shin sauran yara za su iya koyon wannan gwaninta?

“Lokacin da igiyar ruwa ta motsa, sai yaran su ka fara iyo. Sai dai iyon nasu ban taba ganin irinsa ba. Nutso su ka yi cikin ruwan amma idonsu a bude wasai kamar ‘ya’yan ruwa.”

A can cikin kananan tsibiran da ke kogin Andaman, a yammacin kasar Thailand akwai wasu kananan kabilu da ake kira Moken, wasu kuma ke musu lakabin ‘yan ruwa.

‘Ya’yansu na kusan yini a cikin ruwa, su na farautar abinci. Wannan aiki ya dace da su – saboda su na iya gani a karkashin ruwa. Koma kowanne yaro ma na iya samun wannan baiwar.

A 1999, Anna Gislen ta jami’ar Lund da ke Sweden na gudanar da binciken kan abubuwan da su ka shafi yadda idanu ke gani, sai wani abokin aikinta ya shawarce ta da ta yi nazari kan ‘ya’yan kabilar Moken masu gani a cikin ruwa. “Na kwashe watanni uku ina zama a wani dakin gwaji mai duhu, don haka nace a raina, ‘gaskiyane, mai zai hana in tafi nahiyar Asiya?’ in ji Gislen.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Matasa a kabilar Moken ba sa iya gani kamar yara

Gislen da ‘yarta mai shekaru shida su ka tafi Thailanda su ka zauna tare da kabilar Moken, wadanda mafi yawansu kan rayuwa ne cikin gidajen da aka gina akan turaku a bakin ruwa.

Lokacin da ruwa ya kawo, sai ‘ya’yan Moken su ka kunna nutso domin su debo abinci daga can karkashin ruwan fiye da inda Gislen da ‘yarta za su iya hangowa. “Idanuwansu a bude su ke debo kifayen cikin kwanso da sauran dabbobin ruwa ire-irensu,” in ji Gislen.

Gislen ta gudanar da gwaji domin tantance karfin ganin yaran a karkashin ruwa. Yaran sun amince da gwajin cikin gaggawa. Gislen ta ce: “Su dauka su ke yi kamar wani wasa ne.”

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption 'Yan kabilar moken na zaune ne a wani tsibiri da ke gabar ruwa a Thailand

Gwajin dai kan bukaci yaran su yi nutso cikin ruwan ne sannan su aza kawunansu bisa wani faifai. Daga nan su na iya hango wani kati da aka zana layuka akai, wasu a tsaitsaye wasu a kwakkwance. Idan sun gano katin, sai su fito saman ruwa su bayyana alkiblar da layikan ke kalla.

Duk lokacin da su ka sake nutso ana sauya katin, inda ake kara rage kaurin zanen layikan, abinda ke sa ganinsu a cikin ruwa ya kara wuya. Sakamakon ya nuna cewa ‘ya’ya Moken sun nunka yaran Turai, wadanda aka yi wa irin wannan gwajin daga bisani, karfin gani a ruwa.

To me ya jawo haka? Shi dai idon mutane ya kan gani ne ta hanyar karkatar da hasken da ya shigo ido zuwa wani tantani da ke can bayan idon da ake kira ‘retina’. Shi tantanin, shi ya kan sauya haske zuwa sakon da kwakwalwa za ta fassara a matsayin hoto.

Idanu na iya aika hasken zuwa tantanin ‘retina’ saboda fatar da ke gaban ido ta na kunshe da ruwa. Hakan na sa nauyinta ya dara na iskar da ke wajen ido. Don haka sai fatar gaban ta tura hasken zuwa ga tantantanin bayan ido.

Amma lokacin da aka nutsar da ido cikin ruwa, sai fatar gaban idon ta gaza tura hasken zuwa baya sosai saboda nauyinta ya daidaita da ruwan da ke wajen ido. Dalili ke nan da gani kan koma dishi-dishi a ruwa.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Idan aka bawa sauran yara horo, suma za su iya gani tar a cikin ruwa kamar yaran kabilar Moken

Gislen ta yi hasashen cewa tun da yaran Moken na iya gani wasai a cikin ruwa, ko dai halittar idanunsu ce ta bambanta da ta sauran yaran duniya ko kuma sun koyi amfani da idanunsu a cikin ruwa ne ta wata hanya da ta sabawa yadda sauran yara ke amfani da nasu.

Amma sai ta yi tunanin hasashenta na farko ba ya kan turba, saboda idan har halittar idanun ‘yayan Moken ce ta sauya, ke nan ba za su iya gani da kyau a wajen ruwan ba. Da ta gwada karfin ganin ‘ya’yan Moken a waje, sai ta ga sakamakon yayi daidai da sa’anninsu na Turai.

