Me ya sa yankan takarda yake da zafi sosai?

Image caption Yankan takarda ba ya fasa fata, amma ya na da tsananin zafi. Ko me ya sa?

Takarda aba ce mara cutarwa ko kadan, amma wanda duk ya taba jera takardu a na’urar dab’i ko kuma ya bude shafukan littafi cikin gaggawa, ya san cewa takarda na dauke da wani mummunan sirri.

Wato ta na iya zama makami, domin kuwa babu abinda ya ke da zafin yanka kamarta.

Ba’a gudanar da binciken kimiyya da yawa game da gano zafin yankan takarda ba, mai yiwuwa saboda ba kowa ne zai amince masu nazari su azabtar da su da gangan ba.

Sai dai a cewar Dr. Hayley Goldbach, likitan fata a jami’ar UCLA “zamu iya amfani da ilimin na halittar sassan bil’adama domin fahimtar abinda ke faruwa.”

Gaba daya bayanin ya danganci karshen jijiya ne. Na farko dai karshen yatsu nan aka fi samun jijiyon da ke jin radadi fiye da ko’ina a jikin mutane.

Duk da dai Goldbach ya kara da cewa, “za ka iya jin radadi sosai idan takarda ta yanki fuskarka ko kuma al’aurarka, idan hakan zai yi wu.”

Amma dai ko da yake ka na iya jin zafi idan takarda ta yanke ka a kafada, cinya, ko kwauri, ko da wasa ba zaka kwatanta wannan zafin da tsananin radadin yankan takarda a dan yatsa ba.

Ka na iya tabbatar da hakan ta hanyar aiwatar da gwajin da masu nazarin jijiyon jiki kan yi.

Sami karfe mai tsini baki biyu ka caki hannunka ko fuskarka, za ka ji zafi a wuri biyu. Amma idan ka caka a bayanka ko cinya za ka ji zafi daya ne kurum.

Hakan na nuna cewa sassan da babu jijiyoyi da yawa ba sa jin radadin ciwo kamar sassan da ke da jijiyoyi da yawa.

Wannan tsari ya yi ma’ana sosai. “Da ‘yan yatsu mu ke lalube duniya, mu ke gudanar da kananan ayyuka,” in ji Goldbach.

“Don haka abu ne mai kyau mu samu jijiyo da yawa a wurin, ta yadda zamu gano hadari komai kankantarsa.”

Baya ga halittar ‘yan yatsu, radadin yankan takarda na yin tsanani ne sanadiyyar yanayin takardar kanta.

Idan ka yi bincike a shafin Google za ka fahimci cewa takarda cike take da kananan halittun bacteria, wadanda za su mamaye duk wani rauni da ta yi maka.

Sai dai, ko me ye gaskiyar wannan bayani, bacteria da sauran kananan halittu ba za su iya zama dalilin zafin yankan takarda ba, musamman a lokacin yankan.

Bacteria na iya jawo cuta idan ba’a kula da rauni da kyau ba, amma ta kan dau lokaci kafin jawo radadi.

A ido, gefen takarda a mike ya ke sambel babu wata gargada.

Amma idan ka yi amfani da madubin da ke kara girman abubuwa za ka ga cewa bakin takarda ya fi kama da zarto fiye da kaifin wuka.

Don haka yankan takarda ba mikakke ne kamar na wuka ko reza ba.

Wato ta kan fizgi fata ne, ta yaga, ta gutsuttsura.

Bugu da kari, yankan takarda ba shi da zurfi. “Zurfinsu ya kai su keta rubin fata na sama, inda bai kai haka ba da ba za a ji zafi ba.

Saboda babu jijiyoyi a rubin fata na sama,” in ji Goldbach.

Sai dai ba sa yankawa da zurfi zuwa cikin jiki, abinda ke sa wasu ke mamakin zafinsu.

Amma wannan rashin zurfin na yankan takarda shi ne sirrin tsananin zafinsu.

Idan yanka ya yi zurfi, ya na haddasa fitar jini. Jinin nan da ya fita zai daskare ya bushe, abinda ke bai wa fatar da ke kasansa damar warwarewa ba tare da fuskantar barazana daga waje ba.

Amma yankan takarda ba ya bayar da wannan kariya saboda rashin zurfinsa.

In dai ba kai ka sa bandeji ko wani man kare kwayoyin cututuuka ba, jijiyoyin da takardar ta bayyanar lokacin da ta yanke ka, su za su ci gaba da zama a waje, abinda ke kara fusata su, su ci gaba da radadi.

Idan babu jinin da zai lullube su, jijiyon da muke jin radadi da su, za su bayyana, kuma su ci gaba da aika wa kwakwalwa sakon cewa jikinka na fuskantar barazana.

Dama dai, wannan shi ne aikinsu.

Wannan bayani, shi ne abinda masana ke hasashen ya na jawo tsananin zafin yankan takarda.

Kawo yanzu babu wanda ya yi gwajin da zai tabbatar ko ya musanta wannan hasashe.

Duk da haka Goldbach na ganin hasashen ya na bisa tafarki.

Abin takaicin shi ne, kowannenmu zai ci gaba da fuskantar barazanar yankan takarda tsawon rayuwanmu.

Saukinta daya dai, yankan takarda dubu zai yi tsananin tsananin zafi, amma ba zai hallaka ka ba. Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: Why Papers cut hurt so much