Me zai faru idan dabbobi suna da hankali irin na mutane?

Hakkin mallakar hoto Frans LantingSPL

Idan duk halittar da ke fadin duniyar nan na da hankali irin namu, zamu hada kai ne ko kuma zamu yaki juna?

A fim din ‘Planet of the Apes’, wani mutum ya samu kansa a wata duniya da birrai masu hankali da tunani ke bautar da mutane. Pierre Boulle, wanda ya rubuta littafin a 1963 wanda daga baya aka mai da shi fim ya ce labarin na sa na cikin rukunin ‘in-da-ace’.

To me zai faru idan aka fadada hasashen, ya zama ba birrai ne kadai zasu yi irin tunanin mutane ba, har ma dukkan wata nau’in halitta dake duniya? Idan aka wayi gari duk dabbar da ke duniya ta zama mai hankali da tunani me zai faru?

Wata halittar za ta mulki ragowar ne kamar yadda mutane su ka yi ko kuma za a samu sasantawa ne a gudanar da rayuwa cikin daidaito da mutunta juna? Wannan dai batu ne da ba zai taba yiwuwa ba amma tattauna shi zai sa mu fahimci gaskiya game da dabi’ar bil’adama da kuma matsayinmu a duniya, na halittar da ta mallake dukkan halittu.

Abin takaicin shi ne, da hakan za ta faru da lamarin ba zai yi kyau ba: “Rikici ne zai barke a bankasa,” in ji Innes Cuthill, masanin dabi’ar zamantakewar halitta a jami’ar Bristol. “Mu daina dauka cewa hankali ya na sa kirki.”

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Da yake birrai suna kama da mutane, za su iya samun wata dama fiye da sauran dabbobi

“Ai kashe juna zamu yi,” in ji Robin Dunbar, mai nazarin sassauyawar dabi’ar halittu a jami’ar Oxford. “Ba a san mutane da neman zaman lafiya ba idan suka hadu da jinsin mutanen da basu san su ba.”

Josep Call, mai ilimin kwatanta dabi’ar halittu a jami’ar St. Andrews ya amince da cewa. “Idan ka duba tarihin dan Adam, ba na jin mun yi shahara kan kulla abota. Ba mamaki yanzu mun dan sassauta fiye da kakanninmu na baya, amma duba duniyar a yanzu ka gaya man in har mutane jinsin lumana ne.”

Idan aka yi la’akari da dogon tarihin da mu ke da shi na hallaka wasu jinsin halittun har ma da ‘yan uwanmu mutane, babu wani dalili da ke nuna cewa mu, ko kuma duk wata dabba da ta samu irin tunaninmu za mu iya wata dabi’a sabanin wacce mu ke a kai.

A takaice dai, yakin duniya na uku ne zai barke. “Mu na da mummunar alaka tsakaninmu da bakin jinsi musamman wadanda mu ke kallonsu a matsayin barazana,” in ji Cuthill.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Kifayen Shark za su iya yin mulki ne kawai a cikin ruwa

Idan ko haka ne, wa zai yi nasara? Jinsina da yawa dai ba su da alamar nasara. Misali, duk dabbobin da ke cin tsirrai zalla, na bukatar bata lokaci da yawa wurin cin abinci da zai ishe su.

Don haka za su samu takaitaccen lokacin da za su sadar da bayanai a tsakaninsu, su kera ababen more rayuwa, su bunkasa al’adunsu ko kuma su yi yaki. Don haka dabbobin da ke cin abinci samfurin protein su ne za su yi zarra.

A cikinsu, kifayen ‘shark’, ‘dolphin’, da ‘whale’ su ma ba inda za su kai tun da iyakarsu cikin ruwa. Sai dai za su iya fafatawa tsakaninsu don samun mulkin cikin ruwan.

Haka kuma duk dabbobin da ba sa iya rayuwa sai a wasu kebantattun wurare kamar kurmi, ko hamada ba za su iya mulkar duniya ba. Manyan mafarauta irin su zaki, damisa, da kyarkyeci da ma wadanda ba sa farautar irin su giwa da mugun dawa su ne za’a fafata da su, kamar yadda ta faru a fim din ‘Jurassic Park.’

A farkon wayewarsu, su ne zasu zama babbar barazana gare mu. Da za’a tsiraita mu a jefa mu cikin dokar daji, tabbas su za su yi nasara akan mu. Amma kasancewar muna da makaman zamani, kuma mutane sun fi wadannan dangin halittun yawan al’umma, barazanar ta su ba za ta yi nisa ba kafin mu shafe su daga bayan kasa (abinda, a yanzu ma muke cikin yi wa jinsin halittu da yawa).

Kamar yadda Alex Kacelnik, masanina dabi’ar zamantakewar halittu a jami’ar Oxford ya ce: “Daga karshe dai mu zamu yi nasara.”

