Me ya sa bambancin siyasa ya yi kamari a 2016?

Image caption ‘Yancin rayuwa a wurin da ka ke so, ilimi da intanet:ko suna kara farrraka tsakanin akidun siyasa masu hamayya da juna?

Kaddara ka na majalisar hira, ku na tattauna zaben da ke tafe da kai da abokanka. Sai ka ce har yanzu ba ka da dan takara.

A takaice ma kai ka na ganin duk bangarorin biyu su na da ta cewa. Wane irin kallo za su yi maka?

Bambancin siyasa bai taba tsanani kamar bana ba. A Amurka, Donald Trump ne ke karawa da Hillary Clinton.

A Turai, masu goyon bayan gamayyar kasashen Turai ne ke fafatawa da masu adawa da gamayyar.

A Turkiyya, masu kishin Islama ne su ke arangama da ‘yan ba ruwan addini da rayuwa.

A kasashen Amurka, da Australia da nahiyar Turai, gibin da ke tsakanin masu neman sauyi da ‘yan ra’ayin rikau sai kara fadada ya ke.

Idan ka duba shafukan sada zumunta za ka ga cewa adawar da ake nuna wa abokan hamayya sai kara daduwa ta ke yi.

Alal misali, A Amurka, tsanar da ake yi wa abokan hamayya ta nunka daga 1992 zuwa 2014, kamar yadda sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Cibiyar Bincike ta Pew ta gudanar ya nuna.

Karo gaba zuwa 2016 ka tarar mafi yawan ‘yan jam’iyyun Republicans da Democratics na matukar tsanar abokan kasayyarsu.

Daga cikin fiye da mutane 5,000 da su ka bayyana ra’ayinsu, fiye da rabi na ganin ‘yan adawa a matsayin masu karancin tunani, yayinda kaso 40 na ganin ‘yan jam’iyyar adawa sun fi sauran Amurkawa lalaci, rashin gaskiya, da rashin amana.

Ko me ke jawo wannan tsananin adawar? Bincike kan halayyar bil’adama na nuna cewa son zuciya – ko da kuwa ya gamu da gaskiya, ko hujja ta zahiri, ko sanin abinda ya kamata – na hana mutane sauraron ra’ayin da bai dace da nasu ba.

Haka kuma wasu masanan na ganin abubuwa da dama a rayuwar yau na sa mutane su kare kafewa kan ra’ayoyinsu da akidunsu na siyasa – ba ma tare da sun fahimci hakan ba.

Wani abu da zai iya kawo wannan dabi’ar shi ne tasirin cudanya da masu ra’ayi daya.

A haka, sai ka ga kamar tattaunawa da abokanka zai ba ka damar gano kurakuren da ke cikin tunaninka da kuma jin wasu ra’ayoyi na dabam. Amma dai a gaskiya, ba haka ba ne.

“Idan ka hada gungun abokai masu ra’ayi daya a daki guda, su kan taimaki juna wurin karfafa ra’ayinsu ne,” in ji Jessica Keating, mai nazarin halayyar dan Adam a jami’ar Colorado, Boulder.

Image caption Zama tare da wa su mutane da ra'a yoyin ku ya zo iri daya

Domin gwada wannan ikirari, Keating ta kai wasu daliban jami’a dakin gwaji, inda ta bukaci su tattauna ra’ayinsu na siyasa.

A gwajin farko, abokai masu ra’ayi guda sun yi musayar ra’ayi akan wanne shugaban kasa ne yafi; Barack Obama ko George W Bush?

A na biyun kuma, sun tattauna game da dan takarar da za su mara wa baya a zaben 2012 tsakanin Barack Obama da Mitt Romney.

Bayan tattaunawar, an tambaye su ra’ayoyinsu game da dan takarar a yanzu da kuma kafin a gudanar da muhawarar. Kamar yadda Keating ta yi hasashe, baki dayansu sun kara kankame ra’ayoyinsu ne. Abin mamaki, kekashewar ra’ayin na su ya afku ne cikin minti 15 kacal. Kuma ba su ma fahimci cewa hakan na faruwa ba.

“A gwaji na farko ba su fahimci cewa ra’ayinsu ya kekashe ba – a na biyun kuma sun fahinci yadda sabanin ra’ayinsu ya kara tsananta amma ba sa gane cewa ya yi tsanani da yawa haka ba,” a cewar Keating.

Ba wanda ya ke da tabbacin abinda ya ke jawo wannan tasirin, mai yiwuwa ne samun sabon bayani ne: ta hanyar tattaunawa da mutanen da ke da irin ra’ayinsu, su na iya ji wasu kwararan dalilan da za su taimaka musu wurin karfafar ra’ayinsu.

Haka kuma zai iya yiwuwa tasirin ya biyo bayan kokarin da su ke yi na samun karbuwa a wajen abokansu ne.

Sai dai kuma, a wannan zamani abu ne mai sauki mutum ya gudanar da rayuwarsa ba tare da mu’amala da masu ra’ayi daban da na sa ba.

Wannan karancin damar jin ra’ayin da ya saba da naka shi ne ya addabi Matt Motyl, mai nazarin halayyar dan Adam a jami’ar Illinois da ke Chicago.

A ‘yan shekarun baya, ya fara halattar tarurrukan siyasa da wuraren ibadar mutanen da ba zai sami damar haduwa da su a rayuwarsa ta yau da kullum ba.

“Na kan dawo wurin abokaina masu ra’ayin neman sauyi ina kokarin bayyana musu cewa ‘yan ra’ayin rikau ba jahilai ba ne ba kuma mugaye ba ne,” in ji shi.

