An sabunta: 6 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 17:21 GMT

Jawabin juyin mulkin Nijar

Garmaho

A Jamhuriyar Nijar, Sojoji sun kwace mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Tanjda Mamadou.

Rahotanni daga jamhuriyar ta Nijar na cewa shugabannin sojin da suka karbi mulkin kasar jiya sun bada sanarwar bude dukkan kan iyakokin kasar.

Sojojin sun yi juyin mulkin ne bayan dauki ba dadin da aka yi na tsawon wani lokaci da aka yi.

Colonel Goukoye Abdul Karimou shi ne ya bada sanarwar juyin mulkin. Ga ma hoton bidiyon sanarwar:

Jawabin Juyin Mulki

Col. Goukoye dai na cewa ne: "Maza da mata 'yan Nijar masu kishin kasa. A yau sha takwas ga watan Febrairu, mu dakarun tsaron Nijar mun daukar wa kanmu nauyin kawo karshen zaman dar dar da ake fama da shi a kasa kamar yadda kuka sani.

Majalisar koli ta maido da mulkin demokaradiyya a Nijar, wadda ni ke kakakinta, ta yanke shawarar dakatar da kundin tsarin mulki na jamhuriya ta shida, da kuma rusa dukkan hukumomi na gwamnati.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.