Amma fa da zarar mun kawar da manyan dabbobi masu cin nama, zamu fuskanci wadansu abokan adawar: ‘yan uwanmu makusanta, wato birrai. Kamar yadda Cuthill ya bayyana, kayayyakin fasaharmu sun taimaka matuka wurin ci gabanmu, kuma birrai na da halitta irin ta mu, wacce za ta basu damar amfani da fasaharmu.

Za su iya amfani da kwamfutocinmu, su rike bindigoginmu sannan su amfana da halittar jikinsu wacce tafi ta dan Adam kuzari. Haka kuma za su iya kirkiro na su kayan fasahar cikin gaggawa ta hanyar amfani da kayan fasahar mutane.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Dan adam ba shi da karfi kamar sauran dabbobi

Sai dai ‘yan uwanmu birrai zasu iya wadannan abubuwa ne kurum idan har za su iya samun tarin ilimin da mu ke da shin a yadda ake amfani da kayayyakin fasahar, yadda ake yaki, yadda za su fahimce mu – abokan gabarsu – da kuma sauran ilimai da dama.

Amfani da iliminmu domin amfaninsu shi ne hanya guda tilo da zasu iya bi wurin murkushe mu. Sai dai ba za su samu wadataccen lokacin da za su mallaki iliminmu kafin su ma mu kawar da su daga doron kasa. “Da ace za su samu duk ilimin da muke da shi to da za a yi canjaras tsakanin mutane da birrai,” in ji Call. “In kuwa ba haka ba, koda yake za su zamo babban kalubale gare mu, duk da haka ba zasu iya mallake duniya ba.”

Amma fa idan lokaci ya tsawaita, babban ginshikin mallakar duniya shi ne iya rayuwa cikin kowanne yanayi da muhalli. Hakika, wannan kwarewar na daga cikin sirrin daukar bil’adama a ban kasa.

Duk da dai asalinmu daga yanki mai dumi da yawan ciyayi mu ke, mun gano hanyoyi da dama na rayuwa a sassan duniya dabam-daban, kama daga tsaunuka zuwa hamadar kankara.

Haka kuma yawan adadi zai yi rana, da kuma kwarewa wurin iya buya.

Watau dai, alamomi na nuna cewa halittun ‘bacteria’ da sauran kananan halittu irinsu su ne za su gaje mulkin duniya – fiye da yadda su ke yi a yanzu. A’a ‘bacteria’ ba su da kwakwalwa don haka ba zata taba yiwuwa su samu hankali da tunani irin na mutane ba.

Amma dai gazawar tasu, alheri ne a gare mu, idan aka yi la’akari da yawansu. “Ko a yanzu ‘bacteria’ na ko’ina, har da cikin jikinmu,” in ji Call. “Da za su yi hankali da kuwa za su iya ganin bayanmu.”

“Ba zan yi mamaki ba idan wata karamar halitta dangin ‘virus’ ta mallake duniya,” in ji Dunbar.

“Mutane za su shiga cikin bala’i idan fada ya hado su da kananan halittu masu hankali da tunani,” in ji Call. “Matsalar ita ce, ba zamu iya kawar da su ba, saboda mu na bukatarsu domin ci gaba da rayuwa.”

Hakkin mallakar hoto Istock
Image caption Wace dabbace za ta gaji kasa bayan dan adam?

Koda an hallaka mutane baki daya, rikicin dai ba karewa zai yi ba. Babu wani dalili da zai sa mu yi tsammanin dabbobin da ke da hankali da tunani irin na mutane za su yi halayya dabam da wacce mu ke yi ta wurin murkashe sauran halittu da mallake su.

Haka kuma za a samu rikice-rikice cikin jinsin halittu guda. “Ku tuna cewa dabbobi ba sa magance matsaloli domin amfanin jinsinsu baki daya,” in ji Kacelnik. “Su na rigima da junansu ne domin amfanin kabilarsu ko iyalansu.”

Watau dai kusan babu wanda zai amfana idan kowacce halitta ta sami hankali da tunani irin na mutane. Duk lokacin da aka karar da wani jinsin halitta, muhallan da suke ciki za su ci gaba da lalacewa, babu wanda zai tsira sai dai masu kwarin rai irin su ‘bacteria’, kyankasai da ko gafiyoyi.

Kamar dai yadda Cuthill ya ce: “Duk jinsin halittar da aka bari a baya, za su bata duniyar ne kamar yadda mu ke yi a yanzu.”

Ya ce: “Ba na jin akwai wani jinsin halittu da za su fi mu tausayi da jin kai. Daidaiton da ake samu a rayuwar yanzu na faruwa ne saboda wani yafi wani karfi a duniya.”

Idan kan so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What will happen if all animals were as smart as us.