An sabunta: 6 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 13:39 GMT

Hirar Goodluck Jonathan da BBC

Garmaho

Mukaddashin Shugaban Najeriya ya bayyana cewa bai yi magana, kuma bai gana, da Shugaban kasa Alhaji Umaru 'Yar'aduwa ba tun bayan da shugaban kasar ya koma gida watanni biyun da suka wuce.

Goodluck Jonathan, wanda ke kammala ziyarar da ya kai Amurka, ya bayyanawa Jamilah Tangaza cewa a yunkurin sa na kawo gyara a harkar zabe a Najeriya ya baiwa hukumar zabe ta kasar umarnin kidaya kuriu a wajen da aka yi zabe, kana a bayyana wanda yayi nasara a madadin a dauki akwatuna a tafi da su gaba.

"Dokokinmu na zabe sun karfafa cewa a bayyana sakamakon zabe a matakin mazaba, kuma duk wanda ya tsaya takara ya kasance yana da wakili a mazabar.

"Idan aka tattara sakamakon zabe a wannan mataki sannan wakilan 'yan takara suka karbi kwafin sakamakon, ba wanda zai sauya sakamakon.

'A karamar hukuma ake sauya sakamako'

"Abin da ake yi a da shi ne a kan dauki kayan zabe zuwa matakin karamar hukuma; a nan ne sai a rika zargin cewa an sauya sakamakon kuma babu yadda za a yi a tabbatar da hakan.

"To amma yanzu na ba da umarni ga Hukumar Zabe cewa a bayyana sakamako a matakin mazaba saboda ko wanne wakilin dan takara ya rike nasa kwafin sakamakon.

"Idan aka sauya sakamakon a karamar hukuma, masu korafi na da hujja idan suka tafi kotu; sai kotu ta soke zaben".

Dokta Goodluck Jonathan ya kuma ce zai yi nazarin irin ayyukan da shugabannin Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta, wato INEC, suka yi don ganin ko akwai bukatar sauya wasu:

'Za a sauya shugabannin zabe, amma...'

"Gaskiya ne cewa kallon da ake yiwa shugabannin Hukumar Zabe yanzu shi ne cewa ba za su yi zabe na gaskiya ba.

"To amma na sha fada cewa wa'adin yawancin shugabannin Hukumar Zaben zai kare a karshen watan Yunin bana.

"Saboda haka za mu sake nazari idan muka ga wasunsu sun gaza babu shakka za mu sauya su".

Da aka tambaye shi irin kalubalen da ya ke fuskanta, sai Mukaddashin Shugaban kasar ya ce:

Kalubale

"Ba abu ne mai sauki ba--an fara wannan tafiyar ne ina rike da mukamin Mataimakin Shugaban kasa; ina aiki tare da Shugaban kasa, sai rashin lafiya ya kama shi har ya zuwa wannan lokacin da muke magana.

"Ga shi zabe na tunkarowa; saboda haka akwai kalubale da dama a gareni--kowa dai ya san halin da kasar ke ciki, don haka ba sai na yi bayani ba".

Dangane da batun ko yaushe ne rabon da ya yi magana da Shugaba Umaru 'Yar'adua kuwa, Goodluck Jonathan cewa ya yi:

"In dai ana maganar wata tattaunawa ce mai dan tsawo, to ina ganin rabon da mu yi magana tun ranar 26 ga watan Nuwamba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.