Ka san ganyen shayin da ya fi zinariya tsada?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption shan shayi a China tamkar wata alada mai tsohon tarihi

Itatuwan Da Hong Pao na kasar China na samar da ganyen shayin da yafi kowanne tsada a duniya, wanda farashinsa ya nunka na zinariya sau 30.

A 2002, wani mai kudi ya biya yuan 180,000 – kusan $28,000 – domin sayen giram 20 na ganyen shayin Da Hong Pao na kasar China. Ko da yake shayi na da daraja a al’adar China tun kimanin shekaru 1,500, farashin ya isa abin mamaki.

Ganyen shayin Da Hong Pao na asali ya nunka zinariya daraja sau 30, inda giram daya ya kai $1,400, wato tukunya daya ta zarta $10,000. Hakika ya na daga cikin ganyen shayi masu tsada a duniya.

“A ido kamar abin banza, amma farashinsa sai dai sarki, darajarsa sai dai Buddha,” in ji Xiao Hui, wata mai shayi a garin Wushiyan da ke bakin ruwa a jihar Fujian, da ke kudancin China, yayinda ta ke nuna min ganyen Da Hong Pao masu duhu wanda ta tsinko daga lambun shayin gidansu.

Xiao da ‘yan uwanta, wadanda suka gaji sana’ar shayi daga iyaye da kakanninsu na ci gaba da ziyartar tsaunukan gari a duk damina, inda su ke rokon ubangijin shayi, Lu Yu, ya samar da sababbin ganyen shayin.

Garin Wuyishan ya shahara da noman shayi tsawon daruruwan shekaru. Ruwan saman da ke gangarowa daga tsaunukan farar kasa ya Malala a koramun garin, na cike da sinadiran da ke bai wa shayi dandano.

A yanzu haka duk kantin da ke Wuyishan ya na da teburin dandana shayi domin gudanar da al’adar shan shayi ta ‘gong fu chan’, sannan kuma ya na cike da ganyayen shayi iri-iri.

Da na kai ziyarar Wuyishan, na gano cewa da akwai samfuran ganyen shayin Da Hong Pao da dama da basu fi karfin talaka ba. Ko da ya ke na asalin na da matukar tsada, ana iya sayar da Da Hong Pao mai kyau akan $100 duk kilo daya a Wuyishan.

Sai dai duk wani Da Hong Pao na gaskiya ya samu asali ne daga dashen reshen bishiyun da su ka fito daga gona guda. Kuma wadannan bishiyun na asali su ne ba su da yawa kuma ganyen shayinsu ya ke dan karen tsada.

Hakkin mallakar hoto wikipedia
Image caption garin Wushiyan da ke bakin ruwa a jihar Fujian

“Da Hong Pao na asali na da matukar tsada ne saboda bishiyun asalin da su ka rage sun yi karanci kwarai,” in ji malamin hada shayi na Wuyishan, Xiangning Wu.

Ba mutanen China ne kadai ke darajanta ganyen shayin Da Hong Pao ba. A 1849, wani masanin tsirrai daga Burtaniya, Robert Fortune ya ziyarci tsaunukan Wuyishan a asirce bisa umarnin kamfanin mulkin mallaka na East India Company domin satar basirar noman shayin Da Hong Po.

A lokacin, kamar yadda ya ke a yanzu, mutanen Birtaniya mayun shayi ne, kuma a China ne kawai su ke iya samo shayin kamar dai yadda a can su kan samo alharini da tangaran.

Ga shi kuma babu wani abu da ake yi a Birtaniya da mutanen China su ke bukata, don haka sai ya zamo su na sayan abubuwa da yawa daga China ba tare da sun sayar da komai nasu a China ba.

Hanyar da za’a magance wannan matsalar ita ce a yi abinda East India Company ya saba yi game da wasu shuke-shuken masu daraja: a sace iri ko dashe a shuka wani wurin. Idan har Burtaniya za ta iya samar da shayinta a India, ke nan za ta rage dogaro da China.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana tsinkar ganyen shayi a duka gundumar Fujia, sai dai ganyen Da Hong Pao ya fi sauran tsada

Sai dai kuma hakan ya kasa yiwuwa. Irin da ‘yan leken asiri su ka samo daga yankin Guangdong a China yaki fitowa a India, kuma ganyen shayin India na asali sam ba shi da dadin dandano.