Don haka sai Gislen ta samu yakinin cewa akwai dai abinda ‘ya’yan Moken ke yi wa idanunsu a cikin ruwa wanda ya bambanta da na sauran yara. A ilmance, hanyoyi biyu za a iya bi domin kara gani a cikin ruwa; Ko dai a kankantar da kwayar ido, ko kuma a sauya siffar kwanson da ke rike da kwayar idon.

Auna girman kwayar ido abu ne mai sauki, sakamakon kuma ya nuna cewa yaran kan kankanta kwayar idonsu zuwa karshen kankancewar da bil’adama zai iya. Sai dai wannan kawai ba zai iya sa ganinsu ya yi matukar karuwa ba. Wannan ya sa Gislen tunanin duk yadda aka yi su na hadawa da sauya siffar kwanson da ke dauke da kwayar idanunsu.

Ta ce: “Hakan ce ta tilasta mana amfani da alkalumman lissafi wurin gano iyakacin sauyin da su ke iya yi wa kwanson da ke rike da idanunsu domin ganin nesa a cikin ruwa. Mun kuwa gano cewa su na iya sauya siffar kwansan nasu kwarai da aniya, fiye da yadda ake sa rai a cikin ruwa.”

“A dabi’ance, idan ka yi nutso a ruwa kuma ya na dusashe maka ne don haka idonka ba ya kokarin sauya kwansonsa don ba ka damar gani a cikin ruwan,” in ji Gislen. “Sai dai ‘ya’yan Moken na iya yin duk biyun; su kankanta kwayar idonsu sannan su sauya siffar kwanson kwayar idon. Kifayen ‘dolphin’ ma su na iya hakan.”

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Me yiwa idanun yaran sun saba da ruwan teku duk kuwa da gishirinsa

Gislen ta kuma gwada manyan kabilar Moken amma idanunsu ba su da irin baiwar da idanun yaransu ke da ita, abinda ke sa su farautar kifi ta hanyar soke shi da mashi daga gabar kogi maimakon yin nutsu su kamo kifi. “Idan muka girma, kwanson kwayar idonmu kan yi tauri ta yadda ba zamu iya sauya masa siffa ba, don haka ba mamaki don manyan Moken sun kasa gani a cikin ruwa,” in ji Gislen.

Daga nan kuma Gislen ta yi kokarin gano ko ‘ya’yan Moken na da wata kwayar halitta ne ta dabam da ke ba su damar sarrafa idanunsu ta yadda su ke iya gani garau a cikin ruwa ko kuma kurum tsabar sabo ne.

Domin tantance hakan sai ta bukaci wasu ‘ya’yan Turawa da su ka je hutu Thailand da kuma wasu ‘ya’yan Turawan da ke Sweden da su yi atisayen nutso a cikin ruwa tare da kokarin gano inda layikan da aka zana akan kati ke kallo.

Bayan da suka samu atisaye sau 11 cikin wata guda, sai rukunan biyu na yaran duk su ka zama su na iya gani garau a karkashin ruwa kamar ‘ya’yan Moken.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Manya a kabilar Moken na kamun kifi ne daga waje

Gislen ta koma Thailand a shekarun baya bayan nan don ziyartar kabilar Moken sai dai ta tarar da gagarumin sauyi. A 2004 girgizar kasa a cikin tekun India ta haddasa tsunamin da ta lalata kusan daukacin kauyukan Moken.

Tun daga wancan lokacin gwamnatin Thailand ta yi bakin kokarinta na ganin ta tsugunar da su a wuraren da ke nesa da bakin ruwa tare da daukar su aikin kula da gandun daji. “Abin da wuya,” in ji Gislen. “Akwai bukatar a taimaka su, a tsare su daga hatsari tare da shayar da su romon ci gaban zamani, sai dai kuma yin hakan na sa su saki al’adunsu.”

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Gidajen yan kabilar Moken ke nan da Tsunami ta lalata a 2004

A wani bincike da ba ta wallafa ba, Gislen ta auna karfin ganin yaran da ta auna a gwajinta na farko. A wannan karon, yaran sun zama matasa, kuma su na ci gaba da iya gani a cikin ruwa.

Abin takaicin shi ne, yaran da Gislen ta auna a gwajinta na farko na iya zama na karshe a kabilarsu da ke iya gani a ruwa. Ta ce: “Yaran zamani ba sa samun damar shiga cikin ruwa akai-akai kamar yayyensu na baya. Don haka ba na jin kananan yaran da ke tasowa a cikin kabilar a yanzu na da wannan kaifin ganin a cikin ruwa.”