Kauyen da ya tsira a yaki

Image caption Koda yake mutane da yawa na yi wa Bosnia kallon dar-dar, yanayin kasarta da kuma tarihinta sun sa ta na samun karbuwa wurin ‘yan yawon bude ido.

“A nan aka fara yakin,” in ji Mustafa a yayinda muke tsallaka kogin Miljacka wanda ya raba birnin Sarajevo na Bosnia gida biyu.

A baya na tsallaka wannan gadar, a yawon da nake na kallon gari, amma ban san muhimmancinta ba:

A yammacin 6 ga Aprilun 1992, ‘yan bindiga su ka harbe wasu ‘yan mata biyu a lokacin da su ke wata zanga-zangar lumana.

Wannan harbin shi ya haddasa rikicin kabilancin da daga bisani ya koma cikakken yaki lokacin da Sabiyawa su ka zagaye Sarajevo su ka shiga hallaka Musulmi da Kuroshiyawa a kokarinsu na kafa jamhuriyar Sabiya.

Kuma a wannan ranar, ita ce mafarin kewaye na da wani mutum, wanda kamar sauran Bosniyawa, ya shafa shekaru 20 tun bayan yakin ya na kokarin samar da zaman lafiya.

Mustafa, jagorana, na da shekaru 17 lokacin da yakin Bosnia ya barke, amma dai ya shiga cikin dakarun da su ka kare unguwarsu a Sarajevo lokacin da rundunar Sabiyawa ta fara yi musu luguden wuta.

A matsayinsa na Musulmi, Mustafa ya hada kai da Kuroshiyawa masu addinin katolika da Sabiyawa masu kiristancin gargajiya domin kare kai daga Sabiyawa masu kokarin mamaye yankin domin kafa kasarsu.

Shudayen idanunsa, askakken kansa, da kyaun halittarsa na mutanen yankin Balkan sun sa shi kama da jarimin fina-finai.

Bayan yaki ya yi karatun aikin likitan hakora, amma ya rasa jarin bude asibitinsa.

A madadin haka sai ya zama jagoran masu yawon bude ido inda ya kan bada labaran abubuwan da su ka faru da kuma wuraren zaman lafiya da su ka wanzu a kasarsu.

Mun shirya tafiya mai nisan kilomita 111 daga Sarajevo zuwa kauyen Lukomir, da ke can cikin tsaunuka domin ganin rayuwar gargajiyar al’ummar Bosniya.

Har yanzu kauyawan na sanya kayan gargajiya sakar hannu kuma su na kiwon dabbobinsa bisa tsarin kaka da kakanni.

Kauyen na daya daga cikin kwaya biyu tak da su ka tsira daga bala’in dakarun Sabiya, wadanda su ka lalata irin wadannan kauyuka 13 a yankin.

Sunan Lukomir na nufin “tudun-mun-tsira” – sunan da ya dace da tarihin kauyen cikin yankin Bosniya mai fama da rikici.

Shekaru 21 ke nan bayan kammala tashin hankalin da ya biyo bayan rugurgujewar tsohuwar kasar Yugoslavia, amma yakin shi ne babban abin tattaunawa a tsakanin mazauna kauyen da maziyartansu.

Duk da yadda mutane da yawa ke yi wa kasar kallon dar-dar, kyawun yanayin kasar da kuma tarihinta na sa wa a hankali masu yawon bude ido na kara tururuwa zuwa kasar.

Rubutun jikin rigar Mustafa ya dunkule wannan batu inda aka rubuta:

“Ka taba jin mara shiga hada-hada ya ce, ‘mu je Bosnia’?”

A bayan rigar kuma sai aka rubuta: “Haka ne. Bosnia-Herzegovina: Jarumtarka ta kai ka je?”

Mustafa na daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin jagorar masu yawon bude ido na Green Visions, wanda ya taka muhimmiyar rawa wurin samar da wani burtali mai tsawon kilomita 2,000 da ake kira Via Dinarica.

Burtalin ya tashi ne daga Albania zuwa Slovenia inda ya ratsa tsaunukan da ake kira Dinaric Alps wadanda su ka keta kasashen gabashin Turai.

Na so in daba sayyada akan wannan burtali zuwa Lukomir, amma yanayin damina da karancin lokaci su ka tilasta min amfani da mota.

Ba mu jima da barin Sarajevo ba, ni da Mustafa mu ka shiga wani daji mai duhuwa da kyawawan furanni.

Mu ka wuce Babin Do, wato sansanin wasannin zamiyar kankara na gasar Olympics, inda majalisar dinkin duniya ta kafa sansaninta lokacin yaki.

Mustafa ya shaida min cewa a 1984, an gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu a wadannan tsaunuka da ke kusa da Sarajevo, ciki har da tsaunin da muka nufa wato Bjelašnica.

Kauyuka 13 da ke kewayen tsaunin nan aka kone lokacin yaki.

Mustafa ya shaida min cewa Lukomir da wani kauye da ke bayansa, Čuhovići, ne kawai su ka tsira.

Sojojin Bosnia sun yi nasarar tsayar da na Serbia kafin su isa kauyukan.

Hawan da mu ke yi kan tsaunin kamar muna shiga cikin hadari har dai kauyen ya bayyana.

Gidajen na duwatsu da itatuwa ne tare da rufin kwano.

Mustafa ya kai ni wurin wasu tsofaffi a kauyen.

Tsofaffi ne dai zalla su ka rage a kauyen domin kuwa duk matasa sun shiga birane domin neman aiki da kuma rayuwar zamani.

Mazaunan kauyen na dindindin a yanzu ba su kai 20 ba.

Rahima, ta yi mana maraba cikin murmushi sanye da bujen wando na sakakken ulu da doguwar riga da mayafi da safar hannu.

Mijinta, Vejsil ya mike mu ka gaisa; shi kuma ya na sanye da bakar hular sanyi da safa mai launin kore da ruwan goro.

Buzun da ke rataye a bangon dakinsu alama ce mai nuna su makiyaya ne a baya.

Rahima ta hada mana kofi a kan rishonta na karfe yayinda ita da Mustafa ke tattaunawa game da ‘ya’yansu.

Ita da Vejsil sun shaida mana cewa lokacin hunturu, dusar kankara kan katse hanyar kauyen ba-shiga-ba-fita har tsawon watanni shida.

A shekarun baya-bayan nan su kan tafi wurin ‘ya’yansu a Sarajevo ne da zarar dusar kankara ta fara sauka.

Sun ce mata lokacin yaki sun sha wuya, inda su ka yi fama da karancin kayan masarufi.

Jim kadan lokacin sallah ya yi, Vejsil ya yi alwala ya yi mana sallama yayinda ya nufi masallaci.

Rahima kuma ta bamu gurasa da cukui kafin ita ma ta shiga alwala.

Daga nan mu ka kara hawa saman tsaunin zuwa ga kaburburan tsohuwar daular Bosnia, inda hukumar Unesco ta mayar daya daga cikin muhimman wuraren tarihi na duniya.

Mustafa ya ce min ya na cika da farin ciki duk lokacin da ya ziyarci wurin.

“Wani lokacin idan na rako masu yawon bude ido, na kan zo nan in zurawa gajimare ido – kawai domin jin dadi. Nan wurin shi ne kwanciyar hankalina.”

Idan kana son karanta labarin a harshen Ingilishi latsa nan: The village that survived a war