Wannan shi ne dalilin zuwan Fortune. Aikin da aka ba shi, shi ne ya samo ganyen shayin da yafi kowanne daraja a China – Da Hong Pao – tare da koyo yadda ake shuka shi.

Da yake a lokacin kusan baki dayan China ba a bari baki su shiga, wanda kuma duk ya shiga a bakin ransa, bad-da-kama ta zama dole. Sai Fortune ya yanke gashin baransa, ya makala a kansa ya yi wa Wuyishan tsinke da zimmar neman Da Hong Pao.

Kamar yadda su ke a yanzu, lambunan shayin a kan tsaunuka su ke da cikin kwaruruwan da ke kewayensu. Kuma kamar yadda su ke yanzu, ya tarar da ‘yan shukoki kadan kan wani tsaunin farar kasa wanda aka zana alamomin rubutun China guda uku a jikinsa da launin farar kasa: Da Hong Pao.

Sunan, Jar alkyabba babba, ya samo asali ne daga wani jan bargo da wani sarkin China ya bayar shekaru aru-aru sakamakon warkewa daga cutar da aka yi zaton ba za ta kyale shi ba.

Hakkin mallakar hoto wikwpedia
Image caption Yankin Wuyishan ya shahara da nau'ikan gayen shayi tun tale-tale

Fortune ya tare a dakin bauta na Tianxin Yongle da ke kasan Da Hong Pao, inda ya shige cikin masu bauta har sai da ya samu iri da dashen shayin da kuma dabarun kula da tsironsu. Wannan irin da ya kai India aka hada shi da shayi dan kasa, shi ne tushen kasuwancin da a yanzu ya kai darajar biliyoyin dala a kowacce shekara.

Kamar yadda Zhe Dao, limamin dakin bauta na Tianxin Yongle na yanzu ya shaida min: “A cikin karni na 19, wani mai farautar iri ya zo ya sami irin shayin, amma bai san yadda za’a kula da shi ba don haka ya zauna ya koya daga kwararru.”

A shekarar 827 kididdigar Kirista aka kafa dakin bautar Tianxin Yongle. A 1958, lokacin mulkin Mao, aka kori masu bautar tare da iliminsu na hada shayi. Lokacin da Zhe ya dawo daga tsohon birnin Suzhou a 1990, abinda ya rage na dakin bautar ya zamo gidan talakawa.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Gonakin ganyen shayin Wuyishan na kan tsauni ne
Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Ana samun ganyen shayi a ko ina a gundumar Fujian

“Da fari ni kadai ne kurum,” in ji Zhe. “Yanzu kuwa ina da almajirai da dama, don haka shekaru biyar zuwa shida da su ka wuce muka fara yin shayi.”

Shukokin Da Hong Pao na asali su na gonar dakin bautar ne, amma gwamnati ke kula da su. ‘Yan ganyayen da ba su fi daruruwan giram ba da shukokin ke samarwa na karkashin ikon gwamnati ne, kuma har ya zuwa shekarun baya-bayan nan sojoji ke gadinsu da muggan makamai.

Na zarta lambun kayan marmari na dakin bautar na bi wani siririn burtali da ya nausa kan tsauni har zuwa inda shukokin Da Hong Pao na asalin su ke.

Shukokin sun bayyana alamar gajiya. Babu takaimaman kiyasin shekarunsu, amma dai in aka tuni da labarin Fortune, tabbas sun fi shekaru 350. Zai yi wuya wadannan shukokin su ci gaba da fitar da ganyen shayi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A haka kamar wani abu mara daraja, amma shansa sai wanda ya isa

A ranar 1 ga Mayu, da zarar an fara girbe ganyen shayi, za’a shimfida jar darduma domin tunawa da kyautar tsohon sarki. Kyawawan mata sanye da kayan gargajiya za su gudanar da wata ibada a wurin.

Sai dai babu wani girbi da za’a yi musu. Rabon da wadannan shukoki masu daraja su samar da ganye tun 2005, kuma mai yiwuwa ba za su sake bayar da ganyen shayi ba.

Hakan na nufin kwayakin ganyayen da su ka rage hannun mutane, wadanda kan shanya su duk shekara domin kara ingantan dandanonsu za su ci gaba da kara hauhauwa a farashi. Mai yiwuwa ne ma wata ran darajarsu ta kai darajar duwatsun daimon!

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The drink that costs more than gold.