Ya fuskanci kyara daga abokanansa tare da zarginsa da cin amana. Wannan ta sa Motyl yin nazari don gano abinda ke faruwa.

Sanannen abu ne cewa a Amurka, ra’ayin siyasa ya bambanta tsakanin kudu da arewa.

“Ko a yau, idan za ka yi hasashen abinda mutane za su zaba kuma abu daya kawai za ka iya sani game da su, to zabi sanin adireshinsu domin ya na daga cikin manyan dalilan bambancin ra’ayin siyasa,” in ji Jonathan Haidt, masanin halayyar dan Adam daga jami’ar New York.

Don haka sai Motyl ya yi hasashen ko bambancin ra’ayin siyasa na da dangantaka da mazaunin masu zabe.

Idan haka ne wannan ne a gaba – kaza ce ta fara samar da kwai ko kwai ne ya fara samar da kaza? – wato mutane kan amince da ra’ayin makwabtansu ne idan sun koma sabon wuri ko kuma ra’ayinsu ne ke tasiri wurin zaben inda za su rayu?

Domin gano amsar wannan tambaya, Motyl ya yi nazarin bayanin da aka tattara game da miliyoyin Amurkawa da aka yi wa gwajin akidojinsu na boye, wanda su kansu ba su san su na da su ba, irin su wariyar launin fata.

Abubuwa uku ne kawai su ka dame shi: Ina mutumin ya ke zaune a yanzu, ina yafi dadewa da zama a rayuwarsa, kuma menene akidarsa ta siyasa.

Daga nan kuma sai ya kwatanta ya ga bambancin da ke tsakanin ra’ayinsa na siyasa da kuma mafi karbuwar ra’ayoyinsa a wuraren biyu.

Sakamakon ya nuna cewa mutanen da akidunsu su ka saba da na makwabtansu sun fi saurin sauya mazauni – kusan takwas cikin 10, wanda ya gaza biyar cikin 10 tsakanin wadanda ra’ayinsu ya dace da na makwabtansu.

Haka kuma, daga cikin wadanda su ka sauya mazauni, inda su ke koma wa kan dace da irin ra’ayinsu.

Kasancewar mutane da yawa na sauya mazauni domin haduwa da mutanen da ke da irin ra’ayinsu a siyasance, tasirin cudanya da masu ra’ayi daya kan akidar siyasa ya zama tamkar ruwan dare a Amurka.

Ko da wanada bai taba sauya mazauninsa ba, wani abu da ya mamaye tsarin rayuwar zamani ya sa shi ma ya na iya fuskantar wannan tasiri. Wannan abun shi ne intanet.

Shafukan matambayi-baya-bata na intanet kan ba da bayani ne daidai da ra’ayin mai tambayi. In da mutane biyu za su rubuta “Donald Trump” a wani shafin neman bayani, zai iya yiwuwa kowannensu ya sami jerin bayanai mabambanta.

A shafukan sada zumunci kuwa, wannan matatar ra’ayoyin ta na tasiri hark an jerin labaran da mu ke gani.

“Ya na da matukar wuya mutane su kulla alaka da wadanda ke da bambancin akidar siyasa da su a shafukan sada zumunta,” in ji Motyl.

Ko mu da kanmu zamu zaba, mutane da yawa kan zabi kafafen labaran da su ka dace da ra’ayinsu ne.

Fasahar sadarwar zamani irinsu wayoyin komai-da-ruwanka, kwamfutar tafi-da-gidanka, talabijin da sauransu sun bamu damar samun bayanai da labarai da su ka shafi ra’ayoyinmu kawai.

Da ma kuma ka na samun karin bayanai, ka na kara gamsuwa cewa ra’ayinka shi ne daidai.

“Abinda ya kamata a shi ne mutanen da su ka samu hujja guda, ra’ayinsu ya zamo daya. Abinda bai dace ba kuwa shi ne mutane su samu hujja guda amma ra’ayinsu ya bambanta – sai dai kuma hakan shi ke faruwa,” in ji Ross.

Wannan ne ya sa mutanen da ke da ilimi sun fi ra’ayin rikau.

Amma lamarin yafi haka baci. Duk lokacin da ma muka ji ra’ayin da ya saba mana, akwai wasu makarai a cikin zukatanmu da ke hana mu karbar sababbin ra’ayoyin da su ka saba mana.

Abinda yafi komai matsala shi ne mutum ya amincewa kansa cewa ya san abinda ke ran abokin hamayyarsa fiye da shi kansa abokin hamayyar.

Wato ke nan babu bukatar ya saurari abinda wancan zai ce don kuwa ya ma fi shi fahimta.

Baya ga wannan kuma, zuciyarmu kan raya mana cewa duk wanda ya ji bayanin ra’ayinmu wajibi ne ya gamsu da ingancinsa.

“Wannan ce ke sa mutane mamaki misali, idan su ka kalli taron jam’iyyar Democrat,” in ji Ross. Duk dan jam’iyyar ya riga ya amince da duk abinda za’a fada a wurin, inda su kuma ‘yan jam’iyyun adawa ke mamakin ganin wasu na yarda da ra’ayin.

Wadannan makaran da ke cikin zuciyarmu, idan su ka hadu da tsarin rayuwar zamani su ke sa sabanin siyasa ya yi kamari har ya kai ga kiyayya da gaba.Idan kana son karanta wannan labari a harshen Ingilishi latsa nan: The reason why politics feels so tribal in 2016